Jawabin Jagora A Bukin
Mika Wasu Makamai Masu Linzami (Shahab 3)
Ga
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki saboda da kasantuwanku Ya ku wadannan matasa muminai. Hakika daya daga cikin mafi girma da daukakan kadara da wata kasa za ta iya mallaka shi ne samun mutane muminai kuma masu aiki da jini a jika. A yau dai, saboda falalar Ubangiji Madaukaki, ga mu nan gaba ga irin wadannan mutane (muminai), lalle babu shakka ina jinjina wa dukkaninku ya ku wadannan matasa madaukaka da kuma dukkan jami'an sojin sama na dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci saboda irin wannan kokari naku, lalle ina kara mika godiyata gare ku gaba daya. Cikin yardar Allah, tsawon shekarun da suka gabata sojojin sama na dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci sun kasance abin jinjinawa, saboda kwarewar da suka nuna wajen gudanar da aikinsu, an samar da dakaru abin yabawa wadanda suka gudanar da kyawawan ayyuka na a yaba, wannan dai wani bangare ne na karfin al'ummarmu, wadanda suka nuna kawukansu a bangarorin da suka shafi ayyukansu. Babu kokwanto, kowace al'umma tana bukatuwa da ta zama mai karfi don kare madaukakan manufofinta. Sai dai kuma fassarar ma'anar karfi a bisa mahanga ta addini da ruhi ta sha banban nesa ba kusa da fassarar ma'anar karfi a mahanga ta zahiri. Mahanga ta zahiri tana ganin karfi ne kawai cikin mallakan wasu abubuwa da suka hada da makamai masu guda, na kare dangi da dai sauransu, to wadannan abubuwa dai ba su ne karfi kawai ba. Mafi girman bangaren karfi dai yana nan ne a wajen mutanen da suke son amfani da shi. Karfi da iko na hakika akan same su ne a wajen mutanen da suke ma'abuta gaskiya, haka nan kuma su kokari da ba da himma wajen tabbatar da gaskiya da kuma manyan manufofi madaukaka. Wadannan mutane da suke ba da himma wajen kare gaskiya; ba sa amfani da karfi ta hanyar dabbanci; ba sa zalunci; ba sa girman kai; ba sa wulakanta mutane; ba sa wuce gona da iri akan kasar wasu mutane na daban; ba sa kwace dukiyoyi da arzikin sauran al'umma da maishe su mallakinsu; wannan dai shi ne dabi'a ta karfi na hakika na ruhi. A bangare guda kuma karfi irin na zahiri ba shi ba da muhimmanci ga duk wani abin da ya shafi dabi'u na kwarai. Karfi na zahiri ba ya kula da gaskiya da kuma duk wata manufa ta gaskiya, tunani na masu karfi irin na zahiri dai tunani ne na hauka da amfani da karfi, don kuwa suna ganin suna da karfi na zahiri, don haka gaskiya tana tare da su, hakan dai babban kuskure ne kuma bata ce. A yau ku dubi abin da Amurka - wacce tun farkon nasarar Juyin Juya Halin Musulunci ya buga mata alamar kawo karshenta da kuma kwance mata zani a kasuwa - take aikatawa a bangarori daban-daban na duniya, ba sa tunanin kare hakkokin 'yan'Adam da al'ummomin duniya da kuma kyawawan dabi'u na dan'Adam, abin da kawai ya fi damunta shi ne yadda za ta tabbatar da manufofinta na girman kai. A lokacin da karfi na zahiri ya fito filin daga, to akwai yiyuwa hari da kuma gudu, to sai dai kuma babu tsammanin samun nasara da tsira ta karshe. A lokacin da aka hada karfi da tsoron Allah, aka hada karfi na zahiri da na badini (ruhi), to a lokacin za su yi aiki ba tare da take hakkokin 'yan'Adam ba, ba za a wuce wuri akan hakkokin wani mutum ba; a irin wannan yanayi za a yi amfani da shi (karfi) ne wajen tabbatar da gaskiya da adalci, saboda haka za a samu nasara ta hakika kuma ta karshe. Wannan dai ita ce ma'anar karfin da asasinsa shi ne bukatun al'umma, hukuma kuma tana ba da himma wajen kare madaukakan manufofin al'umma. Lalle cikin shekaru ashirin da hudun da suka gabata an ketare wannan jarrabawa. Hakika mun ga dai yadda karfi na zahiri ya gaza wajen fuskantar karfi irin na ruhi a Iran, a Labanon, a Palastinu da ma dai sauran wuraren da karfi na gaskiya ya shigo fagen fama, mun ga yadda wannan karfi na zahiri dai ya fadi kasa war-was sannan kuma duk da wannan girma nasa aka yi waje da shi. Gaskiya dai haka ta kasance, kuma haka take sannan kuma haka za ta ci gaba da kasancewa. (Ku duba ku gani) Amurka a kasar Iraki dai a lokacin da take fada da gwamnatin Saddam, ta fuskanci wani karfi ne na zahiri irin nata, wanda ma yake da rauni, don haka ne ta yi nasara; to amma a yau bayan wannan nasara ta soji da ta samu, tana fuskantar matsaloli da kuma rauni a halin yanzu ma tana kokarin ja da baya saboda tana fuskantar karfi da bukatun al'ummar Iraki ne. A halin yanzun abin da ya tsaya a gaban 'yan mamayan Irakin, ba wani karfi na soji da makamai na zamani ba ne; face dai wani karfi ne kawai na al'umma; al'ummar da ba sa son ganin wani dan mamaya a kasarsu, wanda zai doru a kansu da kuma dukiyoyinsu; ba sa kaunar ganin wani dan mamaya ya zo yana wulakanta musu abubuwan girmamawansu na addini da na kasa. Wannan dai shi ne abin da karfi na gaskiya zai iya kawowa, kuma matukar dai ya ci gaba da kasantuwa haka nan kuma ruhin gwagwarmaya ya ci gaba da zama a zukatan al'umma, to lalle babu wani karfi na duniya da zai iya fuskanto shi. Kasashen Labanon da Palastinu dai kyakkyawan misali ne na hakan. Ko shakka babu, tsarin gwamnatin Musulunci za ta ci gaba da kare gaskiya, hakkokin 'yan'Adam, manufofin Musulunci da na kasa na al'ummarta da kuma girma da daukakan al'umma ma'abuta daukaka, kuma koda wasa ba za ta juya da baya ba wajen fuskantar zalunci. Jamhuriyar Musulunci Ta Iran dai tun farko ta fadi kuma ta tabbatar da cewa ba za ta taba mika wuya ga barazana, zalunci, matsin lamba da girman kan ma'abuta girman kan duniya ba, kamar yadda kuma ba za ta taba juyawa daga madaukakan manufofinta ba. Wannan dai wata mahanga ce ingantacciya, ta gaskiya wacce ta dogara akan karfi irin na badini (ruhi).
A halin da ake ciki dai, al'ummar Iran tare da dakarun kasa masu makamai - wato sojoji, dakarun kare Juyin Juya Hali da kuma Basij (dakarun sa kai) - a shirye suke su yi amfani da karfin da suke da shi da kuma makamansu na zahiri bisa goyon bayan karfi na badini wajen fuskantar duk wani abokin gaban da ke son wuce gona da iri akan gwamnatin Musulunci, kuma babu shakka nasara tana tare da wannan karfi na badini. Ya ku wadannan matasa madaukaka, sojojin sama na dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci, dole ne ku shirya da kuma zama cikin shirin ko ta kwana saboda irin canjin da aka samu a fagen siyasa na duniya. A halin yanzu dai - muna gode wa Allah - ana iya ganin shiri na zahiri da na badini a wajen wadannan dakaru, na san hakan ne ta hanyar masaniyya da kuma rahotannin da suke shigo min, to sai dai kuma har a kullum kofar ci gaba da kuma kara himma a bude ta ke, a bangaren karfafa ruhi da kuma shiri na zahiri. Dole ne ku yi amfani da dukkan himma, kokari, kwarewa da kuma imaninku don ku bayyanar da gudummawarku ga dukkan duniya - ba wai kawai ga Iran ba -. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki, saboda girman jinin shahidai mai tsarki da kuma waliyanSa da Ya tabbatar da mu akan tafarkin shahidai, ya kuma sanya mu a madamashinsu. Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.
|