MAGANGANU DA JAWABAN AYATULLAH UZMA SAYYID ALIYU KHAMENE'I {H}
(Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci)
A bisa la'akari da cewa dan'Adam mutum ne mai yawan mantuwa da kuma jahilci, don haka
nema ya ke bukatuwa da wanda a kullum zai dinga tunasar da shi da kuma yi masa wa'azi don
ya kyautata rayuwarsa da duniya da ta lahira.
To a hakikanin gaskiya, kuma babu shakka, cewa daga cikin muminan bayin da Allah Ya arzurtamu da
da su a wannan zamani namu, wadanda kusan muna iya cewa dukkan kalamai da ayyukansu babban darasi
da hannunka mai sanda ne gare mu, Ayatullah Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Hali, yana daga cikinsu,
ko kuma ma mu ce yana daga sahun gaba cikin irin wadannan bayin Allah.
Allah dai Ya arzurta wannan Jagora namu da dimbin ilmi, hangen nesa, sanin ya kamata, bugu da kari kuma
ga sanin siyasar Musulunci da ma ta yau da kullum, shi yasa ma a duk lokacin da yayi magana, lalle za ka
ga hikima da fitar da al'amurra a fili don amfanuwar dukkan al'umma.
To don haka ne, na ware wannan shafi na musamman don kawo jawabai da kuma kalamominsa na hikima
don su kasance mana "hannunka mai sanda" a rayuwar ta mu ta yau da kullum.
Don haka mai karatu kana iya biyo mu a sannu a hankali don ganin wadannan jawabai da kuma kalamomi.
A sha karatu lafiya.