Matanin Wasikar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Khamene'i
Ga
Ayatullah Muhammad Bakir Hakim

Shugaban Majalisar Koli ta Gwagwarmayar Musulunci ta Kasar Iraki


Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Mai Girma Ayatullah Sayyid Muhammad Bakir Hakim (H)

Hakika kasantuwanku tare da wasu 'yan kasar Iraki da kuma mujahidai wadanda ake zalunta na shekaru a kasar Iran, lalle yana nuni ne da irin damuwa da radadin da al'ummomin Iran da Iraki suka fuskanta tsawon shekaru na mulkin kama karya ta tsohuwar gwamnatin Iraki ga al'ummar Irakin.

Hakika al'ummar Iran da Iraki madaukaka, bayan samun nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, sun fuskanci zalunci da babakeren gwamnatin kama karya ta kasar Iraki, to amma suka yi hakuri kan irin wannan cutarwa da kuma ba da gudummawa da sadaukarwa mai girman gaske wacce ba za a iya kirga ta ba a kokarinsu na kare gaskiya, adalci da kuma 'yanci.

Lallai ina yin sujada don godiya ga Allah Madaukakin Sarki saboda faduwar wannan azzalumar gwamnati da kuma share fagen yin musharakan al'umma da kuma kafa 'yantaccen tsari karkashin kulawar al'umma.

To sai dai a halin yanzu, al'ummar Iraki tana fuskantar daya daga cikin mafi girman jarabawar Ubangiji, ita ce kuwa nauyin dake kan al'ummar wajen kafa tsari da kuma hukuma wacce ta ginu akan dokoki da kuma tsari na Musulunci.

Babu shakka al'ummar Iraki, a washe garin faduwar gwamnatin Saddam, sun nuna mafi alheri yanayi na nufi da kuma masaniyyar da suke da ita, kamar yadda kuma suka tabbatar da wayewarsu ta siyasa, 'yanci da kuma karfin da suke da shi na tabbatar da tsari da kuma hukuma a yayin bukukuwan Arba'in na Shugaban Shahidai (a.s) da kuma wafatin Manzon Allah (s), suna masu nuna irin girma da daukakan da wadannan bukukuwa suke da su. Sun nuna babban misali na tabbatar da tsaro a hannun al'umma, wanda za a ga hakan ta hanyar tarbar da suka yi maka wanda ba shi da na biyu da kuma sauran sanannun malamai da kuma girman maraja'ai da suke gani, wanda hakan yana nuni da irin ganin girman malamai da daukakansu da al'umma suke yi. Hakika hakan ya tabbatar da hujja akan kowa, don haka ya hau kan malamai, manyan maraja'ai, manyan gari da 'yan siyasa - ta hanyar dogaro da al'umma - su dau nauyin tabbatar da tsarin da al'umma din suke so da kuma toshe duk wata kafa ga sojojin mamaya wadanda suke mamaye da kasar Irakin, duk kuwa da nuna rashin amincewa a fili da al'umman Irakin da sauran al'ummomin duniya suke nunawa ga kokarin da 'yan mamayan suke yi na hana kafa gwamnati mai cin gashin kanta wacce al'umman take so.

Hakika al'ummar Iraki - ko daga wata kabila ko addini suke - a kowace rana kuma da baki guda sun kasance masu nuna rashin amincewarsu ta hanyoyi daban-daban da tsohuwar gwamnatin kama karya da aka kawar da kuma mulkin bakin haure na yanzu, kamar yadda kuma suke jaddada batun 'yanci da kuma jagoranci na al'ummar kasar, a fili sun sha nuna cewa ba a shirye suke su mika wuya ga mulkin mallakan bakin haure ba. To sai dai kuma 'yan mamayan sun ki sauraron wannan sauti da al'ummar Irakin madaukaka suke fitarwa, suna masu kokarin dankara wa al'ummar Irakin wata gwamnatin da suke so ta mulkin mallaka, wacce ta saba wa bukatan al'ummar.

Ina mai fatan cewa al'ummar Irakin gaba dayanta - ta hanyar kiyaye hadin kai da yarda da juna - za su shaida 'yantar da kasar Iraki gaba daya daga hannun ikon bakin haure cikin gaggawa da kuma kafa gwamnatin al'umma 'yantacciya.

Dole ne fa al'ummar Iraki su san cewa, duk da cewa an kawar da gwamnatin kama karya a kasar to amma fa akwai sauran gyauron mabiya tsohuwar gwamnatin wadanda za su so haifar da wani yanayi tsakanin al'umma don hana kafa gwamnatin al'umma mai cin gashin kanta da kuma kokarin amfani da kasantuwan 'yan mamaya a kasar don cimma wasu manufofinsu, don haka dole ne al'ummar Iraki su kasance cikin hankulansu, sannan kuma su yi guzuri - ta hanyar tawakkali da Allah Madaukakin Sarki da neman taimako a gare Shi, bugu da kari kan hakuri da tsayin daka - don fuskantar hanya ma'abuciya wahala wacce za ta kai su ga cimma burinsu. Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya kasance tare da ku da kuma tabbatar muku da nasara.

Idan Kun Taimaki Allah, hakika Zai taimake ku, kuma Ya tabbatar da dugaduganku


Wassalamu Alaiku Wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.

Sayyid Aliyu Khamene'i
3/3/1382 (Hijira Shamsiyya)