Gabatarwar Kan Ra'ayin Jagora (H) Kan Kasar Amurka
Muhammad Awwal Bauchi (Madugun Shafi)


Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai:

Hakika a halin da ake ciki hukumar (kasar) da take kiran kanta a matsayin mai kokarin tabbatar da 'yanci, wayewa da kuma kare hakkokin 'yan Adam ta mallaki dogon tajruba da kuma bakin shafi cikin tarihin mulkin mallaka kan dukiyoyi da kuma 'yan al'ummomin duniya.

Ko ba a fadi ba dai wannan hukuma (kasa) tun cikin shekarun da suka gabata ta rasa dama da kuma matsayin da take da shi na mulkin mallaka ido rufe, hakan kuwa ya faru ne saboda irin farkawar da al'ummomin duniya suka yi ne wajen tabbatar da 'yanci da kuma mutumcinsu, don haka sai ya zamanto mata dole ta canja wannan salo nata na mulkin mallaka da fito da wasu sabbin hanyoyi. Maimakon bin tafarkin yin mulkin mallaka na gaba da gaba (kai tsaye), sai ta koma ga tafarkin amfani da mahukunta da 'yan amshin shatanta a kasashe daban-daban don cimma wannan haramtaccen buri da kuma hadafi nata. Bugu da kari kan amfani da kafafen watsa labaranta wajen canja tunani da kuma al'adun mutane da shigo da nata munana duk dai da nufin cimma wadannan bakaken manufofi nata, marasa halalci. Duk kuwa da wannan canji na tafarki da suka yi, sai dai kuma manufarsu dai guda ce ita ce kuwa samun gindin zama da kuma mallake al'umma da dukkan abin da suka mallaka gaba da bugu da kari kan maishe su bayin wadannan kasashe ma'abuta girma.

To daga cikin irin al'ummomin da suka fuskanci irin wannan bakar mulkin mallaka da kuma wannan sabon tafarki da suke bi kuwa har da al'ummar Iran, inda hukumomi 'yan amshin shatan wadannan kasashen masu ra'ayin mulkin mallaka suka mulke su cikin shekaru aru-aru, dan'amshin shatansu na karshe kuwa shi Shah Pahlawi ya mulki al'umma sama da rabin karni tare da hadin bakin tsohuwar 'yar mulkin mallaka (Birtaniyya) da kuma sabuwa ta yanzu (Amurka). A lokacin mulkinsa, Amurka ta taimaka masa da dukkan abin da take iyawa don tabbatar da shi da kuma ba shi ikon rike kahon saniyyar su kuma suna tatsan nononta, bugu da kari kan aikata dukkan wasu nau'o'i na zalunci ga al'umma saboda irin karfin da Amurka ta ba shi.

Daga cikin abubuwan da suka cimma a Iran din kuwa sun hada har da samun mallaken dimbin arzikin Iran din, mai da Iran din wani sansaninta na fada da tsohuwar Tarayya Sobiyeti ko kuma mu ce akidar 'Gurguzu', yada al'adunta munana ga al'umma, musamman matasa da kuma cin mutumcin dukkan wani mai adawa da Amurkan a kasar da ma sauran kasashe.

Irin wannan makirci na Amurka ga al'ummar Iran din dai bai tsaya ga lokacin mulkin korarren sarki (Shah) ba, don kuwa hatta bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci a Iran din, Amurka ta ci gaba da makirce-makircenta wajen ganin ta kawar da wannan jaririyar gwamnati da aka kafa a kasar karkashin jagorancin Marigayi Imam Khumaini (r.a). Daga cikin irin wadannan hanyoyi kuwa har da kwace dukiyoyin Iran din da suke waje, kakabawa Iran din takunkumin tattalin arziki, kokarin haifar da juyin mulki, kallafawa wa Iran din yaki na shekaru takwas (ta hanyar kasar Iraki), ware wasu makudan kudade da nufin kawo karshen gwamnatin Musulunci ta Iran din, kokarin mai da Iran din saniyar ware, yada kararraki da farfagandoji marasa tushe akan kasar Iran, da dai sauran nau'o'i na makirce makirce masu yawa.

Makirce-makircen Amurkan dai bai tsaya nan ba kawai, don kuwa Amurkan ta ci gaba da makirci wajen ganin Iran din ba ta ci gaba ba a dukkan bangarori da kuma sake gina kasar bayan irin hasarorin da kallafaffen yaki ya jawo mata, hakan kuwa ta hanyar yin barazana ne da kuma tsorata kasashen duniya wajen ganin sun hana su taimaka wa Iran din da kuma zuba jari a kasar don kada a samu ci gaba. Hakan kuwa ta hanyar fitowa da wasu dokoki ne da za su hukumta duk wata kasa ko kuma wata kungiya da ta yi mu'amala mai tsoka da Iran ta bangaren kasuwanci, kamar dokar nan ta D'Amato(1), to sai dai kuma, Alhamdu lillahi, kusan dukkan wadannan makirce-makirce sun zama aikin baban giwa ne, don kuwa hakarsu ba ta cimma ruwa ba, face ma dai hakan ya kara wa Iran din ne tsayin daka da kuma dogaro da kai wajen ci gabantar da kasar gaba. Hakan kuwa ya biyo bayan irin jaruntaka da kuma iya jagoranci irin na Marigayi Imam Khumaini (r.a) a lokacinsa, da kuma Jagora na yanzu Imam Khamene'i (H), wanda bai yi kasa a gwuiwa wajen bin wannan tafarki na Marigayi Imam (r.a) kuma yake rike da shi sau da kafa.

Ko shakka babu, kuma hakan alkawari ne na Ubangiji, matukar dai al'ummomin suka tsaya tsayin daka, suna masu dogaro da Allah Madaukakin Sarki da kuma kiyaye dokokinsa, haka nan kuma suka hada karfinsu waje guda da kuma ci gaba da tafiya akan wannan tafarki ba tare da juyawa da baya ba, to babu wani karfi na ma'abuta girman kai da zai iya da su, face ma dai sai dai su ga bayansa, don kuwa Allah Ya yi alkawarin taimakon marasa galihu, wadanda ake zalunta akan ma'abuta zalunci da kuma kunyata su a nan duniya da kuma fuskantar mafi mumin azaba da jin kunya a gobe kiyama.

To sai dai kuma samun irin wannan ruhi na tsayin daka da kuma fuskantar makiya 'yan mulkin mallaka ya dogara ne, ko kuma mu ce samar da irin wannan yanayi yana a kan kafadun masana da malaman ko wace al'umma ce. Don kuwa su ne za su ja wannan jirgi na neman 'yanci saboda su ne masana al'amurran yau da kullum kuma su ne suka fi kowa sanin ya kamata.

To daga cikin irin wadannan mutane (masana) da Allah Ya arzurta duniyar musulmi da su, ko kuma ma mu ce duniya ba ki daya, akwai Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, ko kuma ma mu ce yana a kan sahun gaba da irin wadannan malamai, saboda irin koyarwar da ya samu daga wajen babban malaminsa kana kuma shugabansa, Imam Khumaini (Allah Ya kara masa yarda). Shakka babu duniya dai ta shaida irin tsayin dakan da wadannan bayin Allah suka yi wajen wayar da kan al'umma dangane da hatsarin da Amurka take da shi ga al'ummar duniya, ta hanyar maganganu da rubuce-rubucensu.

Mai karatu abin da ke biye jawabai ne da kalamomin Jagora (Imam Khamene'i) kan Amurka da irin sharrinta da kuma hanyoyin da za a bi wajen kaurace wa irin wadannan sharrin, wanda muka tsara kuma muka ba shi sunan "Ra'ayin Jagora Kan Amurka. Don haka kana iya matsa wannan suna dake baya, ko kuma ka koma da baya don zaba maudhu'in da kake son ganin kalaman Mai Girma Jagora din kansa.

A sha karatu lafiya.







____________
(1)- A watan Augustan 1996 ne shugaban Amurka na wancan lokacin Bill Clinton ya sanya hannu kan wata doka da majalisar dokokin Amurkan ta fitar kan takura wa kasashen Iran da Libya, wanda aka fi sani "Dokar D'Amato", wannan kuwa suna ne na wani dan majalisar daga jihar New York mai suna Alfons D'Amato wanda shi ne ya tsara wannan doka.
Wannan doka dai ta tanadi kakaba takunkumin tattalin arziki ne ga duk wani kamfanin man fetur din waje da ya sanya jari na sama da dala miliyan arba'in a cikin kasashen Iran ko Libya cikin shekara