|
| |||
Daga Muhammad Awwal Bauchi ________________________ Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Sallama gare ku madaukakan al'ummar Iran.
A wannan karon ma fitowar da kuka yi ranar 27 ga watan Khordad (17 ga Yuni) ya sake bayyanar da kuduri da tsayin dakan wannan al'umma ma'abuciyar daukaka sannan kuma kun nuna cewa a shirye kuke wajen ci da kasarku gaba da isa ga manufofinta. Hakika fitowar da kuka yi don kada kuri'a ta sake tabbatar da cewa
demokradiyya ta addini ta samu tsayuwa da kafafunta a wannan kasa da babu wata guguwa ta makiya da 'yan adawa da za ta tumbuke ta. Ta hanyar wannan fitowa taku kun tabbatar wa duniya matsayinku sannan kuma kun amsa mafi girman kiran da kasarku ta yi muku. Har ila yau ta hanyar wannan fitowa, a wannan karon ma, kun karya kashin bayan makircin makiya….
Wawayen makiyanku, sun zaci za su iya razana ku da sa ku yanke kauna ta hanyar farfagandarsu ta karya, wanda a hakikanin gaskiya ma cin mutumci ne ga al'ummar Iran da tsarin Musulunci na kasar. A jawabin riga malam masallaci na shugaban Amurka (wanda ya dare karagar mulki ta hanyar taimakon kamfunan yahudawan sahyoniya don kare haramtattun manufofinsu)
a ranar 16 ga watan Yuni, ya bayyana zabenku a matsayin maras inganci. Babu kunya ballantana tsoron Allah, wannan dan ta'adda mai laifin (gidajen yarin) Abu Ghuraib da Guantanamo ya rufe idanuwansa daga ayyukan ta'addancin da Amurka ke aikatawa a Iraki da Afghanistan, da kuma goyon bayan da gwamnatin Amurkan ta bayar ga gwamnatin kama-karya ta Muhammad
Ridha Pahlawi (Shah) da ya zalunci al'ummar Iran har na tsawon shekaru 25, amma sai ga shi yana tuhumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma nuna cewa gwamnatinsa gwamnati ce da ke son al'ummar Iran da goyon bayan kafa demokradiyya a kasar.
Ya ku madaukakan al'ummar (Iran), Ya ku matasa ma'abuta sadaukarwa, Ya ku maza da mata ma'abuta imani, kun mayar wa Bush da makircinsa sakamakon fitowar da kuka yi ranar zabe, sannan kuma kun bayyana wa duniya da aniyarku ta tabbatar da 'yancin kasarku da kare Musulunci da tsarin demokradiyya na Musulunci. Hakika wadannan kuri'u naku da kuka kada su
cikin akwatunan zabe ga 'yan takaran da kuka zaba da kanku, nuna amincewarku ne ga Jamhuriyar Musulunci, 'yancin kasarku, dokokin kasa, ci gaban adalci da tsarin Musulunci wanda zai lamunce muku lamurran duniya da lahira da kuma 'yanci da daukakar kasarku.
Nauyin farko da ya hau kan kowani dan takaran da ya yi nasara, shi ne kare wadannan manufofi da tabbatar da adalci, kawar da fasadi da 'yan garanci, fada da makirce-makircen siyasa, al'adu da tattalin arziki.
Cikin kaskantar da kai ina mai sujadan godiya ga Allah Madaukakin Sarki saboda shiryar da al'ummarmu da Ya yi, sannan kuma ina gode wa daidaikunku, Ya ku jama'a, saboda sauke wannan nauyi da kuka yi. Don haka ina so in sanar da ku wadansu abubuwa, kamar haka:
1- Wadanda suka yi nasara a wannan zabe su ne al'ummar Iran saboda kunnen uwar shegun da suka nuna wa farfagandar makiya na waje da 'yan amshin shatansu na cikin gida. Bai kamata magoya bayan 'yan takaran da ba su yi nasarar samun damar hidima wa al'umma a matsayin shugaban kasa su ji sun yi hasara ba. A'a kowa ya yi iyakacin kokarinsa kan abin da ya yi
imani da shi, matukar dai an tsarkake wannan niyya saboda Allah to da yardar Allah za a samu sakamako daga wajenSa.
2- A wannan karon ma al'ummar Iran sun sake nuna wa al'ummomin duniya da yankin Gabas ta Tsakiya irin tsarin demokradiyyarsu da ya ginu bisa ra'ayi da gudummawar al'umma ba irin demokradiyyar Amurka da ya ginu bisa karfin bindiga da tursasawa ba. Babu shakka wannan abin farin ciki shi ne ke sosa ran makiya. Don haka ya zama dole ku kiyaye aikata duk wani
abin da zai sanya makiya samun nasarar haifar da fitina tsakaninku da kawar da wannan farin ciki da ake ciki.
3- Shugaban kasar da aka zaba, ko wane ne kuwa, shugaba ne na dukkan al'ummar Iran, don haka dole ne kowa ya ba shi hadin kai wajen ci gaban kasa. Ni ma a nawa bangaren, kamar kullum, zan ba shi cikakken hadin kai wajen aiwatar da ayyukan da doka ta tanadar da kuma kare manufofin gwamnatin Musulunci da yardar Allah.
4- Ina kira ga duk wanda aka zaba a matsayin shugaban kasa, ko wane ne shi, da ya daura damarar hidima wa wannan al'umma musamman matasa da marasa abin hannu wadanda su ne tsarin Musulunci ya fi ba su muhimmanci.
5- Da yake muna farko-farkon shekarar hadin kan kasa da aiki kafada-kafada tsakanin al'umma ne, don haka ina kira ga dukkan al'umma musamman wadanda suke da matsayi na siyasa da shiryar da al'umma, kafafen watsa labarai da dai sauransu da su ba da himma wajen hada kan al'umma da nesantar duk wani abin da zai kawo rarrabuwa tsakanin al'umma.
6- Dole ne in mika godiya ta ga manyan maraja'ai da sauran malaman addini, malaman jami'a, jami'an gwamnati da na al'umma, wadanda suka ba da gudummawa wajen gudanar da zabe musamman hukumar talabijin da radio ta kasa saboda irin shirye-shiryen da suka dinga gudanarwa, majalisar kare tsarin mulki da Ma'aikatar cikin gida da suka shirya wannan zabe da dai sauran
wadanda suka ba da gudummawarsu a wannan bangare da su kansu 'yan takaran.
Daga karshe ina sake gode wa Allah Madaukakin Sarki da kuma neman taimakonSa wajen shiryar da wannan al'umma da wannan bawa nasa mai rauni. Sannan ina rufe wannan kalami nawa da mika gaisuwata ga Waliyullah al-A'azam (Imam al-Mahdi), amincin Allah ya tabbata a gare shi, saboda goyon baya da shiryarwarsa ga wannan kasa da al'umma, wadanda da man mallakansa ne. Har
ila yau, bisa la'akari da cewa wannan zabe ya kai ga mataki na biyu, don haka ina kiran al'umma da a wannan karon ma su fito kwansu da kwarkwatansu wajen kada kuri'arsu.
Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta'ala wa Barakatuhu.
Sayyid Aliyu Khamene'i |
||||