Ayyukan Mai Girma Imam Khamene'i (H) Na Yau Da Kullum
(Watan Disamban 2003)


-23 ga Disamban 2003

Imam Khamene'i: Alakar Mutanen Senegal Da Musulunci Na Daga Cikin Abubuwan Da Suka Sanya Karfafuwar Alaka Tsakanin Iran da Senegal.

Imam Khamene'i Yayin Da Yake Ganawa da Shugaban Senegal

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa al'ummar kasar Senegal cikin karnonin da suka wuce sun ba da gagarumar gudummawa wajen daukaka Musulunci, kuma irin kaunarsu da musulunci a halin da ake ciki ma na daga cikin abubuwan da suka sanya karfafuwar alakar Iran da Senegal. Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan a yayin da yake ganawa da shugaban kasar Senegal Abdullah Wade da ya kai masa ziyara a gidansa da ke birnin Tehran, inda ya bayyana cewa alaka da kasashen musulmi da kuma na Afirka lamari ne da ke da muhimmanci ga jamhuriyar Musulunci ta Iran sannan kuma ya nuna goyon bayansa ga shirin da kasar Senegal din take yi na karban bakunta taron kasashen musulmi a shekara ta 2007.

Jagoran yayin da yake bayani kan irin matsayi mai muhimmanci da kasar Senegal din take da shi a nahiyar Afirka, yayi fatan za a ci gaba da samun kyautatuwar alaka tsakanin kasashen biyu.

Haka nan Jagoran ya bayyana musanyan ra'ayi da hadin kai tsakanin kasashen musulmi a matsayin babban hanya ta magance matsalolin kasashen musulmi, inda ya kara da cewa: Babu makawa Amurka da HKI suna ganin mummunan sakamako na muggan ayyukansu a kasashen Afghanistan, Iraki da kuma Palastinu.

A yayin wannan ganawa dai wanda shugaban Iran Sayyid Muhammad Khatami ma ya samu halarta, shugaban kasar Senegal Abdullahi Wade ya nuna jin dadinsa da kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu, kana kuma ya yi bayani wa Jagoran irin ci gaban da ake samu a kasar Senegal din.

Har ila yau Shugaba Wade ya ce kasar Senegal dai kasa ce da take dauke da turar musulunci a nahiyar Afirka, kuma a halin da ake ciki muna nan muna ta kokarin ganin mun dauki bakuncin taron kasashen musulmi a shekara ta 2007, wanda muke ganin hakan wani kokari ne na tabbatar da hadin kai tsakanin kasahen musulmi.



-21 ga Disamban 2003

Imam Khamene'i: Kasashen Musulmi Na Da Damar Ci Gabantar Da Musulmi Da Kasashensu Gaba.

Imam Khamene'i Yayin Da Yake Ganawa Da Shugaban Kirkizistan

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewar kasashen musulmi musamman na yankin Gabas ta Tsakiya suna da damar ci gabantar da al'ummar musulmi gaba da kuma hada kai waje guda musamman ma bisa la'akari da irin albarkatun kasa da karfin mutanen da suke da shi.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Lahadi 21 ga watan Disamban 2003 a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Kirkizistan Askar Aghayef da tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma a gidansa, inda Jagoran ya bayyana matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta a halin yanzu ciki har da matsalar Afghanistan, Iraki da Palastinu a matsayin daya daga cikin dalilan da suka wajabta samun hadin kai tsakanin al'ummar musulmi.

Jagoran ci gaba da cewa: Amurka ta hanyar fakewa da batun fada da ta'addanci sun jibge sojojinsu a yankin Gabas ta Tsakiya alhali kuwa wannan mataki nasu ya saba wa hankali da kuma manufofin kasashen Afghanistan da Iraki.

Har ila yau yayin da yake ishara da hanya guda kawai ta tabbatar da tsaro da zaman lafiyan yankin, Imam Khamene'i ya ce: Hanya guda kawai ta magance wadannan matsaloli ita ce ficewar sojojin Amurka daga yankin da kuma mika madafan gudanarwa ga al'ummar yankin.

Yayin da kuma yake nuni da cewa matsalar da Palastinawa suke ciki ya samo asali ne daga irin rikon sakainar kashin da ake wa wannan matsala, Ayatullah Khamene'i ya ce: Kamar yadda shekaru da aka yi ana take hakkokin al'ummar yankin tsakiyar Asiya da tsohuwar tarayyar Sobiyeti ta yi bai haifar da wani sakamako ba, haka ma take hakkokin Palastinawa ba zai dawwama ba, don kuwa a halin yanzu Palastinawa maza da mata yara da manya duk sun fito don fuskantar makiyansu.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban kasar Kirkizistan din ya yi nuni da wajicin kara fadada alaka tsakanin kasashen biyu.

Har ila yau yayin da yake ishara da fadaduwar musulunci da kuma yadda matasa suke komawa gare shi a kasarsa, Shugaba Aghayof ya yi kira da a samu fadaduwa alaka da hadin kai tsakanin kasashen musulmi don cimma wannan manufa.

A jiya litinin ne dai shugaban kasar Kirkizistan din da 'yan tawagarsa suka iso Iran a wata ziyara ta kwanaki biyu a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.



-16 ga Disamban 2003

Imam Khamene'i: Duniya Ba Tare Da Bush da Sharon Ba Za Ta Ti Kyaun Gaske

Imam Khamene'i Yayin Da Yake Gabatar da Jawabi A Gaban Al'ummar Qazwin

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) yayin da yake mayar da martani kan kalamin shugaban Amurka kan cewa duniya ba tare da Saddam Husaini ba, za ta yi kyau, ya bayyana cewa duniya ba tare da Bush (shugaban Amurka) da Sharon (prime ministan haramtacciyar kasar Isra'ila) ba, za ta yi kyaun gaske.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Talata 16 ga watan Disamban 2003 yayin da yake gabatar da jawabi a gaban dubban al'ummar garin Qazwin da ke yammacin birnin Tehran babban birnin kasar Iran, inda ya ce wulakancin da Saddam Husaini ke ciki a halin yanzu abu ne da zai samu dukkan ma'abuta zalunci irinsu Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila.

Jagoran ya kara da cewa na ji shugaban kasar Amurka na cewa duniya ba tare da Saddam Husaini ba za ta yi kyau, to ni ina son in gaya wa masa cewa ya kamata ya san cewa duniya ba tare da Bush da Sharon ba, zai kasance abu kyaun gaske ga dukkan duniya.

Yayin da ya koma kan kamun kazan kukun da aka yi wa tsohon shugaban kasar Iraki Saddam Husaini kuwa, Jagoran ya nuna jin dadinsa ga hakan inda ya ce al'ummar Iran ma musamman iyalan shahidai za su yi farin cikin da jin wannan labari na kace Saddam.

Jagoran har ila yayin da ya ke magana kan irin bayanan da jami'an Iran suka dinga yi a baya kan ta'addancin Saddam da kuma kunnen uwar shegun da kasashen duniya suka yi kan hakan, ya ce: Duniya dai a halin da ake ciki tana ci gaba da ganin hakika kan abubuwan da suke faruwa, don haka ne dukkan al'umman duniya da suka san irin zaluncin wannan dabban daji (Saddam) musamman ma al'ummanmu.

Har ila yau Jagoran ya yi ishara da irin goyon bayan da gwamnatocin Yammacin duniya suka ba wa Saddam wajen yakan Iran da hallaka al'ummarsa yana mai nuni da irin gudummawar da sakataren tsaron Amurka na yanzu Donald Rumsfeld ya bayar a wannan bangaren.

A wani bangare kuma na jawabin nasa Jagoran ya yi kira ga al'ummar Iran din da su fito kwansu da kwarkwatansu don zaman 'yan majalisar da suka dace a zaben 'yan majalisar kasar da za a gudanar nan gaba, yana mai cewa dole ne su zabi mutumin da ya damu da addini, mai ra'ayin juyin juya hali, wanda ya damu da matsalolin al'umma wanda kuma zai biya musu bukatunsu.

Yayin da kuma ya koma kan farfaganda da kuma kokarin yin kafar ungulu da makiya suke yi wajen ganin ba a ci nasara ba a wannan zabe, Imam Khamene'i ya jaddada cewa makiyan dai a wannan karon ma ba za su ci nasara ba kamar yadda suka gagara cin nasara a shekarun da suka wuce.

Daga karshe Jagoran ya gode wa al'umma garin Qazwin din saboda irin fitowar da suka yi kwansu da kwarkwatansu wajen tarbansa da yi masa maraba, yana mai fatan Allah Ya ba shi iko da damar yi wa al'umma hidima duk tsawon rayuwarsa.



-04 ga Disamban 2003

Jagoran Ya Yi Kira Ga Al'ummar Iran Da Su Ba Da Hadin Kai A Shirin Gwamnati na Alluran Riga Kafi

Imam Khamene'i Da Ministan Lafiya

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya yi kira ga al'ummar kasar Iran da su ba da hadin kai a shirin gwamnati na alluran riga kafin bakon dauro.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Alhamis 4 ga watan Disamban 2003 yayin da yake ganawa da ministan lafiya na Iran da jami'an hukumar kasa ta allurar riga kafin bakon dauro, inda yayin da yake kira da taimakawa wannan shiri, Jagoran ya ce: Addinin musulunci ma da kansa yana kira zuwa ga irin wannan hidima ta al'umma.

Haka nan Jagoran ya ce irin wannan hidima ta al'umma tana da matsayi mai girma a wajen Ubangiji.

Yayin da kuma yake godewa ministan lafiya da sauran jami'an Ma'aikatar lafiyan, likitoci, da kuma dakarun Basij da dai sauran dukkan wadanda suke taimakawa a wannan bangaren, Imam Khamene'i yace: "Yana da kyau kafafen watsa labarai su ba da himma wajen karin bayani wa al'umma kan wannan shiri, kuma lalle ne al'umma za su ba da hadin kai wa wannan shiri na taimakon kasa.

Shi ma a nasa jawabin, kafin na Jagoran, ministan lafiyan na Iran ya gabatar da rahoton wannan shirin ga Jgoran. Ministan ya ce: Kimanin mutane miliyan 33 ne za su tsira daga wannan cuta, kuma nan ba da jimawa ba za a samu kawo karshen wannan cuta.

Daga ranar asabar 6 ga watan Disamban nan ne ake sa ran za a fara wanann shiri na alluran rigakafin.



-03 ga Disamban 2003

Imam Khamene'i: Ya Zama Dole Kasashen Musulmi Su Matso Kusa da Juna Don Tabbatar da Manufofinsu

Imam Khamene'i da Shugaban Djibouti

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa: "Duk da kokarin da makiya suke yi wajen haifar da rikici da sabani tsakanin kasashen musulmi, to sai dai duk da haka ya zama wajibi kasashen musulmi su matso kusa da junansu don al'ummar su tabbatar da manufofinsu".

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba 3 ga watan Disamban 2003 a yayin da yake ganawa da shugaban kasar Djibouti Ismail Umar Guelleh da tawagarsa da suka kai masa ziyara a gidansa da ke nan Tehran, inda ya bayyana kyautata alaka tsakanin kasashen musulmi a matsayin daya daga cikin muhimman siyasar wajen Iran.

Yayin da yake ishara da yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin Iran da Djibouti a yayin wannan ziyara, Jagoran ya ce: Fadada alaka tsakanin kasashen biyu zai amfane su ne gaba daya, kuma Iran da Djibouti suna iya amfanar juna a kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa.

A yayin wannan ganawa dai wanda shugaban kasa Sayyid Muhammad Khatami ma yana gurin, shugaban Djibouti ya nuna jin dadinsa da ziyarar da ya kawo Iran din, har ila yau kuma ya mika sakon gaisuwar al'ummar Djibouti ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci da kuma al'ummar Iran.

Daga karshe shugaban ya yi fatar za a ci gaba da samun kyautatuwar alaka da hadin kai tsakanin al'ummar musulmi.



-02 ga Disamban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Yi Allah Wadai Da Harin Da Sojojin Amurka Suka Kai garin Samarra Na Iran

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya yi Allah wadai da kuma kakkausar suka ga hare-haren ta'addancin da sojojin mamayan Amurka suka kai garin Samarra da kuma kisan gillan da suka yi wa al'ummar garin da kuma keta hurumin haramomin Imamai al-hadi da Hasan al-Askari (Imaman Shi'a na 10 da 11).

Jagoran ya yi wannan tofin Allah tsine ne cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Talata 2 ga watan Disamban 2003 inda ya ce wannan aika-aika na Sammarra da sojojin mamayan suka kai inda suka kashe sama da mutane 50 wani lamari ne da ke sosa zukata.

Jagoran, cikin wannan sanarwa tasa, ya ce: "'yan mamayan ma'abuta girman kai sun sake tabbatar da cewa ba su damu da rayukan al'umma ko kuma wuraren masu tsarkinsu ba, suna so ne su yi amfani da karfi da tursasawa".

Jagoran ya ci gaba da cewa: "Wawayen 'yan siyasar Amurka ma'abuta girman kai suna rudin kansu da tunanin cewa za su iya sanya al'ummar Iraki ma'abuta imani da daukaka su mika musu kai da karfin cin tuwo. To sai dai babu shakka wannan wauta da jahilci na su shi ne zai kawo karshensu ba da jimawa ba".

Daga karshe Jagoran ya isar da sakon ta'azziyarsa ga Imam al-Zaman (ATFS) da dukkan al'umman musulmi musamman ma al'ummar Iraki da kuma makarantun Hawza saboda wannan danyen aiki na ta'addanci da kuma rokon Allah da Ya kare musulmi daga sharrin makiyansu.

Kadan Daga Cikin Ayyukan Ta'addanci Sojojin Amurka A Garin Samarra Na Kasar Iraki

Mai Son Ganin Cikakken Wannan Jawabi Na Jagora Yana Iya Matsa Nan (CIKAKKEN SAKON)




-02 ga Disamban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Isar Wa Shugaban Kasa Da Shirin Tattalin Arziki Kasa na Shekaru Hudu

A yau Talata 2 ga watan Disamban 2003 ne Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya isar wa Shugaban kasa Sayyid Muhammad Khatami da wasu shawarwari da hannunka mai sanda dangane da siyasar gwamnati na shekaru hudu kan batun tattalin arziki da ci gaban kasa a shekaru masu zuwa.

Rahotanni daga Tehran babban birnin Iran din sun ce wannan hannunka mai sanda dai sun kumshi hanyoyin da za a bi wajen bunkasa al'amurran al'adu, ilmi, bugu da kari kan abubuwan da suka shafi lamurran zamantakewa, siyasa, tsaro, kariya da kuma alakoki na siyasa da na waje da kuma tattalin arziki.

Cikin wannan sanarwar Jagoran ya jaddada cewa babu shakka wannan hannunka mai sanda na ci gaban kasa cikin shekaru 20 masu zuwa zai taimaka nesa ba kusa ba wajen ci gabantar da kasa da kuma tabbatar da manufofin jamhuriyar musulunci.

             

Koma Sama