Hudubar Sallar Juma'a Ta Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
(Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu al-Khamene'i)
(Juma'a 11 ga Afrilu 2003)
HUDUBA TA BIYU
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin KaiDukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kuma Annabinmu Abul Kasim al-Mustafa Muhammad tare da tsarkakan iyalan gidansa, musamman Aliyu Amirul Muminina da tsarkakakkiya Fatima, shugaban matan duniya, da Hasan da Husain, shugabannin matasan aljanna, da kuma Aliyu bn al-Husaini Zainul Abidin da kuma Muhammad bn Ali al-Bakir, da Ja'afar bn Muhammad al-Sadik da Musa bn Ja'afar al-Kazim da Aliyu bn Musa al-Ridha, da Muhammad bn Ali al-Jawad da Aliyu bn Muhammad al-Hadi da Hasan bn Ali al-Zakiy al-Askari da al-Hujja al-Ka'im al-Mahdi, amincin Allah ya tabbata a gare su gaba daya. Aminci ya tabbata akan shuwagabanni musulmi kuma masu shiryar da marasa galihu da kuma muminai. A huduba ta biyu, ya ku masallata, masu daukaka, ina kiranku zuwa ga tsoron Allah cikin dukkan al'amurranku da kuma maganganunku. Ku san cewa dukkan nauyin kula da kasa a dukkan bangarori da kuma ma bangarorin da na yi magana a kansu a huduba ta farko, (suna a wuyanku ne), dole ne dukkan muhimmancinku ku ba da shi ga wajen tabbatar da manufofin Musulunci wadanda suka yi daidai da maslahohin al'umma da kuma na kasa. Ina rokon Allah da ya ba ku nasara cikin a wannan bangare da kuma dukkan bangarori, kuma Ya baku daman wajen tsayawa da ayyukan da suka hau kanku wajen kiyaye maslahar kasa da kuma al'umma. A wannan huduba zan yi magana ne da harshen larabci ga 'yan'uwana larabawa: Yadda Hudubar Take: Amincin Allah ya tabbata akan dukkan musulmi maza da mata a duk inda suke a cikin duniyar nan musamman al'ummar kasar Iraki wadanda ake zalunta da cutarwa. Hakika irin al'amurran da suke faruwa cikin 'yan kwanakin nan a kasar Iraki lamari ne mai muhimmancin gaske kana kuma mai daure kai. Duk da cewa faduwar gwamnatin Saddam, wacce ta ke a matsayin misali na zalunci, tsanantawa da takurawa ga al'ummar kasar Iraki na tsawon shekaru masu yawa cikin kurkukun bauta da kuma azabtarwa ta zubar da jini, za ta kasance ranar farin ciki cikin tarihi, to sai dai kuma irin bala'in da ya fada akan al'ummar Irakin dalilin hare-haren sojin da Amurka da Birtaniyya suka kaddamar akan Irakin da kuma irin shirin da suke yi kan makomar al'ummar babu shakka zai bar dandanonsa mai daci a bakin al'ummar Irakin madaukaka da kuma bata ran dukkan musulmi da kuma 'yantattun al'ummomin duniya. Hakika irin kisan gillan da al'ummar Irakin suke fuskanta, da kuma yawan wadanda aka raunana da kukan yara masu jin yunwa da kuma wadanda aka raunana kuma wadanda aka barsu ba tare da magani ba, bugu da kari kan ruguza gidajen mutane, kame su a matsayin fursunonin yaki ba tare da wasu takamammun hujjoji ba, haka nan kuma da wuce gona da iri kan hurumin iyalai da kuma haifar da yanayi mai ban tsoro tsakanin al'umma, bugu da kari kuma kan cin mutumci da kuma wulakanta mazaje a gaban 'ya'ya da matayensu, da kuma lalata garuruwa ta hanyar jefa dubban bama-bamai da makamai masu linzami, wanda ko wani guda daga cikin hakan ana iya daukansa a matsayin laifin yaki…….Hakika babu wata al'umma da za ta yarda ta ga sojojin bakin haure da suke bugun kirji da nasarar da suka samu suna yawo da kuma shiga gidajensu ba tare da wata matsala da kuma tsara musu abin da za su yi. Amurka da Ingila sun yi ikirarin cewa sun kaddamar da wadannan hare-hare na su ne don kawar da Saddam da kuma kawo demokradiyya da 'yanci ga al'ummar Iraki, to sai dai da gangan sun mance cewa su ne suka ba wa Saddam azzalumi dukkan abubuwan da ya yi amfani da su, su suka sa shi aikata irin wadannan zalunci da ya yi, su ne suka bude masa hanyar aikata irin wannan kisan gilla da ya yi a shekarar 1991 ba tare da sun harare shi ba alal akalla. Su ne suka taimaka masa wajen amfani da makamai masu guba akan al'ummar Iran, kai har da ma al'ummar Halabja ba tare da sun ce masa komai ba. Su ne suka ba shi dukkan abin da yake so na daga makamai da kuma kariya wajen yakar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran na shekaru takwas duk kuwa da irin wahalhalun da Irakawa suke fuskanta dare da rana, don haka ikirarin Amurka da Birtaniyya na kawo 'yanci ga al'ummar Iraki babu shakka na daga cikin mafi girman wasa da kuma wargi.
Gaskiyar dai ita ce shiri suke na samun iko a kasar Iraki, man fetur da kuma yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kawo karshen gwagwarmayar Intifadan Palastinawa da kuma kasashen
musulmi. Haka nan kuma ayyana wani sojan bakin haure a matsayin shugaban kasar Iraki ba karamin karen tsaye ba ne ga 'yanci da kuma jagorancin al'ummar Iraki. Babu shakka ba
abin da suke son yi in banda kawar da alama ta Musulunci da kuma 'yan kasanci na al'ummar Irakin da kuma mayar da kasar ta kasance wata helkwata na ikon Amurka akan dukkan
yankin Gabas ta Tsakiya da kuma irin dimbin arzikin da yake da shi na dukiya da kuma karfin mutane.
Wadannan mutane ba sa ganin cewa al'ummar Iraki suna da karfin zaba wa kansu tafarkin da ya dace da su kana da kuma kasancewa masu mallakan abubuwan da suka mallaka a kasarsu.
A wajensu mafi daukakan mutumin Iraki shi ne wanda ya ke yin hidima mafi girma ga wadannan bakin haure masu wuce gona da iri da kuma juya wa al'umma da kasarsa baya. Lalle babu
shakka al'ummar Iraki da kuma dukkan al'ummomi ma'abuta 'yanci da kuma tarihi za su ba da shaida akan dukkan mutumin da ya ba da wata gudummawa ga Amurka wajen cimma manufofinta
na mallaka a matsayin wanda ya ha'inci kasar Iraki da kuma al'umma da tarihinta.
Lalle babu wani kokwanto cewa mafarkin da Amurka da Birtaniyya suke yi ba zai taba tabbatuwa ba, hakan kuwa saboda a ko ina suna fuskantar tsayin daka da kuma kin yarda da irin
wannan siyasa ta su, kuma hakika al'ummar Iraki, da aka sansu da shirin ko ta kwana, ba za su kasance saniyar ware ba dangane da hakan. Hakika al'ummar Palastinu, da ake zalunta,
sun kunyatar da yahudawan sahyoniya 'yan ta'adda ta hanyar tsayin dakan da suka yi duk kuwa da karfin da suke da shi. Haka nan kuma al'ummar Iran ma'abuta imani da gwagwarmaya,
ta hanyar hadin kai da kuma tsayin daka, sun sami nasara akan yakin da gwamnatin Saddam ta kallafa musu da taimakon Amurka da Birtaniyya, da kuma tsohuwar tarayyar Sobiyeti da
kuma sojojin Gabashi ta hanyar ba shi taimakon makamai, kafafen watsa labarai da kuma siyasa, to sai dai kuma al'ummar Iran din sun kori abokan gaba zuwa wajen iyaka -iyakan kasar Iran -.
Garuruwan kasar Iran sun fuskanci wahalhalu masu yawan gaske daga hannun gwamnatin Saddam na tsawon shekaru, ta hanyar makamai masu linzami da bama-bamai da ya ke jefo musu, kana
kuma matasansu masu sadaukarwa sun gamu da wahalhalu sabili da bama-bamai masu guba da ya jefa musu. To amma irin tsayin dakan da al'umma suka yi ya kawo karshen dukkan babakeren
wannan dan mulkin kama karya da kuma wuce gona da iri.
Babu shakka sojojin mamaya sun sami nasarar kawar da gwamnatin Ba'athawa (ta Iraki), kuma hakan shi ne daman abin da ake tsammanin zai sami duk wani tsari ko kuma wata gwamnati
wacce ba ta da goyon bayan al'umma - tsarin da ba abin da ya yi imani da shi in banda amfani da karfi da kama karya, to sai dai kuma wadannan 'yan mamaya ba zasu taba samun nasarar
kawar da al'ummar Iraki ba. Matukar dai suna son su guji yin fito na fito da al'ummar Iraki, to wajibi ne su kwashe sojojinsu gaba daya cikin gaggawa da kuma tsame hannunwansu
cikin makomar kasar Irakin da kuma al'ummarta.
Babu shakka shugabancin Iraki da kuma masdarorin dukiyar kasar na hannun al'ummar kasar ne kawai, kuma suna da karfin ayyana irin hukumar da suke so ta zo nan gaba don mulkar kasar.
Matukar dai Amurka da gaske suke yi kan ikirarinsu na demokradiyya, to dole ne kada su tsoma bakinsu cikin al'amurran kasar Irakin, su bar al'ummar Irakin da kansu, ta hanyar jin
ra'ayin al'umma, su zaba wa kansu gwamnati mai zuwa, su zabi jami'an da za su yi musu hidima da kuma tsara hanyar da ta dace a bi wajen sake gina abubuwan da wadannan 'yan mamaya suka lalata.
Matsayar gwamnatin Iran da al'ummarta dai a fili ya ke (kan wannan lamari), ita ce kuwa: ba mu yarda da gwamnatin Saddam ta kama karya ba, kamar yadda kuma ba mu amince da wuce gona da
irin da bakin haure 'yan mamaya suke yi wa kasar Irakin ba. Kuma dangane da yaki tsakanin Saddam a bangaren guda da kuma Amurka da Birtaniyya a daya bangaren kuwa, to mun yi amanna da cewa
dukkan bangarorin biyu azzalumai ne, ba mu taimaka wa kowanne daga cikinsu ba, kana kuma mun bayyanar da rashin yarda da dukkan bangarorin biyu (mun zama 'yan kallo ne). To sai dai kuma ba za
mu zamanto 'yan kallo ba a yayin fito na fito tsakanin ma'abuta mamaya da kuma al'ummar Iraki. Don kuwa ma'abuta mamayan 'yan ta'adda ne masu wuce gona da iri, su kuwa al'ummar Iraki masu
tsayin daka suna da hakkin yin hakan don an zalunce su ne. Hakika taimakon da muke bayarwa na siyasa da karfafawa zai ci gaba ga dukkan wata al'umma da ake zalunta, kuma wannan wani tafarki
ne da muka rike kuma ba za mu taba kaucewa daga kansa ba.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ta taimaki al'ummarmu ta Musulunci wajen bin tafarkin tsoron Allah da tsarkake zuciya don cimma manufar da ake son cimmawa, don shi mai ji da kuma karban addu'a ne.
"Kuma ka ce, 'Ku yi aiki, sa'an nan Allah zai ga aikinku, da ManzonSa da kuma muminai".(Suratut Tauba; 9:105)Ina rokon gafarar Ubangiji akai na da kuma
dukkanku gaba daya.
|