Ci Gaban Jawabin Imam Khamene'i Ga ' Yan Majalisar Shawarar Musulunci

Amurka da Jami'anta ne Kusurwoyin Shaidan

Ina ga yana da kyau mu mai da hankali da wannan lamari; makiya dai 'yan siyasa ne masu yaki irin na siyasa, suna tunanin abubuwan da ya zama wajibi su aikata. Daya daga cikin irin hanyoyin da suke bi ita ce boye ainihin manufarsu daga farko, wato tun farkon lamari ba sa bayyana manufarsu sai daga baya takan bayyana, da sannu a hankali har su haifar da wani irin yanayi da zai tilasta wa daya bangaren mika kai. To babu shakka daga lokacin da kuka mika kai, to fa wani sabon mulkin ne zai hau kanku.

A halin yanzu wasu suna cewa, mu ba da wani abu, a maimakonsa kuma mu karbi wani abin! To sai dai kuma hakika babu wani abin da za su bayar din. Wadannan makiya dai su kan tsara wasu take don cimma manufofinsu; (misali) sun sanya Iran cikin kasashen da suka kira su "Kusurwoyin Sharri", (suna cewa) dole ne mu yi wasu abubuwa don su cire mu daga cikin "Kursurwoyin Sharri", shin wannan wani irin magana ce? A hakikanin gaskiya dai sun yi kuskure ne, yanzu kuma suna so su gyara wannan kuskure nasu. Sai dai kuma a duk lokacin da suka ga dama suna iya sake mai da mu cikin "Kusurwoyin Sharrin".

Matukar dai aka samu wani karfi ko kuma wata kasa ta sami wannan dama da kuma tsaurin ido na bayyanar da fushi da rashin amincewarta, kuma ta fito ta ce ni mai karfi ce, na kan iya kai hari, kamewa da kuma rufe gurare, don haka ku mai da hankalinku, irin wadannan kalamai dai suke bayyanarwa. To duk da hakan kuma al'amarin bai kare ba, don za su sake gabatar da wani bukatar kuma: Dole ne ku yarda da wannan hukuma wacce take haramtacciya ce, haka dai za su ci gaba da matsin lamba da kuma barazana. Har ila yau kuma bayan kun yarda da wannan hukuma, nan ma za su sake gabatar da wata bukatar kuma, ita ce kuwa: ku cire sunan Musulunci dake cikin dokokinku na kasa, ku dinga ja da baya a hankali a hankali, lamarin dai ba shi da ranar karewa.

A lokuta da dama dai na sha bayyanar da wannan lamari ga wasu daga cikin jami'an da suke fama da waswasi da kuma rashin fahimta a tare da su, ina mai ce musu: Wai shin ina ne haddin matsin lambar Amurka yake; ku tantance shi, don idan mun kai wannan iyaka mun san cewa mun kai haddin da Amurka ba za ta sake matsa mana lamba ba. Ni ina son sanin ina ne wannan haddi yake? Wannan haddi dai shi ne - duk da cewa ni da ku ba mu da wannan hakkin - da yawun al'umma Iran ku ce mu ba ma son Musulunci, Jamhuriyar Musulunci da kuma hukumar al'umma, duk wanda kuke so ya yi mulki a wannan kasa ya zo ya yi, wannan shi ne haddin da suke so; to wannan dai shi ne farkon sanya wannan al'umma cikin kangi. Shin za mu iya yin haka? Shin ni da ku za mu iya mika wannan al'umma ga hannun makiya? Shin muna da wannan hakki? Hakika al'umma ba su zabe mu don mu yi musu wannan danyen aiki ba.

Ni ina ganin ana kara gishiri cikin karfi da ikon abokan gaba. Ba wai ba ni da bayanai kan hakan ba ne; A'a, lalle ni na fi da dama daga cikinku bayanai kan abubuwan da suke da su, abubuwan da suke kerawa da dai sauransu. Don bayanai daga bangarori daban-daban suna zuwa hannuna, lalle ina sane da me ke gudana a duniya. Babu shakka makamai da na'urorin leken asiri da tara bayanai da dai sauransu ba su wadatar ba wajen tabbatar da mulkin mallakan wata kasa a kan wata al'umma ba; don haka ne za ku ga a halin yanzu suna cewa dole ne a biyo wa Iran ta cikin gida don dagula al'amurra a kasar, dole ne a raunana irin tsayin daka da iradar da al'umma suke da ita. Don kuwa matukar ba a raunana iradar al'umma - al'ummar da iradar ta take jikin jami'anta - ba, to babu wani abin da za a iya aiwatarwa a kan wannan al'umma.


Babu shakka tun tun tuni musulmai suke da kyawawan manufofi; to amma saboda rashin kokarinsu wajen ganin sun cimma wadannan manufofi ya sa har yanzu suka gagara cimma su. A halin da ake ciki, duk inda kuka duba sai ku ga musulmai suna cikin halin wulakanci da matsin lamba, to ba komai ya jawo musu haka ba in ban da zaman dirshan da suka yi. Idan kuwa ba haka ba, to da lalle sun sami nasara, don kuwa a duk inda aka samu kyakkyawar manufa, kana kuma aka rufa mata baya da kokari da tashi tsaye, to lalle fa taimakon Allah da nasararSa babu shakka za su zo.
Hakika abokan gaba suna matsa lamba, hakan kuwa cutarwa ne. Sai dai kuma hakuri da kuma jure wa irin wadannan matsin lamba lamari ne da ya zama wajibi don kare 'yanci da mutumcin al'umma da kuma kasa. Ku duba ku gani da a ce Shah Sultan Husain Safawi, maimakon ya bude kofofin birnin Isfahan ga makiya da suka iso, bayan sun shigo din kuma ya kama hannayensu da kuma dora kambun sarauta a kawukansu, sai ya yi tunanin cewa matukar dai kansa kawai ya ke tunani, kuma ba shi da rai da ya wuce guda haka din ma dai ya riga da ya ci wani abu na daga shekarunsa, to me ya sauran masa kuma na rayuwa? Idan har ina tunanin al'umma, wanda mika garin Isfahan din ga makiya ba abin da zai haifar musu in banda bala'i da wahalhalu, wanda hakan bai gaza irin wanda za su shiga ba matukar suka yi fada da makiyan, to ba zan mika su ba, don haka dai ya ki yarda ya mika garin.

Ku duba tarihin birnin Isfahan ku gani, za ku ga irin bala'in da makiya suka haifar wa al'umma bayan da suka shigo cikin garuruwan Isfahan, Kashan, Yankunan tsakiyar Iran, Fars da sauran yankunan kasar, wani irin kisan gilla ne suka yi wa al'umma bayan da suka mika kai. Makiyan ba su ce to tun da dai kun mika kai, to goronku shi ne cewa dukkanku kuna cikin aminci kuma za ku rayu ba tare da wata matsala ba. To a yau ma dai lamarin haka yake. A halin da ake ciki ku duba irin abubuwan da suke wa al'ummar Iraki. Wadannan mutane dai haka suke, a duk inda suka sami mulki haka suke yi.

Haka nan ma dai tunanin Shah Sultan Husain yake kan cewa ran mutum guda ba shi da wata kima, kuma zai iya sadaukar da shi don samar wa al'umma 'yanci, hukumci na Musulunci, yardar Allah da kuma daukakar al'umma, don haka ya fada fagen daga kana kuma ya yi yaki. Ni na yi amanna da cewa garin Isfahan ba wai ya fadi ba ne hakan kuwa saboda irin iradar da al'umma suke da ita ne, face dai abin da ya faru ya faru ne saboda ayyukan wasu ha'inan jami'ai da kuma kwamandoji, amma al'umma dai sun yi tsayin daka. Abin da ya kamata shi ne su wadannan jami'ai kamata ya yi su shiga cikin al'umma a yi gwagwarmaya da su. Lalle mas'alar tarihi, nauyi da kuma jami'an gwamnati nesa ba kusa ba sama suke da majalisa, ma'aikatar shari'a da kuma gwamnati.

A halin da ake ciki nauyin da ya hau kaina da ku na da nauyin gaske, don haka dole ne mu yi shirin share wannan hanya ta hanyar amfani da hankali, hangen nesa, bugu da kari kan dogaro da Allah da kuma jarunta ba tare da raki da tsoro ba. Aikin farko dai shi ne karfafa cikin gida, kada ku bari tattaunawa da kuma bahasi tsakaninku su zamanto rikici da kuma tada jijiyar wuya, wannan dai ita ce wasiyyata gare ku duka. Saurare, kalamai da kuma nuna rashin amincewa babu wata matala cikinsu. Lalle mutanen da suke kin jinin a nuna rashin yarda da ra'ayinsu, ko dai masu girman kai ne ko kuma mutane ne da ba su da goyon bayan al'umma; suna tsoro ne, zukatansu suna rawa da karkarwa. Matukar dai mutum ba mai girman kai ba ne - wanda mun gode wa Allah wannan bala'i bai iso gare mu ba - kuma yana da goyon bayan al'umma, to babu yadda za a yi ya bata rai daga irin wadannan maganganu da kuma nuna rashin amincewa. To sai dai kuma yana da kyau ku yi hankali kada wadannan kalamai da jiye-jiye naku su kasance abubuwan da makiya za su yi amfani da su wajen cimma manufofinsu.

A yau daya daga cikin hanyoyin da makiya suke bi shi ne fadin da suke yi na cewa akwai rikici da rashin fahimta tsakanin jami'an gwamnatin Musulunci (ta Iran). Na yi imanin da cewa abin da suke nufi ba wai irin zance daya-biyu da kuke yi ba ne, lalle bahasin ba wai wadannan 'yan kalmomi ba ne, don kuwa irin wadannan kalamomi suna nan ko ina. Suna cewa akwai rikici da kiyayya, wato suna nuna cewa wata kungiya tana son ganin bayan daya kungiyar; haka dai suke tunani. Don haka kada ku bari wannan tunani na makiya ya tabbata; don haka ku yi hankali. Babu laifi a yi bahasi da tattaunawa, Imam a lokuta da dama ya sha gaya mana haka. Hakikanin lamarin dai shi ne cewa akwai yiyuwar mutane biyu a fagen nema da tattaunawa su yi fada da tada jijiyoyin wuya, ko wannensu ya yi fushi; to amma bayan bahasi da tattaunawan su kan hadu waje guda su ci abinci, su sha shayi 'kamar babu wani abin da ya faru tsakaninsu'. Sukan tattauna da fitar da maganganu, amma babu wata kiyayya da mugun nufi tsakaninsu. Hakika duk wata tattaunawa da bahasi da ke cike da hujja, babu wata matsala a cikinta kuma ta yi daidai da doka, don haka ku kula da wannan doka.

A ganawar da muka yi da daliban jami'a kwanakin baya na gaya musu cewa an tsara doka ne don kawo karshen rikici, don kada wani ya haifar da rikici da daga murya. Sai dai kuma kada ku yi tsammanin cewa kama-karya da mulkin danniya hali ne kawai na wadanda suke kan mulki, a'a lamarin ba haka yake ba, akwai hakan ma a wajen wadanda ba jami'an gwamnati ba, sai dai kawai hakan ba abu ne mai kyau ba. Dabi'a dai ta kama karya da danniya a ko ina take kuma ta ko wani irin yanayi take, abu ne mai muni, don haka ne doka ta zo don kawo karshen hakan. A bisa doka dole ne dukkan wata magana da mutum zai fadi da kuma dukkan wani abin da zai aikata dole ne ya kasance karkashin doka; hakan kuwa shi ne babban abin da ke tabbatar da kasantuwan hadin kai tsakanin al'umma. Ku yi watsi da sauran manufofin da ba wannan ba.

Yau dai ba rana ce da in muka juya baya daga wannan nauyi na tabbatar da karfin cikin gida da kuma rikon sakainar kashi gare shi, Allah Madaukakin Sarki, al'umma da kuma tarihi ba za su taba yafe mana ba. Yau dai rana ce da bai kamata a yi rikon sakainar kashi wa wannan lamari ba, don haka ya kamata ku kasance cikin hankulanku.


wata rana ne Manzon Allah (s.a.w.a) ya gaya wa Amirul Muminina Ali (a.s) ne cewa: "Kada ka shawarci matsoraci, don kuwa shi zai kuntata maka mafita ne". Don haka kada mutum ya kuskura ya yi shawara da mutum matsoraci mai raki cikin dukkan al'amurransa, don kuwa babu makawa zai toshe masa dukkan hanyoyi da tafarkin tsira.
Lallai ba ya kamata a dinga karin gishiri kan karfin da makiya suke da shi haka nan ba ya kamata a nuna halin ko in kula ga kaidi da kuma makircin makiya ba, dole ne a sa ido kan hakan. Imam Ali (a.s) yana cewa: "Wallahi ba zan kasance kamar kurar da take barci saboda wakan da ake mata ba". Sanannen abu ne tsakanin larabawa cewa lokacin da suke son tafiya farautar kura, sukan dinga rera wakoki masu sa barci "طول اللبد" na nufin rera waka wadanda a hankali a hankali sukan sa yara barci, a lokacin iyaye mata suka rera irin wadannan wakoki a kunnuwan 'ya'yan nasu, hakan shi ne ake kira "لبد". Wadannan wakoki sukan sa kurayen barci cikin ramukansu, daga lokacin da suka yi barcin kuwa sai su kai musu hari. Mai girma Amirul Muminina yana cewa: "والله لا اكون كالضبّع"; Ni ba kamar wancan kurar ba ne da za ku sani barci ta hanyar wadannan wakoki naku ba, daga nan ku aikata duk abin da kuke son aikatawa.

Ina rokon Allah ya kasance tare da ku da kuma taimakonku, ina kuma fatan Allah Madaukakin Sarki ya yarda da mu gaba daya. Kuma cikin wannan shekara guda da ta rage, da Mai girma Sheik Karrubi ya ce ganawarmu ta karshe kenan - duk da cewa dai karshen ganawarmu kenan da Majalisa ta shida, amma da yardar Allah ba za ta kasance karshen ganawarmu da ku ba kenan - ina rokon Allah Ya kasance tare da ku, kuma da fatan za ku san kimar wannan shekara guda. A cikin wannan shekara guda kuma ana iya aikata ayyuka masu yawan gaske ga al'umma. Dole ne mu san ayyukan da suka hau kawukanmu kamar sanya idanuwa kan kasafin kudin biliyoyin kudade da gwamnati ta kan tsara, kula da ayyukan gwamnati na wuyanku ne, ku yi hankali. Ku yi kokarin zama a kwamitocin da Malam Karrubi ya yi nuni da su cikin jawabinsa, don samar da hanyoyin da za ku yi hidima da kuma magance matsalolin al'umma.

Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu.