Jawabin Jagora A Garin Waramin Da Ke Kusa Da Birnin Tehran A Ziyarar Da Ya Kai Can


  • Maudhu'i: Abokan Gaba Da Kokarinsu Na Haifar da Sabani da Ruguza Gwamnati
  • Wuri: Garin Waramin-A Ziyarar da Jagoran Ya Kai.
  • Rana: 11/Rabi'us Sani /1424 = 12/Yuni/ 2003.
  • Shimfida:A safiyar wannan rana 12 ga Watan Yunin 2003, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (h) ya kai ziyara garin Waramin da ke kusa da birnin Tehran don gane wa ido da kuma ganawa da al'umma garin, to bayan ziyarar wadansu gurare Jagoran ya gabatar da wani jawabi mai muhimmanci a gaba ga dubban al'ummar garin da suka taru. Abin da ke biye fassarar Jawabin ne:

Jagora - Imam Khamene'i A Garin Waramin Yayin Ibada, Jawabi da kuma Karbar Kyauta daga iyalan shahidai

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu, Annabinmu kuma abin kaunarmu Abil Kasim al-Mustafa Muhammad (s.a.w.a) da kuma Alayensa tsarkaka, musamman ma Bakiyatullah (Imam Mahdi), rayukanmu su kasance fansa gare shi.

Ina gode wa Allah Madaukakin Sarki saboda wannan dama da Ya bani na ziyarar wannan gari mai tsarki da kuma ziyartarku Ya ku mutanen wannan gari madaukaka. Na zabi wannan ziyara ta kasance ne a wannan wata na Khordad (Yuni) saboda muhimman abubuwan da suka faru a wannan watan. Hakika watan Khordad ga garin Waramin wata ne da ba za a taba mancewa da shi ba, don kuwa mutanen garuruwan Waramin, Peshwa, Karjak, Jawad Abad da Pakdosht madaukaka, mutane ne da imaninsu, azama da iradarsu sun kasance abubuwan da suka tabbatar da girman wannan yanki, wannan dai shi ne hakikanin lamarin. Tun daga ranar da daya daga cikin 'ya'yan Imam Musa bn Ja'afar (al-Kazim), wanda ake kira Ja'afar bn Musa (a.s) ya iso wannan wuri jina-jina saboda hare-haren da makiya suka kai masa, kana kuma al'ummar Waramin suka karbe shi hannu bibbiyu har lokacin da ya yi shahada saboda raunin da ya samu, muke ganin riko hannun bibbiyu da koyarwa ta Musulunci a tsakanin al'ummar Waramin, musamman ma dai ga abubuwan da suke bukatuwa da azama mai girma.

A ranar 15 ga watan Khordad na 1342 (hijira shamsiyya) al'ummar Waramin sun tabbatar wa duniya kudurinsu na sadaukar da duk abin da suka mallaka, ko da rayukansu ne a tafarkin tabbatar da gaskiya da kuma kare Musulunci. (A wannan rana ce dai) al'ummar Waramin suka taru a haramin Ja'afar bn Musa (a.s), inda suka yi alkawari wa Ubangiji kan ci gaba da jihada, daga nan kuma suka nufi garin Tehran, to sai dai kuma a hanyarsu sun gamu da hare-haren jami'an tsaron tsohuwar gwamnatin 'yan gidan sarautar Pahlawi na SAVAK, inda suka fada musu da kuma zubar musu da tsarkakan jinannakinsu da ya jika kasar yankin Bakir Abad da Karjak, inda suka yi shahada.

A wancan lokacin dai babu wani mutum da zai yi tsammanin cewa wadannan shahidai da aka zalunta wadanda kuma aka mance da su za su bayyana a sama kamar tauraruwar zahra mai haske, ba wai kawai a yankin Waramin ba har ma dai a duk fadin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran. Allah Ya albarkaci wannan sadaukarwa tasu, sannan kuma Ya sanya wannan tsayin daka da jihadi nasu ya ci gaba da yaduwa har ya haifar da wasu gwagwarmayoyi a kowace rana har suka kai abin da ake gani a yau.

A yau din nan a duk lokacin da muka kalli garin Waramin, za mu ga cewa gwagwarmayar al'ummar yankin ba ta dakata ba, ba ta dakata daga shahidan 15 ga watan Khordad 1342 ba, a daidai lokacin da wasu suke tsayawa kawai akan abubuwan da suka wuce. Addinin Musulunci dai ya wajabta mana kokari wajen haifar da tabbatar da sabbin ci gaba, yana mai bayyana hakan a matsayin hanya ta isa zuwa ga kamala.

Baya ga shahidan da suka sadaukar da kawukansu a wancan lokacin, al'ummar yankin Waramin dai sun bayar da shahidai 32 a yayin kallafaffen yakin da Iraki ta kallafa wa Iran, baya ga kwamandojin soji, lalle hakan kuwa a ba karamin abu ba ne.

Wannan yankin dai ya kaddamar da shahidai madaukaka da dama na daga kwaman-doji da jaruman sojojin sama da dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci, akwai wasu iyalai ma da suka ba da shahidai biyu zuwa uku daga cikin 'ya'yansu. Allah Ya yi rahama ga ma'abucin addinin nan madaukaki Sheikh Junaidi, wanda ya ba da shahidai uku daga cikin iyalansa, kai ana cewa ma hudu ne idan aka hada da karamin dansa dan shekaru 4 wanda ya sami rauni saboda makamai masu guba na abokan gaba, kamar yadda aka sanar da ni. Akwai sauran wasu iyalan ma, kamar iyalin shahid Sattari, shahid Urdustani, shahid Ali al-Kummi da dai sauran iyalai madaukaka wadanda suka kaddamar da kawukansu da na iyalansu a matsayin shahidai.


A halin da ake ciki abin da Amurka take son haifarwa shi ne wani irin nau'i na mulkin kama karya a duniya; sai dai kuma sun mance da cewa al'ummomin duniya ma'abuta 'yanci ba za su taba amincewa da hakan ba kuma ma za su fuskanci wannan kama-karya da aka samar da shi da karfin bindiga da kuma ganin bayansa. Al'ummar da take da 'yanci da daukaka, ba za ta taba amincewa da mulkin kama-karya ba, kamar yadda al'ummar Iran ba su amince da gwamnatin dagutanci ta Shah ba, to ina ga mulkin bakin haure kuma!

Wannan dai shi ne yanayin wata al'umma daga cikin al'ummai, yanayi na wani gari daga cikin garuruwa, yanayi na wata kasa daga cikin kasashe, duk da haka dai wasu sun so su yi wasa da irin wannan yanayi da matsayi na mu na 'yan kasantaka da kuma tarihi, suna so su kai mu su baro daga wannan daukaka tamu. Hakika daya daga cikin abubuwan da suke sa al'umma su kasance tsaye da kafafunsu shi ne dogaro da abubuwan alfaharinsu da suka gabata, ba wai kawai da nufin tsayawa akan wadannan abubuwan ba, face dai da nufin samar da wasu sabbin abubuwan alfaharin. Wannan dai shi ne abin da ya haifar da nasarar Juyin Juya Halin Musulunci da kuma kafa tsarin Musulunci.

Ya ku wadannan matasa madaukaka! Ya ku 'ya'yana madaukaka wadanda ku ne kuka fi yawa a wannan taro namu! Ya kamata ku san cewa a da babu wani mutum da ke tunani kai ko ma da mafarki ne na samar da tsarin Musulunci a wannan kasa ta ku (Iran), babu wani mutum guda da ya yarda da hakan, ba wai kawai a nan ba, hatta ma a duk fadin duniyar musulmi, babu wani mutum guda da ya yarda cewa wata al'umma za ta iya kira da kuma fitowa da sunan Musulunci, ta daga tutar Musulunci sama da kuma kiran dukkanin duniya zuwa ga adalci da 'yanci na Musulunci. Hakan kuwa ya faru ne saboda irin takunkumi da yanayin da aka sanya al'ummar musulmi ciki, shin wani mutum ne ya ke wannan tunani? To amma hakan dai ya tabbata, kuma ba wai haka kawai ne ba shiri ya faru ba.

Lalle akwai wasu dalilai cikin wannan abu da ya faru da ya sa Allah Madaukakin Sarki ya tabbatar da faruwar wannan babban lamari na tarihi, wanda kuma ya samo asali ne daga irin azama, kokari da kuma farkawa na wannan al'umma tamu, wanda hakan na daga cikin wadannan dalilai da suka dinga faruwa daya bayan daya.

A wancan lokacin dai akwai wadansu da dama da suke kokarin karya gaban al'umma da kuma mujahidai, suna masu cewa: wannan abin da kuke yi dai ba shi da wani amfani; zahirin al'amurra dai yana tabbatar da abin da wadannan mutane suke fadi. (A wancan lokacin) wani adadi na matasan kauyuka da garuruwa sun sadaukar da jininsu a kan gadar Bakir Abad, amma babu guda daga cikin masu ikirarin kare hakkokin 'yan'Adam da 'yanci da ya ce uffan ga gwamnatin Pahlawi da ta aikata wannan danyen aiki. Har ila yau kuma a daidai wannan rana ne dai jami'an tsaron gwamnatin Pahlawi suka bude wuta kan wasu dubban matasan garuruwan Tehran da Kum, inda suka kashe wasu dubbai, to amma wadannan masu da'awar karya ta kare hakkokin 'yan'Adam ba su ce komai ba. Shin wane ne ya ke tunanin cewa wata rana wannan zalunci da zubar da jini zai daukaka da kuma bayyana a fili kowa ya gan shi. A zahiri dai masu kokarin sanya waswasi cikin zukatan mutane sun yi kokarin hakan, to sai dai kuma tsayin daka da himma ya sanya abin da ake ganin ba zai yiyu ba ya yiyu.

A yau ma dai haka lamarin yake, dukkan hanyoyin farfaganda na duniya an daga su sama don a nuna wa al'umman Iran da ma sauran al'ummomin kasashen musulmi cewa wannan farkawa ta Musulunci da suka samu ba shi da wani fa'ida kuma babu inda zai je, kuma wannan tsari na Musulunci ma dake Iran bai iya sauke nauyin da ke kansa ba. Bari in gaya muku, dukkan abin da za su iya sun yi kuma za su ci gaba da yi, to sai dai kuma da ikon Allah, ba za su ci nasara ba, kuma da sannu za su wulakanta.

Himmansu na farko dai shi ne kokarin karya gaba da sanya al'ummar Iran su yanke kauna. Ina son in sanar da dukkan al'ummar Iran da ku madaukakan al'ummar Waramin cewa duk wani mutumin da aiki da halayensa ya sanya al'umma suka yanke kauna to ya san cewa ya taimaka wa makiya, ko mene ne aikinsa kuwa. Sabanin abin da suke cewa wai ba wanda zai iya fuskantar dakarunsu. Wadannan mutane cewa suke wai dakarun Amurka dakaru ne da ba za a iya ja da su ba, sun tabbatar wa zukatansu cewa Afghanistan ta gagara ja da su, haka ma kasar Iraki. To sai dai abin da ba sa fadi shi ne irin ha'inci da wasu suka yi (da ya kawo faduwan wadannan gwamnatoci); ba sa fadin wace irin gwamnatoci ne a wadannan kasashe; ba sa fadin yadda al'ummomin wadannan kasashe suka kosa da wadannan gwamnatoci nasu na kama-karya; kamar yadda kuma ba sa fadin irin sadaukarwa da tsayin dakan da al'ummar Iran suke nunawa wajen kare mutumcin Musulunci da kuma gwamnatin Musuluncinsu. Wadannan mutane dai duk ba sa fadin wadannan abubuwa, abin da kawai ya dame su shi ne razanar da mutane.

A halin da ake ciki dai kafafen yada farfagandan abokan gaba sun bude bakunansu wajen sa al'umma su yanke kauna da kuma tsorata su. To ni dai a nan a fili ina son sanar da al'ummar Iran cewa babu guda daga cikin wannan barazana da sanya yanke kauna da ke bisa kan hanya ballantana ya cimma manufa, dukkansu biyun kuskure ne, kamar yadda kuma zancen cewa ba za a iya fuskantar dakarun abokan gaba ba zance ne kawai na wauta kuma kuskure ne. Hakika da a ce Amurka za ta iya kawar da gwamnatin Musulunci na Iran, to da ba ta bata lokaci ko da na minti guda ba wajen aikata hakan. Abin da jami'an Amurka suke fadi a halin yanzu na cewa yaki ba shi ne hanyar da za su bi wajen yin galaba akan Iran ba, ai gaskiya suke fadi, don kuwa yaki da Iran a gare su ba zai kasance kamar yakin da suka yi da Iraki ba. Saboda a Iran dai akwai jaruman al'umma wadanda za su fuskanci abokan gaba da dukkan karfinsu da kuma janyo musu hasarori masu girman gaske.

Hanyar da suke son bullo wa Iran daban ne, kuma wannan wani lamari ne da a shekarun baya a jawabai da wasiyyoyi na musamman da na ke wa jami'an gwamnati na sha fadi da kuma ishara gare shi, amma wasu 'yan adawa suke cewa wannan ba wani abu ba ne face kawai wani tunani maras tushe, to amma a hakikanin gaskiya abin da suke tunani shi ne tunani maras tushe, don kuwa a halin yanzu ga su su kansu Amurkawan suna fadin hakan, suna cewa mu abin da muke so shi ne haifar da rikici a cikin Iran. Aikinsu dai shi ne haifar da sabani da rashin jituwa tsakanin al'umma da jami'an gwamnati. Abin da dai suke son yi shi ne idan suka sami wasu mutane wadanda suke cikin fushi (saboda wasu dalilai) kana kuma suke shirye su tada hankali da kuma zama 'yan amshin shatan (Amurkawan), nan take ba tare da bata lokaci ba za su goya musu baya. Idan suka sami wani adadi na mutane suka daga muryoyinsu a daya daga cikin lunguna, sai su kuma su daga nasu muryoyin a duniya su ce mu muna goyon bayansu. Lalle gaskiya suke fadi, su ne dai masu goyon bayan duk wani tashin hankali da kawo sabani tsakanin al'umma, wannan dai shi ne abin da nake fadi 'yan shekarun da suka wuce, amma wasu marubuta da 'yan jaridu suka ta rubuta wasu maganganu kan hakan cikin jaridunsu, duk da cewa gaskiyar dai ita ce abokan gaba dai suna kokarin haifar da sabani da rikici ne tsakanin al'umma.

Don haka, dole ne al'ummar Iran, musamman ma dai matasa, su kasance cikin hankulansu, kamar yadda kuma dole ne jami'ai su ma su yi hankali, dole ne su yi hankali. A daidai wannan lokaci ina son jawo hankali da yin wasiyya ga matasa muminai, ma'abuta 'yanci kana kuma dakarun Hizbullah a duk fadin kasa da cewa: Ku yi hankali kada ku fada tarkon wadansu mutanen da suke share fagen rikici da sabani tsakanin al'umma, a'a hakan bai kamata ba. Kada ku bari wadansu mutane su lalata muhallin jami'a da sauran yankuna na kasa da sabani da rikici kana daga baya su ce muminan matasa daliban jami'a ne suka aikata hakan, lalle kada ku bari hakan ya faru. Al'ummar Iran dai idan har suna son fuskantar wadannan masu son tayar da fitina, to za su yi hakan ne ta tafarkin da suka bi a ranar 23 ga watan Tir shekara ta 1378 (hijira shamsiyya).

Da ikon Allah, farkawa da kuma karfafawar tabbataccen imani wannan al'umma, jami'an gwamnatin wannan kasa ba za su taba barin Amurka ta cimma buri da manufofinta a wannan kasa ba.

To a halin yanzu dai da wadannan abokan gaban al'ummar Iran, wato gwamnatin da ke mulki a halin yanzu a Amurka da kuma yahudawan sahyoniya 'yan fashin kasar Palastinu, a fili sun fadi cewa ba abin da suke son haifarwa a Iran in ban da fitina da tashin hankali, to dole fa hukumomi da jami'ai su tsaya da kafafunsu, su yi hankali da kuma sanya ido kan abubuwan dake gudana. Da farko dai na ce al'ummar Iran ba za ta taba yin rahama da tausayawa 'yan amshin shatan abokan gaba ba, to a halin yanzu ma zan fadi cewa jami'an gwamnati, wadanda su ne wakilan al'umma, ba su da hakkin yin rahama da nuna tausayawa ga 'yan amshin shatan abokan gaba.

A yau dai a'ummarmu dai tana bukatuwa da aiki da kuma kokari ba dare ba rana wajen ci gaban kasa. Abin da mai girma shugaban lardin Waramin ya fadi anan dangane da matsalolin wannan gari, irin wadannan matsaloli ko kuma makamancinsu muke fama da su a da dama daga cikin garuruwan wannan kasa tamu, wadannan abubuwa dai suna bukatuwa da tsare-tsare masu kyau daga jami'ai, wadanda a halin yanzu ma dai suna yin hakan, wajen magance wadannan matsaloli, duk wani wanda kuma ya saba wa doka to a hukumta shi; wannan dai shi ne aikin jami'an gwamnati. Sai dai kuma duk wadannan abubuwa suna bukatuwa da yanayi mai kyau na tsaro da zaman lafiya.

Akwai wadansu mutane da suke son lalata yanayi da haifar da sabani, ba sa so su ga an aiwatar da wadannan ayyuka (na ci gaba), ba sa so su ga an gina kasa, ba sa so su ga jami'an gwamnati da masu tsare-tsare sun yi nasara. Akwai wadansu 'yan tsirarru "wadanda akwai cuta a zukatansu" da suke nan da can, a wasu lokuta ma sun kafa shekarsu cikin hukumomin gwamnati, ba abin da suke yi sai yada maganganun abokan gaba, suna lalata yanayin zamantakewar al'umma da kuma hana aiwatar da ayyukan ci gaba.