Imam Ali Khamene'i
Maudhu'i: Fassarar Sakon Jagoran Juyin Juya Hali IMAM KHAMENE'I (H) Kan Harin Ta'addancin Sojojin Amurka A garin Samarra na Kasar Iraki
Kwanan Wata: 02 Disamba 2003

Shimfida:A cikin wani sako da ya fitar , Jogaran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya yi Allah wadai da harin ta'addancin da sojojin mamayan Amurka a Iraki suka kai garin Samarra na kasar Iraki, da ya yi sanadiyyar kashe sama da mutane 50 da kuma keta hurumin haramin Imam al-Hadi da Askari (Imaman Ahlulbaiti na 10 da 11). Abin da ke biye fassara ce ta wannan sako da Jagoran ya fitar:

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Harin rashin tausayi da 'yan mamaya masu wuce gona da iri suka kai wa al'ummar garin Samarra (na kasar Iraki) da kuma keta hurumin haramin Imam al-Hadi da Askari (a.s) masu tsarki da ya yi sanadiyyar kashe sama da mutane 50 da suka hada da maza, mata, kananan yara da kuma raunana wasu da dama abu ne mai tada hankali.

A wannan karon ma, 'yan mamayan ma'abuta girman kai sun sake tabbatar da cewa ba su damu da rayukan al'umma ko kuma wuraren masu tsarkinsu ba, suna so ne su yi amfani da karfi da tursasawa. Wawayen 'yan siyasar Amurka ma'abuta girman kai suna rudin kansu da tunanin cewa za su iya sanya al'ummar Iraki ma'abuta imani da daukaka su mika musu kai da karfin cin tuwo. To sai dai babu shakka wannan wauta da jahilci na su shi ne zai kawo karshensu ba da jimawa ba.

Ina mika sakon ta'aziyyata ga Imam Mahdi (a.s), al'ummar musulmi musamman al'ummar Iraki da ake zalunta da kuma makarantun Hawzah sannan kuma ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa Musulunci da musulmi nasara (akan abokan gabansu) da kuma rokonSa da ya kare su daga sharrin 'yan mamaya masu wuce gona da iri.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu

Sayyid Aliyu Khamene'i

2 Disamba 2003.


Kadan Daga Cikin Ayyukan Ta'addanci Sojojin Amurka A Garin Samarra Na Kasar Iraki