Ayyukan Mai Girma Imam Khamene'i (H) Na Yau Da Kullum
(Watan Augustan 2003)


-31 ga Augustan 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jagoranci Zaman Makokin Tunawa da Ayatullah Hakim a Tehran

A safiyar yau Lahadi (31 ga Watan Augustan 2003) ne Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya jagoranci taron zaman makoki da karatun Fatiha ga ruhin Ayatullah Muhammad Bakir Hakim, shugaban majalisar Juyin Juya Halin Musulunci a Iraki da aka gudanar a Makarantar Shahid Mutahari da ke nan birnin Tehran.

Wannan zaman makoki da karatun Fatiha dai da aka yi shi karkashin Jagorancin Jagoran ya samu halartar Shugaban Kasa Sayyid Muhammad Khatami, shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Sheikh Mahdi Karrubi, Shugaban Ma'aikatar Shari'a Ayatullah Mahmud Shahrudi, shugaban Majalisar Fayyace Maslahar Tsarin Musulunci ta Iran Ayatullah Ali Akbar Hashemi Rafsanjani, 'yan majalisar Iran, sauran jami'an gwamnati da na soji da kuma manyan malaman addini na kasar.

Yayin da yake gabatar da jawabi a wajen wannan zaman makoki, babban sakataren majalisar tsaron kasa ta Iran Hujjatul Islam Hasan Ruhani ya ce dole ne Amurka da Birtaniyya su dau nauyin wannan aika-aika na kashe na kashe Shahid Hakim din kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tabbatar.

Sheikh Ruhani, yayin da yake ishara da irin barazanar da ake yi wa malamai a birnin Najaf din da kuma mika lamarin kula da tsaron kasa ga tsoffin jami'an tsohuwar gwamnatin Iraki da sojojin mamayan Amurka suka yi, ya ce: "Dole ne Amurkawan su cikakken bayani kan shigan wasu jami'an leken asirin Haramtacciyar kasar Isra'ila (MOSSAD) cikin garin Najaf cikin 'yan kwanakin nan kafin kisan gillan da aka yi wa Shahid Hakim din.

Sheikh Ruhani ya kara da cewa lalle ya kamata Amurka ta san cewa ta sayi kiyayyar al'ummar musulmi da na Shi'a har abada da kudinsu.

Babban sakataren majalisar tsaron kasar ya yi kira ga al'ummar Iraki da su kare hadin kan da ke tsakaninsu don hakan shi ne kawai zai tabbatar musu da nasara akan abokan gabansu da kuma 'yantar da kasar.

A ranar Juma'an da ta wuce ne dai (29/8/2003) Shahid Ayatullah Hakim ya yi shahada lokacin da wasu motoci guda biyu da aka cika da bama-bamai suka fashe a bakin kofar Haramin Imam Amirul Muminina (a.s) da ke Najaf bayan an gama sallar juma'a a ranar a hanyarsa ta fitowa.



-28 ga Augustan 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Shugaban Kasa da Kuma 'Yan Majalisar Ministocinsa

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya bayyana kauna da goyon bayan da al’umma suke bayarwa ga gwamnati a matsayin ummul aba’isin din ci gaban da aka samu tun bayan nasarar Juyin Juya Halin Musulunci yana mai kiran jami’an gwamnati da su aikata abubuwan da zai ci gaba da rike al’umma da sanya su ci gaba da ba da gudummawa wajen ci gaban kasa.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Laraba (27/8/2003) a yayin ganawarsa da Shugaban kasa, Sayyid Muhammad Khatami da ‘yan majalisar ministocinsa a lokacin da suka kai masa ziyarar ban girma a bukin “Makon Gwamnati” don tunawa da kisan gillan da aka yi wa shugaban kasar Iran Ali Raja'i da Prime Ministansa Jawad Bahonar da wasu jami’an gwamnati a shekarar 1981, inda yayin da yake jinjinawa shugaba Khatami da ‘yan majalisar ministocinsa kan irin hidimar da suka yi wa al’umma ya jaddada wajibcin da ke ciki kara kaimi wajen kyautata yanayin zamantakewar al’umma.

Har ila yau Ayatullah Khamene'i yayin da yake girmama matsayin shahidan gwamnati musamman shugaba Ali Raja'i da Prime minista Bahonar ya jaddada muhimmancin da ke cikin sanar da al’umma irin kokarin da jami’an gwamnati suke yi wajen kyautata rayuwarsu, inda ya ce hukumar radio da talabijin ta kasa da kuma jaridu suna da gagarumar rawar da za su iya takawa a wannan bangaren.

Haka nan kuma yayin da yake nuna jin dadinsa da matakan da gwamnati ta dauka wajen magance matsalar tsadar kayayyaki cikin ‘yan watannin da suka wuce wanda hakan kuma ya sanya al’umma farin ciki, Imam Khamene'i ya bayyana cewa: “Yana da kyau ku ci gaba da wannan kokari na magance matsalar tashin farashin kayayyaki kamar yadda kuka yi a watannin baya”.

Imam Khamene'i har ila yau ya bayyana kokari wajen kyautata rayuwar al’umma da kuma gyara kasa a matsayin asalin nauyin da ya hau kan gwamnati, inda ya kara da cewa: “Duk da cewa ko ba dade ko ba jima al’umma za su ga ayyukan da gwamnati take yi, to amma fa yana da muhimmanci gwamnati ta ba da muhimmanci wajen magance matsalolin al’umma na yau da kullum cikin gaggawa da kuma taka tsantsan”.

Yayin da kuma yake ishara da aiwatar da adalci da kuma fada da fasadi, rashawa da kuma nuna banbanci a matsayin abubuwan da za su tabbatar da al’umma a fagen siyasa da ba da gudummawa wajen ci gaban gwamnati, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci cewa ya yi: “Babban nauyin da ya hau kan jami’an gwamnati shi ne kokari wajen tabbatar da adalci, kuma halalcin kasantuwan kowani jami’in gwamnati a kujerar da yake kai ya ta’allaka ne da kokarinsa wajen tabbatar da adalci da kuma fada da fasadi. Don haka duk wani jami’in da ba ya ba da himma wajen tabbatar da adalci da fada da fasadi, to bai halalta ya zauna a kan kujerar da ya ke kai ba”.

Yayin da kuma yake jaddada wajibcin kula da kyautata rayuwar duniyar al’umma tare da kula da kuma lamurran lahiransu, Ayatullah Khamene'i cewa ya yi: “Samarwa al’umma rayuwar duniya ya ta’allaka ne da tabbatar da adalci a tsakankanin al’umma, don kuwa idan har aka samar da karuwar hanyoyin samun kudade shiga wa kasa amma kuma ba a kula da adalci da tsoron Allah ba, to wadansu ‘yan tsirarru ne kawai za su ji dadi, alhali kuwa abin da Musulunci ya ke kira gare shi shi ne samun jin dadi ga dukkan al’umma ba wai wasu ‘yan tsirarru ba”.

Haka nan kuma a wani bangare na jawabin nasa Jagoran ya jaddada wajibcin yin waje da bara gurbin jami’ai daga fagen jagoranci don ba wa na kwarai daman ba da tasu gudummawar.

Yayin da kuma yake kiran jami’an da su guji haifar da rikice-rikicen siyasa don al’umma su ci gaba da kasancewa tare da jami’an da kuma tsarin Musulunci da ke mulki a kasar, Imam Khamene'i ya ce: “Rikice-rikice da kace-nace na siyasa maras amfani ba abin da zai haifar in banda dagula fagen siyasar kasa kuma daga karshe hakan zai cutar da gwamnati da tsarin Musulunci ne, don haka wajibi ne jami’an gwamnati su nesanci haifar da irin wannan yanayi”.

Kafin jawabin Jagoran, sai da shugaban kasa Sayyid Muhammad Khatami ya gabatar da jawabinsa da kuma gabatar da rahoto kan irin ayyukan da gwamnatin tasa ta aikata don kyautata rayuwar al’umma.

Shugaba Khatami, yayin da yake jinjina wa shahidan Juyin Juya Halin Musulunci da kuma na kallafaffen yaki musamman ma dai tsohon shugaba Raja'i da prime minista Bahonar, ya bayyana cewa: “Wadannan mutane biyu sun kasance babban misali na hidima wa tafarkin Allah da kuma al’umma ba tare da gajiyawa ba, don haka muna fatan za mu yi koyi da su wajen tabbatar da manufofin Juyin Juya Halin Musulunci”.

Har ila yau kuma bayan jawabin shugaba Khatamin, ministocin gwamnatinsa ma daya bayan daya sun gabatar da rahotannin ayyukan da suka yi wa Jagoran.

Bayan kare dukkan wadannan jawabai kuma Jagoran ya jagoranci jami’an gwamnatin sallolin azahar da la’asar kafin nan kuma aka watse.



-24 ga Augustan 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayi Allah Wadai Da Kokarin Kashe Ayatullah Muh'd Sa'id Hakim

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ofishin daya daga cikin maraja’an shi’a na kasar Iraki Ayatullah Sayyid Muhammad Sa’id Hakim da ya yi sanadiyyar kashe wasu mutane uku da raunana wasu guda goma, ciki kuwa har da shi Ayatullahin.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan 24 ga watan Augustan 2003 cikin wata wasika da ya aike wa Shugaban majalisar koli ta Juyin Juya Halin Musulunci na Iraki Ayatullah Sayyid Bakir Hakim.

A cikin wannan wasika dai Jagoran ya ce: “Mujiriman da suka kai wannan hari, wani kokari ne suke yi na raunana makarantun Hawzan birnin Najaf da kuma yin barazana ga matsayin manyan malamai”.

Jagoran ya kara da cewa: “Irin wannan aiki na ta’addanci ba abin da zai haifar in ban da ba wa ‘yan mulkin mallaka daman ci gaba da amfani da karfi akan al’umma da kuma haifar da sabani tsakanin al’ummar Iraki a daidai lokacin da babu abin da suke bukatuwa da shi da yafi hadin kai”.

Har ila yau Jagoran ya ce: “Idan dai har wadanda suka kai wannan hari ba ‘yan amshin shatan abokan gaba ba ne, to kuwa babu shakka mutane ne da suka fada tarkon abokan gaban wadanda suke aikata abin da ya saba wa addini, tunani da kuma kyawawan dabi’u”.

A wani bangare na wasikar tasa, Imam Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya ce: “Muminan al’ummar Iraki za su yi nasara akan abokan gabansu saboda irin taka tsantsan da kuma tsayin dakan da suke da shi, haka nan kuma matukar suka yi riko da Musulunci to babu makawa za su iya karbo ‘yancinsu daga hannun ‘yan mamaya.



-21 ga Augustan 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa Da Jami'an Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya yi kira ga jami’ai da ma’aikatan Ma’aikatar tsaron cikin gidan Iran da su kara kyautata alakarsu da Allah Madaukakin Sarki baya ga irin kwarewar da suke da ita don samun ci gaban a yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau alhamis (21 Augustan 2003) yayin da yake ganawa da ministan tsaron cikin gida da jami’an ma’aikatar.

Yayin da yake jinjinawa irin ayyuka ba dare ba rana dda ma’aikatar tsaron cikin gidan take aikatawa, Imam Khamene'i ya ce: "Wannan kokari dai da jami’an suke yi a halin mafi wahala, da dama daga cikin al’umma da ma wasu jami’ai ba su san ana yinsu ba, to amma Allah Madaukakin Sarki Yana kula da kuma ganin wannan aiki, don haka ya zama dole jami’an ma’aikatar tsaron cikin gidan su girmama wannan falala da matsayi".

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin karfin iko na ilmi da kwarewa da ma’aikatan ma’aikatar tsaron cikin gidan suke da shi da kuma irin hatsarin da aikin nasu yake da shi, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya ce: Shugabanni da sauran ma’aikatan ma’aikatar tsaron cikin gidan dole ne, baya ga kokarin kara kwarewar da suke da ita, su kara karfafa alakarsu da Ubangiji Madaukakin Sarki don kada su mika kai ga duk wani waswasi da kokarin wasa da hankali".

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya ce tunawa da Ubangiji da kuma samun yakinin taimakon Allah suna daga cikin abubuwa na gaba-gaba wajen haifar da sakamako mai kyau a lokutan da ake cikin mawuyaci, inda ya kara da cewa: "Yin taka tsantsan ma dai na daga cikin muhimman abubuwa, don haka dole ne dukkan jami’an gwamnati da hukumomi musamman ma ma’aikatar tsaron cikin gidan su kula da kuma kiyaye wannan abu".

Har ila yau kuma yayin da yake jinjinawa wannan taka tsantsan da kwarewar da jami’an ma’aikatar tsaron cikin gidan suka nuna a lokacin fitinar da ta faru a watan Khordad (a gefen Jami’ar Tehran), Jagoran ya ce: "A duk lokacin da aka samu taka tsantsan cikin ayyuka, to babu makawa makircin abokan gaba ba zai yi nasara ba".

Kafin jawabin Jagoran dai, sai da ministan tsaron cikin gidan na Iran Hujjatul Islam Ali Yunesi ya gabatar da jawabi da kuma rahoto kan ayyukan da ma’aikatar tasa ta aikata.



-19 ga Augustan 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Bukin Zagayowar Haihuwar Nana Fatima al-Zahra (a.s)

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya jaddada wajibcin kyautata alaka da kuma kusanci da Ahlulbaiti (a.s) da kuma irin koyarwarsu.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din Talata (19/8/2003) yayin da yake maraba da tawagar al’ummar Iran da kuma mawakan Ahlulbaiti (a.s) da suka kai masa ziyarar ban girma da kuma taya murnar zagayowar ranar haihuwar ‘yar Manzon Allah kuma shugaban matan aljanna Fatima al-Zahra (a.s) da kuma Mu’assasin Juyin Juya Halin Musulunci Marigayi Imam Khumaini (r.a) wadanda aka haifa a dai-dai wannan rana ta 20 ga watan Jimada al-Thani (19/8/2003).

A yayin da yake gabatar da takaitaccen jawabi Jagoran ya mika sakon taya murnarsa ga daukakin al’umma musulmin duniya saboda zagayowar wannan rana mai albarka.

Yayin da yake kiran al’umma da su kyautata alakarsu da Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a), Ayatullah Khamene'i ya ce: "Dole al’ummar Musulmi su dauki alakar da suke da ita da Iyalan gidan Manzo din a matsayin wata falala ta Ubangiji gare su".

Jagora ya ce: “Yin biyayya ga Allah Madaukakin Sarki wani jigo ne cikin daukakar dan’Adam. Iyalan gidan Manzon Allah (s.a.w.a) sun sami wannan matsayi da suke da shi ne saboda biyayyarsu ga Allah, don haka kuma kuna iya bin wannan tafarki don samun daukaka".

Har ila yau kuma saboda wannan buki na haihuwar Fatima al-Zahra (a.s) Jagoran Juyin Juya Hali din ya yi afuwa wa wasu fursunoni mata, rage wa'adin daurin da aka yi wa wasu da kuma sake wadanda suke kasa da shekaru 18.

Wannan afuwa dai da Jagoran ya yi ya biyo bayan bukatan da Alkalin alkalan Iran din Ayatullah Mahmud Shahrudi ya gabatar wa Jagoran, inda Jagoran ya amince da hakan.

Afuwa din da ta hada da matayen da aka daure su shekaru 15 kuma suka yi kashi daya cikin biyar na wa'adin nasu. Haka nan kuma macen da ba ta da miji (wanda aurenta ya kare) kuma ita ce take rike da 'ya'yanta.

Haka nan kuma wannan afuwa ta hada har da 'yan matan da suke kasa da shekaru 18 a duniya. Sai dai kuma wannan afuwa ba ta hada da matan da aka same su da wasu laifuffuka da suka hada da take hakkokin al'umma, fataucin muggan kwayoyi, fashi da makami, almubazzaranci da kuma cin amanar kasa.



-18 ga Augustan 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Ministan Waje Da Jakadun Iran a Kasashen Waje

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya jaddada cewa: "Jamhuriyar Musulunci Ta Iran ba za ta taba yin sako-sako da barin muhimman akidunta, wadanda su ne alfaharin kasarmu".

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Litinin (19/8/2003) a yayin ganawar da ministan harkokin wajen Iran Sayyid Kamal Kharrazi, jami’an Ma’aikatar Harkokin Waje da kuma jakadun Jamhuriyar Musulunci Ta Iran a kasashen waje, a ziyarar da suka kai masa gidansa da ke Tehran, inda ya ce: "Dole ne jakadu su gudanar da muhimmanci ayyuka a kasashen da suke wajen bayyanar da akidun Jamhuriyar Musulunci Ta Iran cikin hidima da tabbatattun hujjoji".

Imam Khamene'i, yayin da yake jaddada wajibcin kula da aiki, kwarewa, kula, sauri wajen gudanar da aiki da kuma tsare-tsaren da suka dace wajen ci gabantar da aikin diplomasiyya cewa ya yi: "Muhimmin abu cikin siyasar harkokin wajen Iran shi ne kare tsarin Musulunci da kuma tafiya a bisa tafarkin akidun Musulunci, don haka babu wani abin da za a iya musanya asasi da akidun al’umma, wanda shi ne abin alfaharin al’umma, da shi".

Haka nan kuma Mai girma Jagora, yayin da yake ishara da sabbin canje-canjen da aka samu a duniya da kuma bukatar gudanar da kyawawan tsare-tsare a bangaren Ma’aikatar Waje don samun nasara wajen alaka da kasashen duniya, ya yi kira ga Jakadu din da su nuna kwarewa wajen gudanar da ayyukansu.

Imam Khamene'i ya bayyana cewa muhimmin aiki jakada shi ne kula da kare yanayin tsarin gwamnatin Musulunci, inda ya kara da cewa: "Wasu daga cikin dokokin kasa da kasa da ake kafawa a halin yanzu a duniya sun samo asali ne saboda kudurin mulkin mallaka na wadansu kasashe na duniya, wanda yarda da su tamkar yin watsi ne akidunmu na kasa da na Musulunci ne, kuma mu ba za mu taba juyawa da baya daga akidunmu ba saboda neman yardar wasu kasashe na duniya karkashin jagorancin gwamnatin shaidanci da girman kai ta Amurka".

Yayin da kuma yake ishara da matsayin da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran ta ke da shi a halin yanzu a tsakanin kasashe musamman ma dai kasashen musulmi da kuma nuna cewa hakan ya samo asali ne daga irin rikon da Iran din ta yi da akidu na Musulunci, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin cewa ya yi: "Saboda wannan dalili ne ma ya sa ake kara yada munanan farfaganda akan Iran din da nufin sanya ta ta juya daga wadannan akidu nata na Musulunci, don a samu damar rage irin wannan tasiri da Iran din take da shi tsakanin kasashe".

Jagoran ya ce: “Muhimmin hidima wa kasa shi ne riko da akidun Musulunci da na Juyin Juya hali, kuma tsayin daka da kuma riko da wadannan akidu karfafa kasa da manufofinta ne".

Har ila yau yayin da yake jingina irin ci gaban da Iran ta samu a bangarorin siyasa, tattalin arziki, al’adu, ilmi da kuma irin matsayin da al’umma suke da shi a wannan tsari na Musulunci ga wannan tsari na Musulunci da ke iko a kasar, Imam Khamene'i cewa ya yi: "Dogaro da wadannan abubuwa da kuma uwa-uba Allah Madaukakin Sarki muna iya magance dukkan matsalolin da muke fuskanta a bangaren kasa da kasa".

Yayin da kuma ya ke jaddada kudurin Iran na ci gaba da alaka da kasashen duniya da kuma siyasar Iran na rashin neman fada, Jagoran Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya ce: "Amincewa da kasashen duniya abu ne mai kyau, sai dai kuma hakan ba zai ta’allaka da yin watsi da akidun Jamhuriyar Musulunci Ta Iran da mutumcin al’ummar Iran ba".

Hakan nan kuma yayin da ya koma kan matsin lambar Amurka da wasu kasashen Turai ga Iran din na ta janye hannunta daga shirinta na mallakan makamashin nukiliya, Imam Khamene'i cewa ya yi: “Wadannan bukace-bukace dai rashin adalci da gaskiya ne, kuma koda wasa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran ba za ta taba amincewa da wadannan bukatu ba.

Yayin da kuma yake magana kan alaka da Amurka, Mai Girma Jagora cewa ya yi: "Matukar dai Amurka ta ci gaba da alaka da sauran kasashen duniya tamkar bayinta, to nuna duk wani rauni da kuma mika wuya da wadannan bukatu na Amurka, zai kasance babban kuskure".

Har ila yau kuma yayin da yake koma kan kasashen larabawa da kuma siyasarsu kan kasar Palastinu, Imam Khamene'i cewa ya yi: "Cikin shekaru 35 da suka gabata gwamnatocin kasashen larabawa ba su nuna damuwa ta hakika ga lamarin Palastinawa ba, alhali kuwa Amurka ita kuwa ba ta yi kasa a gwuiwa ba wajen ba da cikakken goyon baya da taimako ga haramtacciyar kasar Isra'ila, ko da da rana guda ba su taba kasance tare da larabawan ba".

Kafin jawabin Jagoran dai sai da ministan harkokin wajen Iran din Sayyid Kamal Kharrazi ya gabtar da rahoton aikin da ma’aikatar ta sa ta aikata da kuma irin nasarorin da aka samu a bangarorin alaka da kasashen waje, yana mai cewa duk da irin yanayin da duniya ta ke ciki, to amma bisa dogaro ga Allah Madaukakin Sarki da kuma kwarewar da jakadun su ke da shi an cimma nasarori na a zo a gani.



-06 ga Augustan 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Manyan Jami'an Gwamnati da na Tsaron Iran a Gidansa

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (H) ya bayyana cewa al’ummar Iran da jami’an gwamnatin Musulunci sun kuduri aniyar yin tsayin daka da kuma ci gaba da bin tafarkin ci gaban kasa da daukaka.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Laraba (6/8/2003) a yayin ganawarsa da Shugaban kasa, Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci, Shugaban Ma’aikatar Shari’a, Shugaban Majalisar Fayyace Maslahar Tsarin Musulunci, Membobin Majalisar Ministoci, ‘Yan Majalisa, jami’an Ma’aikatar Shari’a, manyan jami’an Soji da ‘yan sanda da dai sauran jami’an hukumomi da cibiyoyi daban daban na Iran wadanda suka kai masa ziyara, inda yayin da yake bayani kan ci gaban da aka samu da kuma irin abubuwan da suka gaban jami’an, Jagoran ya ce hidima wa al’umma na daga cikin abubuwan alfahari ga jami’an.

A cikin jawabin nasa, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya yi kira ga jami’an da su ba da himma wajen sanar da matasa irin nasarorin da aka samu da kuma irin abubuwan da ake fuskanta don su kasance cikin masaniya kana kuma ya kasance an girmama su.

Yayin da kuma ya koma kan kasar Amurka da kuma ishara da cewa Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila su ne markazin kiyayya da al’ummar Iran, Imam Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya ce: “Hadin kai da hobbasa wajen kare kasa da mutumci su ne kawai hanyoyin da za a bi wajen fuskantar abokan gaba”.

Jagoran ya ce duk wani sassauci a gaban makiya ba abin da zai haifar in ban da karin matsin lamba wa akan Jamhuriyar Musulunci ta Iran din.

Yayin da kuma ya koma kan jami’an da kuma shirin bunkasa tattalin arzikin kasa da gwamnati ta bullo da shi, Jagoran ya ce dole dukkan wasu tsare-tsare da matakai da za a dauka a wannan bangaren su kasance sun yi daidai da tsarin mulki wanda ya ginu a kan tabbataccen turba ta Musulunci.

Har ila yau kuma yayin da yake ishara da cewa dukkan kungiyoyin siyasa na kasa sun yi imani da akidu na Musulunci kana kuma yayin da yake jaddada wajibcin hadin kai don aiki tsakanin jami’an gwamnatin, Imam Khamene'i ya ce: “Dole dukkan jami’an su share amintaccen yanayi wajen zaben share fage na ‘yan majalisa da za a gudanar a Iran din nan gaba”.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Sayyid Muhammad Khatami ya gabatar da jawabinsa.

A yayin jawabin nasa Shugaban Khatami ya yi nuni da irin ci gaban da aka samu a cikin gida cikin shekaru 24 na samu nasasar Juyin Juya Halin Musulunci a Iran, kana kuma ya ce shekaru masu zuwa za su kasance masu haske da daukaka ga al’ummar Iran.

Yayin da yake magana kan farfaganda makiya kan karyar cewa Iran tana kokarin mallakan makaman kare dangi, Hujjatul Islam Khatami cewa ya yi: “Makaman kare dangi ba su waje a shirin Iran na kare kanta, amma fa Iran din ba za ta taba barin kokarin da take yi na amfani da makamashin nukiliya din don amfani al’ummar Iran din ba.

Bayan jawabin kare wannan ganawa dai Jagoran ya jagoranci jami'an gwamnatin sallar azahar da la'asar kafin daga baya kuma suka ci abincin rana tare da Jagoran, kafin aka yi ban kwana da juna.



-01 ga Augustan 2003

Taron Juyayin Shahadar Fatima al-Zahra (a.s) A Husainiyyar Imam Khumaini Dake Gidan Jagora

A daren yau 2 ga watan Jimada Sani (1/8/2003) wanda ya yi daidai da zagayowar daren ranar Shahadar 'yar Manzon Allah Nana Fatima al-Zahra (a.s) an gudanar da bukin juyayi don tunawa da wannan rana da abin da ya faru a "Husainiyyar Imam Khumaini (r.a) da ke nan Tehran karkashin jagorancin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H).

A yayin wannan taro dai wanda ya sami halartar Jagoran da manyan jami'an Jumhuriyar Musulunci ta Iran din da suka hada da Shugaban kasa Sayyid Muhammad Khatami, Kakakin Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Sheikh Mahdi Karrubi, Alkalin Alkalai Ayatullah Sayyid Mahmud Hashemi Shahrudi, Shugaban Majalisar Fayyace Maslahar Tsarin Musulunci Ayatullah Ali Akbar Hashemi Rafsanjani da dai sauran manyan jami'an gwamnati da kuma sauran al'umma,an gudanar da bayanai kan matsayin Fatima al-Zahra da kuma abin da ya faru a wannan rana, kafin kuma mawaka a bisa taimakon dubban mutanen da suka halarci taron sun rera wakokin juyayi da tunawa da abin da ya faru din.

A yayin wannan buki na juyayi dai, kamar yadda da man aka saba kusan dukkan mahalarta taron sun sanya bakaken kaya ne don nuna bakin cikinsu da abin da ya faru din. Haka nan kuma zauren taron ma dai an yi masa ado da bakaken kalle da kuma wasu kalamai dangane da falalar Nana Fatima (a.s) da dai sauransu da ke nuni da irin matsayinta da kuma zaluncin da aka mata. A gobe ma Asabar asalin ranar da Nana Fatiman ta yi shahadan za a gudanar da irin wannan taro a gidan Jagoran.

             

Koma Sama