Ayyukan Mai Girma Imam Khamene'i (H) Na Yau Da
Kullum
|
-30 Ga Yulin
2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Yayin Ganawa da Matasan Garin Ahwaz da ke Kudancin Iran:
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H)
ya bayyana cewa iradar al’ummar Iran ta mikewa wajen kare manufofi, mutumci da kuma ‘yancinsu wata falala ce ta Ubangiji,
don haka ya hau kan jami’an da al’ummar Iran din su kula da wannan babbar falala
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan (30 Yuli 2003) a yayin da yake maraba ga dubban matasan garin Ahwaz
da ke Kudancin Iran din wadanda suka kawo masa ziyara a gidansa da ke birnin Tehran.
A cikin jawabin nasa Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya ce: “Babban dalilin da ya sa Amurka take gaba da
Musulunci shi ne kiran da Musuluncin ya ke yi wa al’umma na su kare ‘yanci, mutumci, hakkoki da kuma manufofinsu na ‘yan kasanci.
Har ila yau kuma Jagoran ya ce: Amurkawan suna kokarin amfani da kafafen watsa labarai da farfagandojinsu wajen
gaba da kuma shafa wa Musulunci kashin kaza, suna masu cewa gaban da suke yi da wannan bayyanannen addini na Musulunci yana komawa ga kiran da Musuluncin ya ke yi ga yaki, tayar
da fitina, take hakkokin ‘yan’Adam, ta’addanci da kuma adawa a duniya. To sai dai kuma Jagoran ya ce duk da hakan Amurkawan sun gagara cimma wannan manufa ta su yana mai cewa:
"Sai dai babu wanda ya yarda da wannan gagarumar karya ta su, don kuwa Musulunci ya barranta daga wadannan abubuwa. A halin yanzu dai kowa ya riga da ya san cewa Amurka ita ce ta ke
kirkiro yaki da zaluntar sauran al’ummomi, kamar yadda kuma ita ce ta ke aikata ayyukan ta’addanci da gaba tsakanin al’umma a duk fadin duniya".
Yayin da kuma ya koma kan zargin da Amurkan take wa Iran kan daure wa ta’addanci gindi da kuma take hakkokin ‘yan Adam,
Imam Khamene'i ya ce: Ummul aba’isin din rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka, shi ne cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana son ta kasance kasa ce mai cin gashin kanta wacce al’ummarta
ne suke zaban abin da ya dace da su, ba wai su kasance bayin manyan kurayen duniya ba, don haka ne riko da Jamhuriyar Musulunci tamkar riko da kula da ‘yanci da hakkokin al’umma ne”.
Ayatullah Khamene'i, yayin da ya koma kan mamaye kasar Iraki da Amurkan ta yi, cewa ya yi: “Irin munanan ayyukan Amurka
a kasashen duniya daban-daban ciki kuwa har da Iraki ya sanya al’ummomin duniya suka kara kin Amurkan a kowace rana.
Jagoran har ila yau ya ce duniya dai ta ga irin ikirarin kare hakkokin al’umma na karya da Amurkan ta ke yi a kasar Iraki,
dalilin irin dankara wa al’umma gwamnatin da Amurkawan suke so, sace dukiyoyin al’umma, haifar da rashin tsaro, take hakkokin al’ummar Iraki da kuma cin mutumcin mutane, wanda duk hakan suna
nuna wa al’umma hakikanin Amurkan ne.
Daga karshe Jagoran ya yi kira ga matasan da su ba da himma wajen samun cikakken ilmi da masaniya don taimakon kansu da
kasarsu da kuma, da kuma yin kafar ungulu wa abokan gaba wajen cimma burorinsu. |
|
-21 Ga Yulin
2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Yayin Ganawa da Minista da kuma Jami'an Ma'aikatar Tarbiyya da Ilmi Mai Zurfi:
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H)
ya bayyana cewa babban aikin ma'aikatar ilmi shi ne tsara tsare-tsaren da suka dace wajen tarbiyya da kuma gina shaksiyyar matasa.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan (21 Yuli 2003) a ganawar da ya yi da minista da kuma
jami'an Ma'aikatar Tarbiyya da Ilmi mai Zurfi na Iran a gidansa dake birnin Tehran.
Yayin da kuma yake ishara da cewa aikin farko da ma'aikatar tarbiyyar za ta yi wajen tarbiyyantar
da matasa shi ne kwadaita musu samun yanayi mai kyau a nan gaba da kuma nuna musu hakikanin yanayin Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah Khamene'i cewa
ya yi: A halin yanzu, farfagandan kasashen duniya sun hadu ne wajen sanya shakku tsakanin matasa, don haka dole ne a rayar da shirye-shiryen da suka dace
na tarbiyya da koyarwa da kuma shu'uri da Ubangiji da kuma kawar da dukkan wata shakka cikin zuciyar matasa.
Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin yayin da yake bayani kan irin 'yancin siyasa da Iran take ciki
a halin yanzu wanda ya samo asali daga albarkar Juyin Juya Halin Musulunci da kuma kira da a tsara tsarin da ya dace wajen sanar da matasa matsayin Juyin
Juya Halin Musulunci, ya bayyana cewa: Bayani kan hidimar da ake yi da kuma irin ci gaban da kasa ta samu a bangaren tattalin arziki, 'yancin siyasa da
dai sauransu da aka samu bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci ya zama dole don matasan su san irin matsayi da ni'imar da Allah ya yi musu.
Yayin da kuma yake ishara da irin gagarumar rawar da salla take takawa wajen kyautata dabi'un matasa,
Imam Khamene'i ya ce: Dole ne a samar da yanayi da ya dace a makarantu don kwadaitar da matasa kan sauke farali.
Kafin jawabin Jagoran dai sai da ministan tarbiyya da ilmi mai zurfi na Iran din ya gabatar da rahoto
kan ayyukan ma'aikatar tasa da hukumomi da ma'aikatun da suke karkashinta suka gudanar a duk fadin kasar. |
|
-20 Ga Yulin
2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Yayin Ziyara da Kuma Mika Wasu Makamai Ga Dakarun Kare Tsarin Musulunci:
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kana kuma babban kwamandan sojojin Jamhuriyar Musulunci
ta Iran Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya jaddada cewa tsarin Jamhuriyar Musulunci da kuma kafa shi da aka yi a bisa tsari na hankali da kuma
dogaro da karfi irin na ruhi yana tabbatar da kariya ga yanayi na ‘yan kasantaka, Musulunci da kuma ‘yancin al’umma kuma koda wasa ba zai mika wuya ga duk
wata barazana da take fuskanto Juyin Juya Halin Musuluncin ba
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau (20 ga watan Yuli 2003) a ziyarar da ya kai wajen bukin
kaddamar da kuma mika wasu makamai ga dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci , inda yayin da yake bayani kan banbancin da ke tsakanin “tunani na hankali da
ya dogara bisa adalci da dan’Adamtaka” da kuma “tunani na karfin abin duniya da ya dogara kacokam a kan dunniya ya bayyana cewa: “Babu shakka nasara ta karshe
za ta kasance ne ga karfi na hankali”.
Imam Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin, ya ci gaba da cewa: “Hakika al’ummar
Iran da dakarun kasar, masu kare Juyin Juya Halin Musulunci ne ko kuma sauran dakarun kasar, bisa la’akari da karfin ruhi da na duniya da suke da shi a shirye
suke wajen fuskantar abokan gaba a duk lokacin da haka ya taso”.
Jagora ya bayyana cewa a tunani irin ma’abuta karfin fir’aunanci na duniya sun halalta wa
kansu aikata ayyukan cin zalin al’umma da kuma yin karen tsaye wa dan’Adamtaka da duk nau’oi na take hakkokin dan’Adam yana mai cewa Amurka ta kasance babban
misali na irin wannan karfi.
Yayin da kuma ya koma kan babbar manufar Amurka na kokarin tabbatar da karfinta na fir’aunanci,
Imam Khamene'i ya ce irin wannan karfi na zalunci har abada ba zai iya cimma burinsa ba, duk kuwa da irin kokarin cimma hakan.
Jagoran har ila yau ya bayyana tsarin Jamhuriyar Musulunci a matsayin tsarin da ke misalta karfi
irin na ruhi, inda ya ce: “Karfi irin na ruhi ya nuna kansa a Iran cikin shekaru 24 din da suka wanda karfi irin na duniya kuma ya gagara nuna kansa da kuma cimma
manufofinsa a ko ina a duniya kuma muna iya ganin hakan a kasashen Labanon da Palastinu”.
Daga karshe Jagoran ya kirayi dakaru masu kare Juyin Juya Halin Musulunci din da su ba da
muhimmanci wajen karfafa kansu da karfi na ruhi da kuma ma na duniya a lokaci guda.
Kafin jawabin Jagoran, sai da kwamandan dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci Janar Rahim
Safawi yayi bayani kan irin karfin da dakarun suke da shi da kuma shirin da suke da shi na fuskantar duk wata barazana ta bakin haure da dukkan
karfinsu.
Mai son ganin cikakken wannan jawabi, sai ya matsa nan don ganinCikakken Jawabin
|
-16 Ga Yulin
2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Yayin Ganawa da Wasu Matasa Masu Karatun Alkur'ani:
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (h) ya bayyana makomar tsarin Musulunci na Iran a matsayin makoma mai cike da haske
da alheri. Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan (16 ga watan Yuli 2003) a yayin ganawarsa da wasu matasa wadanda aka zaba
don musabakar Alkur'ani mai girma na goma sha biyu.
Jagoran ya ce duk da kokarin makiya amma dai ni ina da imanin cewa irin
ci gaban da matasa suke samu a Iran babu makawa zai jayo hankulan duniya zuwa ga matasan Iran. Har ila yau Jagoran ya ce matasa
Iran ta hanyar fahimta da hangen nesansu za su iya kasancewa abin koyi ga al'ummar musulmi.
Yayin da kuma ya koma kan irin gudummawar da matasan Iran din suka bayar
a lokacin kallafaffen yaki da kuma a fagagen ilmi, Imam Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya ce: Samun matasanmu
a sahun gaba wajen musabakokin kasa da kasa lamari ne da ke nuni da yanayi mai kyau na bayyanar da wadannan matasa.
Yayin da kuma ya koma kan bayyanar da al'ummar Iran suka yi a bangarorin
ilmi tsawon tarihin duniya, Jagoran ya ce irin wannan fahimta da basira ta al'ummar Iran din abu ne abin yabawa cikin tarihin
kasarmu.
Har ila yau kuma yayin da yake nuna rashin jin dadinsa da kokarin da
wasu suke yi na ficewa da matasan Iran ma'abuta basira zuwa kasashen waje, Ayatullah Khamene'i ya ce: Hakika akwai gungun
matasanmu masu basira da fahimta wadanda suke da basira a fannoni daban-daban na ilmi, lamarin da ya kasance abin alfaharinmu,
don haka dole ne a kula da su da kuma samar musu da kyakkyawan yanayi na aiki don taimakawa kasarsu.
|
-28 Ga Yunin
2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Yayin Ganawa da Alkalin Alkalai, Jami'an Ma'aikatar Shari'a da Iyalan Shahidan 7 ga Watan Tir:

|
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya
bayyana cewa dole ne tsarin shari'a ya gudanar da aikinsa na tabbatar
da doka oda don samun yardar al'umma da kuma amincewarsu.
Jagoran ya
bayyana hakan ne a yau Asabar (28 ga watan Yuni 2003) a yayin ganawarsa da
Alkalin alkalai da kuma jami'an Ma'aikatar Shari'a ta kasa da kuma iyalan
Shahidan 7 ga watan Tir da 'yan kungiyar munafukai ta MKO suka kashe,
inda ya ce ya kamata ma'aikatar shari'ar ta nuna gagarumar ci gaba a
kokarin da ake yi na fada da rashin adalci, wanda haka zai jawo hankula
da kuma yardar mutane zuwa gare ta.
Jagoran, yayin da yake bayani kan
wajibcin kawo karshen duk wani nau'i na rashin adalci a cikin Ma'aikatar
Shari'a cewa ya yi: "Al'umma za su amince da aikin Ma'aikatar Shari'ar ne
a lokacin da suka ga Ma'aikatar tana gudanar da aikinta na tono asirin dukkan
wani nau'i na rashin adalci a cikin ma'aikatar".
Jagoran ya kara da cewa: "Dole ne a kawo karshen duk wani nau'i na
rashin adalci komai kashinsa a cikin Ma'aikatar".
Yayin da kuma ya koma kan abin da ya faru a irin wannan rana na kisan
gillan da munafukan suka yi wa Dr. Beheshti da kuma wasu dakarun Juyin Juya Halin Musulunci guda 72, Imam Khamene'i cewa ya yi:
"Faruwar irin wannan lamari na iya kawo faduwar kowace irin gwamnati ce, to amma tsarin Musulunci na Iran, saboda imani da Allah
da kuma goyon bayan al'umma, hakan kara masa karfi da tsayin daka ma ya yi".
Kafin jawabin Jagoran dai sai da Alkalin alkalai na Iran din, Ayatullah
Mahmoud Shahroudi ya gabatar da rahoto kan ayyukan da Ma'aikatar ta yi da kuma irin ci gaban da aka samu.
A wani bangare na jawabin nasa, Alkalin alkalan ya jinjina wa Dr. Beheshti
da sauran shahidan da suka yi shahada a wannan rana, yana mai cewa Dr. Beheshti wani alama ce na adalin alkali da ya ba da rayuwarsa
wajen kare adalci. |
|
-23 Ga Yunin
2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Yayin Ganawa da 'Yan Kasuwa da Masu Masana'antu

|
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i ya yi
kira da da a kwadaitar da 'yan kasuwa wajen sanya hannu cikin
harkokin masana'antu da kamfanoni na cikin gida. Jagoran ya bayyana
hakan ne a yau din nan a yayin ganawarsa da 'yan kasuwa da masu
masana'antu inda ya ce fadada masana'antu na daga cikin ajandojin
gwamnati, don haka ya kirayi gwamnatin da ta ba da himma mai girman
gaske wajen taimaka wa bangaren masana'antun Jagoran ya ce
hukumomin kasa masu kula da da masana'antu an kafa su ne don samar
da ayyukan yi da kuma adalci na zamantakewa. Har ila yau Jagoran ya
yi watsi da ra'ayin cewa karfafa gudummawar da 'yan kasuwa za su
bayar zai raunana yanayin adalci na zamatakewa, yana mai cewa
banbanci tsakanin al'umma zai faru ne kawai a lokacin da 'yan
kasuwan suka sa kansu cikin wasu ayyuka koma bayan ayyukan
masana'antu kana kuma wasu kuma suka dinga dinga tara kazaman
kudade. Imam Khamene'i ya kara da cewa aiki a fannin masana'antu
da ma'adinai na da hatsarin gaske ga masu zuba jari, yana mai kira
ga gwamnati da ta goyi bayan zuba jari a wadannan
bangarori. Yayin da ya koma kan batun zuba jarin 'yan kasashen
waje, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya kirayi wakilan gwamnati
da suke waje da su kwadaita zuba jarin 'yan waje a cikin gida tare
da hadin gwuiwar Ma'aikatar Masana'antu da kuma ta kasashen waje.
Haka nan kuma Jagoran ya kirayi gwamnati da ta rage harajin da aka
sa wa kayayyakin cikin gida, don taimaka wa masu masana'antu na
cikin gida don su kara da na wa je. Kafin jawabin Jagoran, sai da
Ministan Masana'antu da Ma'adinai na Iran Ishak Jahangiri ya gabatar
da rahoton kan ayyukan ma'aikatar da kuma shirye-shiryen da take yi
wajen bunkasa lamarin masana'antu, yana mai cewa ya zuba yanzu
ma'aikatar ta sa ta tsara wani tsari na ci gaban masana'antu a kasar
na shekaru ashirin. |
|
-18 Ga Yunin
2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Yayin Maraba da Shugaban Afghanistan Kharza'i


|
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i ya
jaddada cewa manyan kasashe ma'abuta girman kai kokari suke su
lalata asalin wayewar al'ummomi. Jagoran ya bayyana hakan ne a yayin
da yake maraba wa Shugaban Gwamnatin Rikon Kwaryar Kasar Afghanistan
Hamid Kharza'i a gidansa dake birnin Tehran a lokacin da Kharza'in
ya kai masa ziyarar ban girma. Jagoran ya ce wadannan kasashe masu
karfi da suka fada wa wayewar Musulunci na al'ummar Afghanistan,
suna kuma kokari dora wa al'ummar irin wayewa ta Turai da nufin
tabbatar da ikonsu na har abada a kan al'ummar Afghanistan din, don
haka ya kirayi al'umman da su bude idanuwansu kan wannan makirci.
Har ila yau Imam Khamene'i ya nuna jin dadinsa dangane da irin ci
gaba da Afghanistan din take samu a bangaren tsawo da kuma kwanciyar
hankali yana kiran al'umman da hadin kai don fuskantar irin
matsalolin da yaki ya jawo wa kasar. Har ila yau jagoran kuma ya
bayyana yarjejeniyoyin da aka sanya hannu a kansu a yau din tsakanin
kasashen Iran, Afghanista, Tajikista da kuma Uzbekistan a matsayin
lamari mai amfani, yana mai kiran Shugaba Kharza'in da ya dau
matakan da suka dace wajen kawo karshen noma hodar ibilis da ake yi
a kasarsa Shi ma a nasa bangaren, shugaba Hamid Kharza'i na
Afghanistan din ya nuna jin dadinsa kan irin taimakon da gwamanati
da al'ummar Iran suke wa kasar tasa, yana mai jaddada cewa hadin kan
da ake samu tsakanin Shi'a da Sunna suna daga cikin abubuwan da suka
haifar da zaman lafiya a kasar tasa, |
|
-16 Ga Yuni
2003
Jagoran Juyin Juya Halin
Musulunci A Yayin Ganawarsa da Shugaban Kasar Tajikistan A Tehran
A wannan rana
ce Jagoran Juyin Juya Halin Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i
ya gana da Shugaban Kasar Tajikistan Imam Ali Rahmanov. A yayin
wannan ganawar Jagoran ya yi nuni da irin kusanci da kasashen biyu
suke da shi a bangaren tarihi, al'adu da kuma addini yana mai cewa:
"Addinin Musulunci da kuma harshen Farisanci suna asasai guda biyu
da suka hada al'ummar Iran da Tajikistan, don haka yana da kyau a
karfafa wadannan abubuwa biyu a kullum.
Har ila yau
Jagoran ya bayyana karfafa addinin Musulunci da harshen Farisanci. a
matsayin alamun 'yan kasanci na kasashen Tajikistan da kuma
Afghanista yana mai cewa don kuwa wadannan abubuwa guda biyu sun yi
hidima wa manufofin wadannan kasashen guda biyu, kuma hadin gwuiwa
tsakanin kasashen Afghanistan, Tajikistan da kuma Jamhuriyar
Musulunci ta Iran, saboda irin abubuwa guda da suke da shi, zai
taimaka nesa ba kusa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tabbatuwa
a yankin.
Hakan nan
kuma Imam Khamene'i ya jaddada muhimmancin da ke cikin hadin gwuiwa
tsakanin kasashen musulmi saboda irin abubuwa guda da suke da su,
yana mai nuna jin dadinsa da yarjejeniyoyin da aka sanya hannu kansu
tsakanin Iran da Tajikistan a bangaren makamashi, yana mai cewa ci
gaban kasar Tajikistan din babban hidima ce ga manufofin Iran da
kuma dukkan yankin baki daya.
Haka nan kuma
Ayatullah Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin, ya
siffanta barazanar da Amurka take wa zaman lafiyar duniya a matsayin
tada fitina da dai sauransu, yana mai nuni da irin matsalolin da
Amurkan take fuskanta a kasashen Afghanista, Iraki da kuma
Palastinu, inda ya ce: "A halin yanzu Amurka duk da irin fankaman da
take yi, tana fuskantar faduwa da kuma rugujewa kamar yadda kankara
take narkewa".
Yayin da kuma
yake tofin Allah tsine ga Amurkan kan matsayar da take dauka kan
kasar Palastinu, Jagoran al'ummar Musulmin ya ce: "Maimakon kasar
Amurka ta gudanar da aikin da tace tana yi na mai sulhuntawa, sai
kawai ta shigo filin daga a matsayin abokiyar al'ummar Palastinu da
kuma taimaka wa yahudawan sahyoniya, don haka duk wani bala'in da ya
fada wa yahudawan sahyoniyan to babu shakka zai fada wa Amurkan ita
ma". |
|
-13 ga Yunin
2003
Jawabin Jagoran Juyin Juya
Halin Musulunci A Ganawarsa da Iyalan Shahidai a Garin Waramin
(Kudancin Tehran)
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i ya
bayyana samun ilmin makamashin nukiliyya na gaba gaba a matsayin
wani babban abin alfahari ga al'umma, yana mai cewa hakan kuwa ya
biyo bayan kokari malamai da masana ne a wannan bangaren.
Jagoran ya
bayyana hakan ne a yayin ganawar da ya yi da iyalan shahidai,
wadanda suka sami raunuka a wajen yaki da kuma sakakkun yaki a
ziyarar da ya kai garin Waramin a yau din nan. Yayin da kuma ya koma
kan gaba da Amurka ta ke yi da wannan ci gaban da Iran din ta yi,
Imam Khamene'i ya ce: "Amurka tana fushi saboda ganin cewa al'ummar
Iran sun mallaki irin wanann ilmi mai girma kuma a bisa kokarin
al'ummarta, to amma suna kokarin boye wannan fushi nasu ta hanya
yada tuhumce-tuhumce marasa tushe da cewa Iran tana kera makaman
nukiliyya".
Yayin da yake
ishara da cewa kasar Iran ba ta da nufin mallakan makaman kare
dangi, Ayatullah Khamene'i ya ce: "Matsalar abokan gaba kawai ita ce
ba sa son ganin Iran ta mallaki ilmin makashin nukiliyya, kuma lalle
Amurka ba za ta iya yin komai ba ga hakan kuma ba za ta iya hanawa
ba".
Har ila yau
kuma yayin da yake ishara da irin ci bayan da Iran ta yi a bangaren
ilmi a lokacin mulkin dagutu, Imam Khamene'i cewa ya yi: "A lokacin
da abokan gaba suka fahimci irin karfin da al'ummar Iran suke da shi
a bangaren ilmi da kuma nan gaba fa Iran din ba za ta bukaci wani
taimako na bakin haure ba, sai suka fara makircin neman ta da zaune
tsaye cikin al'umma don su shiga tsakanin irin wannan ci gaba na
ilmi da aka samu a fagen ilmi....".
Haka nan kuma
yayin da yake ishara da irin kokarin da manyan kurayen duniya suke
ni na haifar da rashin fahimtar juna tsakanin al'ummar musulmi,
Jagoran Juyin Juya Halin ya ce: "Hakika irin girmamawar da al'umman
musulmi suke wa al'ummar Iran saboda tsayin dakan da ta yi a gaban
ma'abuta girman kai, da kuma irin kaunar da al'ummomin duniya suke
wa Imam Khumaini(r.a),duk hakan sun samo asali ne saboda daga tutar musulunci da suka yi ne wanda kuma a dalilin hakan suka sadaukar da shahidai"
.
Mai son ganin cikakken wannan jawabi, sai ya matsa nan don ganinCikakken Jawabin
|
|
-11 ga Yunin
2003
Sakon Jagora Ga Taron Kula da
Muhalli
A wannan rana
ce Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatullah al-Uzma Sayyid
Aliyu Khamene'i (H) ya aika da wani sako zuwa ga mahalla taron kula
da muhalli da aka gudanar a birnin Tehran.
A cikin
wannan sako, wanda shugaban ofishin Jagoran, Hujjatul Islam wal
Muslimin Muhammadi Golpaygani ya karanta a madadinsa, Shugaban
al'ummar musulmin ya bayyana cewa gudanar da wannan taro yana nuni
da irin kyakkyawan nufi na 'yan kasanci wajen kare yanayi da muhalli
daga gurbacewa.
Har ila yau a
cikin wannan sako dai Imam Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin
Musuluncin, shirya wannan taro dai yana a matsayin mayar da martani
ne mai kyau ga daya daga cikin bukatun al'umma wajen kara kaimi
wajen kula da yanayi da kuma hakkin dukkan
al'umma.
Jagoran ya ce
manyan kasashen duniya masu karfin masana'antu sun fi mummunan karen
tsaye da kuma cutar da yanayi nesa ba kusa ba da kuma cutar da
hakkokin sauran al'umma na duniya ta wannan hanya na lalata yanayi,
al'amarin da ya haifar da cututtuka daban-daban da suka yi
sanadiyyar mutuwar dimbin al'umma.
Daga karshe
dai Jagoran ya yi fatan alheri ga mahalla taron da kuma fatan za a
cimma sakamako mai kyau a yayin
taron. |
|
|
|
|
|
|
|
Koma Sama
|
| |