Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Mai Girma Hujjatul Islam Sayyid Hasan Nasrullah (Allah Ya Tsawaita Rayuwarsa)
Ina taya ka da dukkan madaukakan Mujahidan (kungiyar) Hizbullah ta kasar Labanon, iyalan fursunonin da aka sako da kuma al'ummar kasashen Labanon da Palastinu murnar nasarar da gwarazan dakarun Hizbullah na kasar Labanon suka samu wajen 'yanto darurrukan 'ya'yan Musulunci
daga hannun azzaluman yahudan sahyoniya 'yan kaka-gida, sannan kuma ina mika sallama da fatan alheri ga daya bayan daya daga cikin wadannan 'yan'uwa da abokan gaba suka gagara samar da wani gibi cikin imaninsu duk kuwa da irin matsin lamba da azabtarwa irin ta abokan gaba.
Hakika wannan wata jarabawa ce mai girman gaske da ta tabbatar da rashin nasara ga gwamnatin sharri ta yahudawan sahyoniya a gaban nufi mai karfi da imanin Mujahidai a tafarkin Allah da fuskar al'ummar musulmi, kuma hakan ya kara wa azama da fatan matasan musulmi wadanda suka yi amanna da
alkawarin Ubangiji ba Ya saba shi karfi da ci gaba da wannan tafarki na gwagwarmaya.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya ba wa jaruman al'ummomin kasashen Palastinu da Labanon nasara da kuma sako sauran fursunonin Hizbullah (da suke hannun 'yan mamaya), sannan kuma Ya kara maka lafiya da tsawon rai, Ya kai dan'uwa mai girma.
Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah.
Sayyid Ali Khamenei
29/01/2004.