TAMBAYA: Sheikh Muhammadi Golgaygani, kana daga cikin mafiya kusanci da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, idan har ka yarda zan so in yi maka wasu tambayoyi kansa. Da farko dai, zan fara tambayarka ne dangane da yanayin lafiyar mai girma Jagoran. Kamar yadda ka sani cikin 'yan kwanakin nan kafafen watsa labaran kasashen waje suna ta maganganu kan lafiyar Jagora, musamman ma cikin wannan wata da muke ciki. Don haka muna son ka yi mana bayani kan yanayin lafiyar mai girma Jagoranmu?
AMSA:Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai, Ina gode maka da wannan tambaya da ka min, a yayin amsa wannan tambaya taka, zan so in bayyana cewa daya daga cikin tarko abokan gaba, shi ne kaddamar da yaki na kwalkwalwa don gamawa da abokan hamayyansu. Bisa la'akari da cewa a yau din nan babban jigon Juyin Juya Halin Musulunci shi ne mai girma Jagora, kuma kamar yadda ka sani ne bai canja ba daga irin matsayar da Marigayi Imam (r.a) ya dauka kuma yake kai ba, a hakikanin gaskiya ma dai ya yi tsayin daka wajen kare wannan tafarki na Imam, don haka makiya ta hanyoyi daban-daban sun yi ta kokarin bayyana sabanin hakan amma dai ba su yi nasara ba. Don haka ne makiyan yanzu kuma suka koma wajen yada irin wadannan jita-jita da kararraki don haifar da damuwa da karyewar zuciyar al'umma da kuma masoyansa.
Shakka babu, a dabi'ance 'yan Adam sukan kamu da ciwo nan da can, to amma ina son in sanar da kai cewa lalle Jagora kan yana nan cikin koshin lafiya. Ina ga watakila zai ba ka mamaki idan na sanar da kai cewa ya kan je wasan hawa dutse sama da sau guda a kowani mako, kuma a kowani zuwa ya kan dau awoyi a can, kuma ma da dama daga cikin matasa ma ba za su iya karawa da mai girma Jagora ba a wannan bangaren.
TAMBAYA:Shin akwai wani lokaci na musamman ne da mai girma Jagoran ya ke zuwa hawa dutsen?
AMSA:Hakan yana da alaka ne da yanayin da ake ciki, misali a lokacin sanyi lokacin da kankara take zubowa akan duwatsu, to mai girma din ba ya tafiya hawa dutse a wannan yanayi, don haka ba zai yiyu a fayyaye wani lokaci na musamman ba, kamar yadda kuma babu wani waje na musamman da yake zuwa. Anan yana da kyau a gane cewa Mai girma Jagora yana da wata jumla mai kyau gaske dangane da wasannin motsa jiki, ina babu laifi idan mai karatu ya san cewa Jagora yana daga cikin mutanen da suka fi kowa kwadaitar da al'umma wasannin motsa jiki, ya kasance ya kan ce:"Wasannin motsa jiki yana da kyau ga matasa kana kuma wajibi ne ga tsoffin mutane".
TAMBAYA:Mun sami labarin cewa a wasu lokuta ma ya kan yi sallar Asubahi a daya daga cikin duwatsun da suka bayan birnin Tehran?
AMSA:Na'am, a wasu lokutan ya kan yi sallar Asubahi a kan duwatsun, a wasu lokuta ma ya kan haura can kololuwa.
TAMBAYA:Shin ka taba samun damar raka shi?
AMSA:E a wasu lokuta. Amma kasan ni tsoho ne, ka san ba zan iya tafiya da shi kowani lokaci ba. Amma duk da haka dai na riga da na san tsare-tsaren ayyukansa. Ina son in sanar da kai cewa da a ce ba shi da koshin lafiya da ba zai iya yin irin wannan wasannin motsa jiki ba, musamman ma dai hawan dutse, wanda kamar yadda ka sani ne, wasa ne mai tsananin wahala. To amma Alhamdu Lillahi yana cikin koshin lafiya da walwala.
TAMBAYA:A dali'ance a duk lokacin da ya je hawa dutsen sauran mutane da kuma wadanda su ma suka zo wajen don hawa dutsen za su ganshi, shin ka taba ganin irin wannan ganawa da Jagoran wacce ba a riga da an tsara ta ba?
AMSA:A'a ni dai ban taba ganin irin wannan ganawa ba, amma dai ina sane da ita. Ina sane da cewa Jagoran ya kan sadu da mutane, a lokacin tafiyarsa ko kuma lokacin dawowa, wadanda sukan zo su gaishe cikin kaunar juna da girmamawa, shi ma kuma ya mayar musu da irin wannan gaisuwa tare da girmamawa a yayin da suke ganawar da kuma magana da juna.
TAMBAYA:Shin ko za ka iya bayyana mana yanayi ayyukansa na kowace rana ko kuma na sati? Hakan kuwa saboda da dama za su so sanin yadda rayuwarsa ta ke, kuma kana daga cikin wadanda suke a matsayin da za su iya bayyana hakan?
AMSA:To, daya da cikin ayyukan da yake yi dai kusan ko yaushe shi ne farkawa alal akalla awa guda kafin kiran sallar asuba, ya kan yi amfani da wannan lokaci wajen ibada da salloli. Daga nan kuma sai ya yi sallar asuba, a wasu ranakun kuma sai ya tafi hawa dutse, in kuwa bai tafi ba ya kan dan huta. Ya kan fara ayyukansa na rana ne da misalin karfe 8 na safe.
Ayyukansa dai suna da yawa; daga cikinsu dai shi ne ganawa da jami'ai gwamnati, fararen hula da na soji, wadanda suka bukaci ganawa da shi kuma aka ba su lokaci na musamman. Wadannan jami'ai sukan zo da kuma gabatar da rahotanninsu, daga nan kuma Jagora mai girma ya kan bayyana musu abubuwan da ya kamata su yi. Irin wannan aiki dai ya kan kare zuwa wajen sallar azahar. Daya daga cikin abubuwan da ya kebantu da su shi ne ya kan yi sallolinsa ne a jam'i (tare da jama'a) koda kuwa sallar asuba ce da ya ke yi a gida. Ya kan yi sallar azahar ne kuwa tare da bakin da suka zo masa da kuma sauran ma'aikatan ofishinsa. A wasu lokuta ma wasu mutane, jami'ai da kuma malamai da suke son yin salla a bayansa sukan zo a daidai wannan lokaci.
Bayan gama sallar azahar, ya kan shiga don cin abincin rana da kuma dan hutawa, kana kuma ya dawo ofis da misalin karfe hudu na yamma (a wasu lokuta ya kan ci gaba da ganawa da mutane). Haka nan zai ci gaba har zuwa lokacin sallar magariba, wanda ya kan yi ita ma tare da jama'a. Da daddare kuwa, mai girma Jagora ya kan yi karatu ko kuma sauraron labarai a talabijin ko kuma ya kasance tare da iyalansa.
TAMBAYA:Ka yi magana kan karatu, shin wasu bangarori ne Jagora din yake irin wadannan karatun, baya ga labarai da kuma rahotanni na musamman? Shin akwai wani fage ne na musamman da yake karatun a ko yaushe?
AMSA:E, lalle Jagora ya kan karanta littattafa da suka shafi fannin fikihu na musamman, kana kuma ya kan zauna da manyan malamai sau guda a kowani mako. A kowani sati ya kan gana da manyan malamai da mujtahidai a nan ofishin don tattaunawa kan mas'alolin da suke bukatuwa da a yi dubi cikinsu, kuma wadannan tarurruka sukan kasance masu amfani sosai. Baya ga haka kuma ya kan yi darasi kan wasu fannonin na daban kuma.
TAMBAYA:Shin wadannan tarurruka (da yake yi da malamai) akan yi su ko yaushe ba tare da fashi ba?
AMSA:Kwarai kuwa akan yi su ko yaushe ba tare da fashi ba, kuma shekara da shekaru aka yi ana yinsu, sai dai kawai lokacin da ba ya nan a birnin Tehran (idan ya yi tafiya).
TAMBAYA:To ya ya sauran bangarori na ilmi kuma, kamar su adabi?
AMSA:E, lallai kuwa, hakika irin matsayin da yake da shi na Jagoranci ya kere dukkan sauran matsayi da daukakan da yake da shi, shi dai mawaki ne kamar yadda kuma ya kasance masanin adabi a daidai wannan lokaci. Hakika waken da ya rubuta suna cike da fasaha da kuma ma'ana. Kamar yadda kuma Mai Girma Jagora ya kan zauna da mawaka tun shekaru sai dai hakan ba wai a koda yaushe ba ne. A lokacin da ya zauna da sanannun mawaka kuma suka gabatar da wakensu, to fa a duk lokacin da Jagora ya budi baki don ba da ra'ayinsa kan wakan za ka ga sanannun mawakan suna jinjina masa da kuma girmama irin ra'ayin da yake bayarwa saboda irin masaniyyar da yake da ita kan wake. A hakikanin gaskiya dai Jagora ya kan gabatar da sabbin abubuwa ne a lokacin da yake ba da ra'ayin nasa, don yana da cikakkiyar masaniya a fannin adabi da kuma wake. Watakila ka ji jawabin da ya yi a yayin bukin girmama (sanannen mawakin nan) Hafiz Shirazi, lalle babu wani wanda ya taba magana kan Hafiz da irin shakalin cikakke kamar yadda Jagora ya yi.
Daya kuma daga cikin ayyukan da yake yi shi ne ziyarar iyalan shahidai, ya kan kai irin wadannan ziyara ne kuwa ba tare da an sanar da iyalan da za a kai musu ziyarar cikin lokaci mai tsawo ba. A takaice dai iyalan da za a kai musu ziyarar ba sa sani waye ne zai kawo musu ziyara, har sai Jagoran ya iso kafin su san wane ne ya kawo musu ziyaran. Kafin nan dai akan buga musu waya a sanar da su cewa wani jami'in gwamnati zai kawo musu ziyara, hakan ma don a tabbatar da cewa suna gida ne, don haka ana bukatan su kasance a gida. A wasu lokuta na kan raka shi kai irin wadannan ziyarce-ziyarce. A rana guda ya kan kai ziyara ga iyalan shahidai kimanin uku ko hudu ko kuma biyar.
TAMBAYA:To ya ya ake zaban wadannan iyalan shahidai?
AMSA:Abin ban sha'awan shi ne cewa akan zabi iyalan da suke zaune ne a guraren da marasa abin hannu suke, wato wadanda suke nesa da gari, don kai wannan ziyara, da wuya ka ga Mai girma Jagora ya kai ziyara yankunan da masu abin hannu suke zaune, kuma a mafi yawan lokuta ya fi kai ziyara ga iyalan da suka ba sadaukar da shahidai biyu, uku ko kuma hudu. Wannan ganawa dai da jagoran ya ke yi da iyalan shahidan ta kan kasance abin sha'awa da kuma kaunar juna, ya kan yi kimanin minti talatin ko fiye a kowani gida da ya kai ziyara. Da farko dai ya kan bukaci a kawo masa hoton shahidin, daga nan kuma sai a bukaci a yi masa bayani inda shahidin ya yi shahada da kuma yadda ya yi shahadan. Jagoran ya kan yi mu'amala da iyayen shahidin cikin tausayawa da kuma kauna, idan kuwa shahidin yana da kananan yara, ya kan dauke su ya zaunar da su akan cinyarsa yana rungumarsu da nuna musu soyayya da kuma kauna.
Dukkan maganganun da ya kan yi dai sukan shafi shahidi ne, matsayin shahidi da kuma kaunar shahidi...a wasu lokuta ma dai iyayen shahidin sukan gagara magana, sai kawai su fashe da kuka saboda shaukin ganawa da suka yi da shugaba abin kauna, ba sa iya gaskata kansu kan cewa yau ga Jagora ya kawo musu ziyara don tattaunawa da su. Na sha jin da dama daga cikin iyayen shahidan da aka kai musu ziyarar suna cewa sun yi mafarkin cewa daya daga cikin waliyan Allah zai kawo musu ziyara rana guda kafin a kawo ziyarar. Wannan dai na daga cikin ayyukan Jagora na koda yaushe.
Daga cikin ayyukansa kuma har da ziyarar da yake kai wa garuruwa daban daban, a lokuta da dama ya kan zabi garuruwan da aka bar su a baya ne wadanda suke da nisa don kai musu ziyara. Hakika irin wadannan ziyara suna dadada rai kamar yadda kuma irin tarbar da al'umma suke masa ba ta kwatankwaci. Daga cikin ayyukan da yake yi a yayin wannan ziyara har da ganawa da al'umman yankin. A kowane lokaci za ka dogon layin mutane da ya kai kilomitoci wadanda suka taru don yi masa maraba, shi kuma ya kan tarbe su da so da kauna da kuma budaddiyar zuciya, a wannan lokaci maza da mata sukan iso don ganawa da shi kuma hakan babban abin farin ciki ne ga su kansu al'umma din. Jagoran dai ya kan yi musu jawabi da kuma jin irin halin da suke ciki gwargwadon yadda lokaci ya ba shi dama.
A yayin wannan ziyara dai mu kan ayyana wasu mutane daga cikin ma'aikatan ofishin nasa don amsa wasikun mutane da kuma magance musu matsalolinsu, a wasu lokuta ma wadannan mutane sukan zauna a wannan gari har na tsawon wasu kwanaki don magance matsalolin al'umman yankin.
TAMBAYA:Mutane za su so sanin yanayin tattalin arzikin Jagoransu, zai yi kyau idan da za ka mana bayani kan yanayin tattalin arzikin Jagora, a wani irin yanayi ne yake rayuwa, kuma ta ina ne yake samun abin da yake rayuwa da shi da kuma irin dukiyar da ya mallaka?
AMSA:Ina iya cewa yanayin rayuwar Mai Girma Jagora dai, duk kuwa da irin damar da yake da ita na amfana da dukkan abubuwan da ake da su, ba ta dara yanayin yadda sauran mutanen da ba komai ba suke rayuwa. Hakika ya takaita da wannan yanayi kuma yana rike da shi, a koda yaushe kuma ya kasance mai yin wasiyya ga jami'an gwamnati da su guji yin almubazzaranci. Babu laifi idan na bayyana cewa daga cikin irin ayyukan da Jagora ya ke yi a lokutan bukukuwa na musamman na addini shi ne gudanar da bukukuwan daurin aure, a wannan lokaci ya kan tara samaruka goma zuwa sha biyu, mafi yawansu 'ya'yan shahidai ne ko kuma mutane muminai, misali a lokacin bikin aiko Manzon Allah (s), to Jagoran ba karban abin da ya wuce sisin zinare guda 14 a matsayin sadaki, ba wai yana ganin hakan ya saba wa shari'a ba ne, face dai yana da ra'ayin cewa lallai ne a kirayi mutane wajen rayuwa mai sauki, idan har sun bukaci su sanya sadaki mai yawa sama da sisin zinare 14, to Jagoran ya kan bukace su da su je wani waje don daurin auren, ya kan sa hakan a matsayin sharadi. Sai dai kuma ba ya hana a kara da aikin hajji ko kuma Umra akan wannan sadaki, hakan kuwa saboda wannan aiki ne na ibada.
Wani abin sha'awa shi ne mintoci sha biyar kafin daurin auren ya kan gudanar da jawabi da kuma ba da shawarwari ga ango da amarya dangane da rayuwa cikin sauki, ya kan shawarce su da su yi watsi da rayuwa ta jin dadi da almubazzaranci. Shi kansa ya kan lizimci wannan abu da yake fadi.
Amma dangane da masdarin kudaden da yake rayuwa da su, yana da kyau ka san cewa, Jagora dai ba shi karban wani albashi daga wani waje kamar yadda kuma ba ya amfani da kudaden da suka shigo hannunsa daga wasu gurare (kamar khumusi da sauransu) don amfanin kansa, face dai ya kan rayu ne ta hanyar kyaututtukan da masoya da mabiyansa suke ba shi. Hakan 'ya'yansa ma suke rayuwa akan wannan tafarki na sa, su ma suna rayuwa ne kamar yadda yake rayuwa cikin sauki.
TAMBAYA:Me 'ya'yayensa suke yi....shin suna rike da wani mukami na siyasa a gwamnati ne?.
AMSA:A'a...ko da wasa...face dai suna karatu ne na addini.
TAMBAYA:Ya ya alakar Mai Girma Jagora take da Shugaban kasa? Don kuwa kamar yadda ka sani ne kafafen watsa labaran kasashen waje suna kokarin nuna cewa babu wata alaka mai kyau tsakaninsu, kuma wasu suna so su yi amfani da wannan batu (don cimma wasu manufofi)....me za ka ce dangane da wannan lamari?
AMSA:Lalle babu gaskiya ko tushe cikin wannan zance, al'amarin ba kamar yadda suke tsammani ba ne. Tun daga ranar farko na kama aikin Sayyid Khatami a matsayin shugaban kasa ya zuwa yanzu, a lokuta daban daban shugaban kasa (Khatami) ya gana da Jagora kuma ganawar tasu an yi su ne cikin soyayya da kaunar juna, kai a gaskiya ma dai irin girmamawan da Sayyid Khatami yake wa Jagora lalle abin misaltawa ne. Hakikanin gaskiya akwai kyakkyawar alaka tsakanin Jagora da shugaban kasa kamar yadda alakar take tsakanin Jagoran da sauran shuwagabannin hannayen gwamnati (Alkalin alkalai da shugaban majalisa).
TAMBAYA:Shin an taba samun lokacin da Mai Girma Jagora ya yaba ko kuma ya nuna rashin jin dadinsa ga ma'aikatan ofishin nasa dangane da faruwar wani abu?
AMSA:Lalle ba mu taba ganin yadda ya yi Allah wadai da wani ba a nan...Idan wani daga cikin ma'aikata a nan ya yi wani abin da ya burge Jagoran ko kuma ya janyo hankalinsa ya kan saka masa da cewa "Allah Ya albarka ce ka, kuma Ya taimake ka".
TAMBAYA:Shin dukkan wasiku da bukatun al'umman gari sukan isa hannun Jagoran kuwa?
AMSA:Kwarai kuwa....a nan ofis muna da wani sashi da aikinsa kawai shi ne amsa bukatun al'umman gari...wato akwai daya daga cikin mataimakana a nan da yake daukan nauyin bangaren (Alaka da Al'umma), dukkan wasikun da suka shigo ofis, idan har sun shafi lamurra ne suka shafi mutum kansa, akan tura su zuwa ga wannan sashi...haka nan kuma muna da wasu wasiku na aikin ofis, to wadannan ba su da alaka da wannan sashi.....a takaice dai ofishin namu na kokarin iyakacin iyawansa wajen amsa dukkannin wasikun da suka shigo, don kada wata wasika ta yi kwantai.
TAMBAYA:Kamar yadda ka sani ne Mai Girma Jagora kuma shi ne babban kwamandan sojojin kasa, shin ko za ka yi mana karin bayani kan hakan?
AMSA:Alhamdu lillah, dakarun kasarmu a halin da ake ciki suna cikin kyakkyawan yanayi na karfi. Bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, saboda dalilin matsin lamban da muka fuskanta, dakarun kasarmu, Ma'aikatar Tsaro da sauran cibiyoyin soji sun sami damar toshe dukkan gibobin da muke da su da magance sauran matsalolin da muke da su. Mun samu nasarar iya gyara kayayyaki da kuma makaman yaki kai har ma da kera wasu. Lalle ana iya cewa Jagora ya taka gagarumar rawa a wannan bangare, wato a fagen kere-kere kayayyakin aikin soji da muke yi. A duk lokacin da aka samu nasara kirkiro wani abu ko kuma kera wani abu daga cikin kayayyakin aikin soji, to lalle hakan ya kan samu kwadaitarwa da kuma kulawa ta musamman daga Jagora.
Kafin samun nasarar Juyin Juya Hali, babu wani abin da muke iya yi, kasashen yammaci ba su yarje mana hakan ba, ba su taimaka mana da kayayyakin wadannan ayyuka ba, idan har irin wadannan kayayyaki na soji suka lalace sai dai mu koma da su kasashen da aka kera su, Amurka a mafi yawan lokuta. To amma a halin yanzu an samu canji a wannan bangaren, kusan dukkan abubuwan da ake yi akan yi ne a cikin gida, a halin yanzu ba ma bukatuwa da masana daga kasashen waje sai dai kawai a wasu 'yan lokuta marasa yawa sosai. Don haka Jagora a matsayinsa na babban kwamandan sojoji ya kasance a sahun gaba wajen karfafa irin wadannan ayyuka, kuma dukkan umarni da hani sukan zo ne daga gare shi. Ya kan kuma kai ziyara ga cibiyoyi daban-daban na soji a lokuta daban daban.
TAMBAYA:Ya ya Jagora ya ke samun muhimman labaran abubuwan da suke faruwa a cikin kasa? Shin ta hanya guda yake samun wadannan labarai ko kuma akwai wasu hanyoyin? Ya ya alakarsa da jaridu, radio da talabijin?
AMSA:To a gaskiya dai hanyoyin da labarai suke shigo masa ba su takaita kawai da wadannan ba, yana da masaniyya kan dukkan abubuwan da suke faruwa a cikin gida, kai watakila ma dai saboda irin matsayin da yake da shi ana iya cewa shi ne mutum na farko da yake sanin abubuwan da suke faruwa a cikin gida gaba daya. Ya kan karanta jaridu da mujallu sosai kuma da nitsuwa...mu ne muke tanadar masa da irin wadannan jaridu, sai dai kuma bai takaita kawai da hakan ba, dukkan jaridun da aka buga da safe da yammanci duk suna nan a ofishinsa, ya kan karanta su musamman ma dai abubuwan da wadannan jaridu suka fara da su, kamar yadda kuma mu kan kawo masa mujallun da ake buga su a kowani wata ko kuma fasali...hakika yana da ayyuka da yawan gaske.... a wasu lokuta a fili ya kan ce min awannin da aka da su a rana (awanni 24) sun kasa masa.
TAMBAYA:Idan haka ne to fili kenan cewa ba ya shiga barci da wuri kenan?
AMSA:Lalle kan...lamarin haka yake, sai dai kuma a wasu lokuta mu da wasu na kurkusa da shi mu kan ba shi shawarar ya dinga kwanciya da wuri, to sai dai kuma duk da hakan dai ba ya kwanciya da wuri. A takaice dai ya zama wajibi dai ga Mai Girma Jagora da ya damu da kuma kula da lafiyarsa.
TAMBAYA:To mai girma mun gode kwarai da gaske.
AMSA:Babu komai ni ma na gode.