|
| |||
(Fassarar Hububar Sallar Juma'a ta Jagora Imam Khamene'i) 2002 ________________________ Shimfida: Shekaru biyu da suka wuce, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya gabatar da wani muhimmin jawabi kan ranar Ghadir a haramin Imam Aliyu bn Musa al-Ridha (a.s) da ke birnin Mashhad na Iran. Saboda muhimmancin wannan jawabi, Muhammad Awwal Bauchi daga Tehran ya fassara mana shi, don haka abin da ke biye fassarar jawabin ne. A sha karatu lafiya: Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Dukkan godiya ta tabbata ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Shugabanmu kuma Annabinmu masoyin zuciyarmu Abul Kasim al-Mustafa Muhammad tare da tsarkakan Alayensa shiryayyu masu shiryarwa musamman ma da Bakiyatullah (Imam al-Mahdi). Allah Madaukakin Sarki Yana cewa: "Daga yau wadanda suka kafirta sun debe kauna daga (karya) addininku, saboda haka ka da ku ji tsoronsu, ku ji tsoraNa. A yau na cika muku addininku, Na kuma cika ni'imata a gare ku, Na kuma zaba muku addinin Musulunci a matsayin addini (na gaskiya)". (Suratul Ma'ida; 5:3) Hakika wannan rana ce mai girma da karama. Ina gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya bani wannan dama na gudanar da Idul Ghadir mai albarka a inuwar hubbaren Imam Ali bn Musa al-Ridha (a.s) mai albarka tare da 'yan'uwana maza da mata. Don haka ina taya dukkanku madaukaka, dukkan madaukakan al'ummar Iran da kuma dukkan 'yan shi'a da sauran al'ummar musulmi murnar zagayowar wannan rana mai albarka. Duk tsawon wannan shekara da shekaru da suka gabata, madaukakan al'ummarmu sun daukaka da girmama sunan Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s), don kuwa wadannan shekaru biyu (shekara ta 1380 da 1380 hijira shamsiyya) an sanya musu sunayen "Shekarar Imam Ali" da kuma "Shekarar Koyi da Ayyukan Ali", lamarin da ya sanya zukata suka koma zuwa ga wannan babban bawan Allah da ke da kauna a zukatan masana Allah da kuma masu son gaskiya da adalci na duniya. Da farkon wannan jawabi nawa ina ga yana da kyau in dan yi takaitaccen bayani kan ma'anar Ghadir. Don kuwa bai kamata a dinga dubin wannan al'amari na Ghadir mai girman tarihi, da muke gudanar da bukukuwa don shi a yau, a matsayin wani lamari na bangaranci ba. A hakikanin gaskiya ma'anar Ghadir ba wai kawai ta ta'allaka ne ga 'yan shi'a ba, duk da cewa dai 'yan shi'a ne dai suke gudanar da bukukuwa a wannan rana saboda nada Amirul Muminina a matsayin halifan Manzo, to amma a hakikanin gaskiya ranar Ghadir, ci gaban tafarkin sakonnin Ubangiji kuma mafi hasken wannan tafarki a duk tsawon tarihi. Idan muka dubi asalin sakonnin Ubangiji, za mu ga cewa duk tsawon tarihi annabci da sakonnin Ubangiji, wannan tafarki mai haske ya yi ta hannun Annabawa daya bayan daya har zuwa lokacin Manzon karshe kuma ya tabbatar da shi a aikace a karshen rayuwarsa a lokacin Ghadir. A daidai wannan lokaci ya zama dole in yi ishara da muhimmancin Du'a al-Nudbah, wanda a hakikanin gaskiya magana ce da ke bayyanar da fata da abubuwan da 'yan Shi'a Imamiyya suka yarda da shi duk tsawon tarihinsu. Idan muka duba wannan addu'a, za mu ga bayani kan wannan tafarki mai haske a farko-farkon wannan addu'a, wato: (الحمد علي ما جري به قضائك في اوليائك), (Godiya ta tabbata gare Ka kan abin da kaddararka ta hukumta a kan waliyanka - bayinka). Tun daga farkon tarihin sakon Ubangiji har zuwa lokacin annabcin Manzon karshe (s.a.w.a), wannan tafarki mai haske dai yana ci gaba. Abin da wannan sako, wanda shi ne addinin Allah, ya kunsa a hakikanin gaskiya shi ne haifar da shakali da kuma jiha ga dukkan kokarin dan'Adam. Addini dai yana nufin tafarkin rayuwa. Idan da za ku dubi al'ummar dan'Adam ko kuma wata kasa, za ku ga cewa wadannan al'ummomi suna ba da kokari da kuma dukkan karfinsu ne wajen cimma lamurran da suka shafi son kansu da rayuwarsu ta yau da kullum. To a nan addini dai ya kan tsara wa wadannan kokari na dan'Adam hanya da tafarkin da ya dace ne; ya kan shiryar da su ne , ya kan taimaka wa dan'Adam wajen tsara wadannan kokari da kuma tsai da su da kafafunsu don tabbatar masa da sa'adar duniya da ta lahira. Wasu daga cikin kokarin da mutane suke yi sun shafi batutuwan da suka shafi daidaiku ne duk kuwa da cewa wadannan abubuwa wani sashe ne kawai na rayuwar mutum - misali neman abin rayuwa, kyautata ruhi, alakarsu da junansu - to sai dai kuma mafi girman ayyukan dan'Adam, ayyuka ne da ake gudanar da su a al'ummance, wannan lamari kuwa shi ne ake kira da 'siyasa', siyasar tattalin arziki, siyasar zamantakewa, siyasar soji, siyasar al'adu, siyasar kasa, siyasar kasa da kasa; duk wadannan dai kokari ne na dan'Adam a rayuwarsa ta yau da kullum. Abin tambaya a nan shi ne me ya sa wannan lamari ya zamanto na asasi? saboda dukkan wadannan siyasu suna juya dan'Adam zuwa ga wata jiha ko kuma bangare na musamman ne. Hakika jigon kokarin dan'Adam, kokari ne na gaba daya da ke ba wa dukkan kokarin mutum babba da karami manufa da tafarki na musamman. Don haka shi addini yana da alaka da dukkan bangarorin biyu, wato bangaren kokarin mutum guda da kuma bangaren siyasa wanda fage ne mai girman gaske na rayuwar dan'Adam. Akwai wasu abubuwa guda biyu da suke barazana ga riko da addini kamar yadda kuma suke barazana ga siyasa. Daya daga cikinsu (dake barazana ga) riko da addini, shi ne riko da addinin wata kaucacciyar al'umma ko wani kaucaccen mutum mai nuna halin ko in kula, wanda aka bar shi a baya, wanda ya yi watsi da gudummawar hankali da dai sauran irin wadannan abubuwa da suke ciyar da dan'Adam baya. Wani bala'in kuma da ke barazana ga riko da addini shi ne a takaita addini da rayuwar daidaikun mutane, a mance da shi a rayuwar al'ummance ta al'umma. Akwai wasu abubuwa guda biyu kuma da suke barazana ga siyasa. Na farko dai shi ne cire batun kyawawun dabi'u daga siyasa, ya zamanto ta yi nisa da abubuwan daukaka ruhi da falala; wato shaidanci ya yi galaba a kan siyasa, son zuciyan mutum ya mamaye al'amurran siyasa; wasu 'yan a fasa kowa ya rasa na al'umma su rike al'amurran siyasa, su aikata dukkan abin da suke so. Matukar dai wannan bala'i ya fada wa harkokin siyasa, to a nan fa dukkan bangarori na al'umma za su fuskanci matsaloli. Wani bala'in kuma na siyasa shi ne a samu wasu mutane marasa hangen nesa, masu tunani irin na yara su rike al'amurran siyasa, su kwace ragamar mulki da siyasa daga hanmnun ma'abuta karfi da hangen nesa, ya fada hannun wadansu marasa kwarewa. To abin tambaya a nan shi ne mene ne abin yi? Mafi kyaun tafarki da hanyar aiki dai shi ne a samu mutanen da a bangaren addini da siyasa ba su da wadannan bala'oi su rike akalar gudanarwa ta al'umma; wato mutanen da za su rike ragamar mulki su kasance ma'abuta addini da kyawawan dabi'u; tunanin addininsu ya kasance a sama; su zamanto ba su da kaucaccen tunani dangane da ddini, su kasance ba mutane ne da aka barsu a baya masu ra'ayin 'yan mazan jiya da babu ci gaba wajen fahimtarsu ta addini ba; wadanda ba su mai da addinin fagen wasunsu ba. A mahangar siyasa dai, dole ne mutanen da suka dace kana ma'abuta tunani mai kyau kuma jarumai, wadanda ba su yi nisa da kyawawan dabi'u ba, su ne za su kasance a sahun gaba. Hakika idan irin wadannan mutane suka dare karagar mulkin al'umma, to a nan ne fa rayuwar al'umma za ta ci gaba kuma ta yi kyau. Sai dai abin tambaya a nan shi ne yaushe ne ake samun kolin irin wannan yanayi? (To amsar dai ita ce) a lokacin da aka samu wani mutumin da ya kubuta daga sabo da kuskure ya dare karagar gudanar da al'amurran al'umma; wannan kuwa shi ne Imam. Imami ma'asumi dai, mutum ne madaukaki, wanda a bangaren addini, zuciyarsa wani madubi ne da ya ginu a kan hasken shiriya ta Ubangiji; ruhinsa na tare ne da mabubbugan wahayi, shiriyarsa, tsarkakkiyar shiriya ce, a bangaren dabi'un dan'Adam kuma dari bisa dari sun yi daidai da daukaka, babu son zuciya cikinsu, sabo ba shi da mazauni a tattare da shi, sha'awace-sha'awacen dan'Adam ba su mai shi shi bawa ba, fushi da rashin jin dadi ba sa kawar da shi daga tafarkin Ubangiji; a bangaren siyasa, yana da mahanga mai fadi gaske ta yadda ya kan iya ganin mafi karancin motsi da harkar da take faruwa a fagen rayuwar al'umma, kamar yadda Amirul Muminina (a.s) yake cewa: (والله لا آكون كالضبع تنام علي طول اللدم ) ("Wallahi ba zan kasance kamar kurar da bugun dutse yake sa ta barci ba) wato ni ba irin mutanen ne da rarrashi yake sanya su barci ba - wajen fuskantar rayuwa da abubuwan da suke faruwa, su kan nuna jaruntaka da tsayin daka; ransa ba shi da wata kima, amma wajen 'yantar da rayukan sauran al'umma hatta wadanda ba na kusa da shi ba, hatta matayen da ba su hada addini guda ba, ya kan ba da muhimmanci da kuma ba da rayuwarsa. Amirul Muminina (a.s) ya kan fuskanci matsaloli da dukkan jaruntaka har ma yake cewa babu wani da zai iya kasha wutar fitinar da na riga da na kashe ta - a nan yana nufin fitinar Khawarijawa. A bangare guda ga addini, ma'anawiyya, kyawawan dabi'u da kuma daukaka, a bangare guda kuma ga zurfafafiyar mahanga, jarunta, sadaukarwa da tausayin dan'Adam, to dukkan wadannan abubuwa dai sun samo asali ne daga Ismah (tsarkaka daga zunubi); don kuwa Allah Madaukakin Sarki ya kai shi matsayi na ismah, kuma babu kuskure da sabo cikin aikinsa. Matukar dai aka sami irin wannan a sahun gaba gaban jagorancin al'umma, to za a samu cimma abin da ake son cimmawa. To wannan dai shi ne ma'anar Ghadir, irin wannan abu ne ya faru a Ghadir. (Yana da kyau a fahimci cewa) Ghadir ba wai kawai lamari ne na ayyana wani mutum (a matsayin halifa) da Manzo (s.a.w.a) ya yi ba ne, lalle gaskiya ne cewa a wannan rana Manzon Allah (s.a.w.a) ya nada Amirul muminina (a.s) a matsayin halifansa a gaba ga dubban musulmi, wannan lamari ne da babu kokwanto cikinsa, don ba wai abu ne da shi'a kawai suka nakalto ba, a a 'yan'uwanmu Ahlusunna ma cikin littattafansu sun nakalto wannan abu da shi'a suka nakalto. Wannan lamari ne da babu wanda zai iya inkarinsa, sai dai kawai lamarin ba wai ya tsaya ga haka ba ne kawai.
Lamarin dai shi ne cewa tun daga lokacin Annabi Adamu wanda daga lokacinsa ne tushen annabcin da manzancin ya fara kuma a lokuta daban-daban aka samu hukumomi na Annabawa cikin tarihi (irinsu Sulaiman da Dawud da sai sauran mutane daga Bani Isra'ila har zuwa lokacin Annabinmu), to sai dai ana iya cewa wannan siyasa da kuma addini sun sami cikakken lamuni da garkuwa wajen shiryar da al'umma ne lokacin waki'ar Ghadir don haka ne cikin Du'a al-Nudhbah da na ambata a baya, muke
karanta cewa: 11(Sanannen abu ne cewa) Annabi dai ba mai dawwama (dawwamamme) ba ne, kuma al'umma dai suna bukatuwa da wani mai shiryarwa, Musulunci kuwa ya yi bayanin wannan mai shiryarwa; (a wannan tsari) Ma'asumai daya bayan daya za su zo a lokuta daban-daban su rike harkokin gudanarwa na al'umma, su koyar da su koyarwa ta Alkur'ani mai tsarki, a takaice dai su gudanar da dukkan koyarwa da dabi'u na Musulunci. To sai dai fa duk da haka, dole ne a samu wani 'hujja' na Ubangiji cikin mutane a koda yaushe don kuwa duniya ba za ta taba rayuwa ba tare da kasantuwan wannan 'Hujja' ba, duk da cewa dai shi dan'Adam shi ne zai gudanar da rayuwarsa. Wannan dai shi ne koyarwa ta gaba daya ta Musulunci; kuma wannan dai shi ne ma'anar Ghadir. Imamanci dai shi ne irin wannan tsari da ake bukata na jagorantar al'umma sabanin sauran tsari na jagorantar al'umma da ke cike da rauni, sha'auce-sha'auce da son ran dan'Adam. Hakika Musulunci ya fitar wa dan'Adam tsarin shugabanci (imamanci) shi ne kuwa samun wani mutum da zuciyarsa take cike da hasken shiriya, wanda ya san koyarwa ta Musulunci da kuma fahimtarta - wato ya iya fayyace tafarkin - kamar yadda kuma zai kasance mai karfin aiki, (wato kamar fadin Allah Madaukakin Sarki cewa) (يا يحي خذ الكتاب بقوة) kamar yadda kuma son zuciya da son kan kansa ba za su kasance masu muhimmanci ba a gare shi, to amma a daidai lokaci guda kuma rai da rayuwar sauran al'umma sun kasance abin girmamawa da ba da muhimmanci a gare shi, kamar yadda Amirul Muminina cikin shekaru biyar na halifancinsa ya nuna hakan a fili. Ku duba ku gani cikin kasa da shekaru biyar na mulkin Amirul Muminina an haifar wa dan'Adam da abin da ba zai taba mancewa da shi ba, kuma ya ci gaba da wanzuwa duk tsawon tarihi. Wannan dai sakamakon darasi da fassarar waki'ar Ghadir. Mu (dai a wannan kasa) shekaru biyu kenan muka mayar da hankali da zukatan al'umma zuwa ga sunan Amirul Muminina (a.s) wannan madaukakin halitta mai madaukakin matsayi da ba za a taba mancewa da shi cikin tarihi ba, duk da cewa hakan ba wai yana nufin ne idan wannan shekara ta kare shi kenan ba za mu ba da muhimmanci ga rayuwar Amirul Muminina (a.s) ba kenan; a a ko da wasa, face dai mu a kowani lokaci muna bukatuwa da wannan mai koyi. Ku duba (rayuwarsa) ku gani, don mu dau abubuwan koyi, sannan kuma mu yi kokarin rage banbamcin da ke tsakanin ayyukanmu da ayyukansu gwargwardon iyawanmu. Babban hatsarin da zai iya fuskantar tsari irin namu wanda aka samo shi da sunan Musulunci shi ne mu mance da babban abin koyinmu, wanda shi ne Amirul Muminina (a.s). Mu dubi sanannun abin koyin na duniya da tarihi mu gani sannan kuma mu kwatanta kanmu da su; mu dubi yanayin da karkatattun hukumomin da suke zaluntar al'ummomi tsawon tarihi, mu gani; za mu ga cewa idan har suka haskaka wani janibi na rayuwar dan'Adam, to za su cutar da wasu janibobi kuma cutarwa da da wuya a iya magance ta. Don haka dole ne Jamhuriyar Musulunci ta dada kusantowa ga wannan abin koyi da aka bayyanar da shi a (ranar) Ghadir wato Amirul Muminina (a.s). Idan muka duba, za mu ga cewa yakin da Amirul Muminina (a.s) ya yi cikin wannan dan karamin lokacin (na mulkinsa) ya yi ne don hana karkatar da halifancin Musulunci zuwa ga karkataccen yanayi; mayar da halifanci zuwa sarauta; mayar da hukumar ilmi zuwa ga ta jahiliyya; mayar da hukumar da take rufe ido kan manufofi na mutum kansa da hukumar da masu gudanar da ita mutane ne da suka ba da himma wajen tabbatar da manufofinsu da kuma tara kudade don amfanin kansu. A halin da ake ciki, matukar dai muna son mu tabbatar da sa'adar wannan kasa tamu da kuma kare albarkatun da Allah Madaukakin Sarki Ya ba wa al'ummarmu, to dole ne mu yi riko da wannan tafarki, mu dauki wannan hukuma (ta Amirul Muminina) a matsayin abin koyi; wannan hukuma da ta tsira daga dukkan dauda, son zuciya da sha'auce-sha'auce; hukumar da ta ginu a kan addini da kyawawan dabi'u, hukumar da ta ba wa manufofin al'umma gaba daya kolin muhimmanci; hukumar da a cikinta ake lamunce wa mutane bukatunsu na yau da kullum cikin girmamawa da mutumci. A yau din nan dai muna bukatuwa da irin wannan yanayi (hukuma), za mu iya samun hakan ne kuwa lokacin da muka samu jami'ai da suka damu da bukatu da akida ta al'umma; hakan zai kasance abin koyi cikakke. Idan har mu a nan Jamhuriyar Musulunci muka bi wannan tafarki - wanda cikin yardar Allah lamari ne da za a iya aikata shi kuma jami'anmu cikin shekaru 23 sun kai ga wasu daga cikinsu - to a wannan lokaci ne Allah zai yarda (da mu); sannan kuma mutane za su samu karin amincewa da hukumar. To sai dai kuma, cikin shekaru biyun da suka gabata, musamman ma a wannan shekara da muke ciki - da aka kira da shekarar (aikata) ayyukan Ali - saboda albarkan sunan Amirul Muminina (a.s) a wannan kasa an gudanar da ayyuka daban-daban don samun kusanci da wannan abin koyi, daya daga cikin wadannan ayyuka kuwa shi ne yaki da rashawa da cin dukiyar al'umma da aka kaddamar. Bangarori daban-daban na duniya sun nuna matsayarsu dangane da wannan matsaya ta Jamhuriyar Musulunci kuma hakan ya tabbatar mana da cewa lalle wannan matsaya da muka dauka tafarki ne na gaskiya. Fada da rashawa da wasa da dukiyar al'umma dai na daga cikin mataki da tsare-tsaren farko-farko na (hukumar) Amirul Muminina (a.s), don haka mu ma a nan Jamhuriyar Musulunci dole ne mu yi koyi da wannan tsari da kuma binsa. Wasu sukan ce maganar da ake yi na fada da rashawa da wasa da dukiyar al'umma na nufin ne za a tuhumci dukkan jami'ai masu hidima wa al'umma; koda wasa, wannan ai kuskure ne. Babban abin da ke tabbatar da zaman lafiya gwamnati, shi ne lokacin da aka fara fada da lalacewa da fasadi, kuma manyan jami'ai suka shigo fage don ba da gudummawarsu. Ma'anar hakan dai shi ne cewa gwamnati, dalilin tausasawa ta Ubangiji da kuma albarkan Amirul Muminina (a.s), za ta iya magance matsalolin da ake fuskanta. A cikin kowani rafi mai tsarki da kyau za a iya samun wata dauda ta shige shi (da nufin bata shi), abin da muke so shi ne ganin bayan hakan. Manyan jami'an gwamnati, kamar sauran al'umma, suna farin ciki da wannan fada da ake yi da fasadi da lalacewa. Abokan gaban wannan al'umma tamu da wasu mutane suna son mu janye daga wannan gwagwarmaya, don fasadi ya samu matsuguni a wannan kasa; ina, ko da wasa; mu dai a Jamhuriyar Musulunci muna fada ne da wani abin da a halin yanzu ake ganinsa a da dama daga cikin gwamnatoci da hukumomi na duniya. Fada da fasadi dai daya ne daga cikin halayen Amirul Muminina (a.s), kuma da ikon Allah Madaukakin Sarki jami'ai su ne a kan gaba wajen wannan gwagwarmaya, don haka ya zama dole mu yi aiki da wannan tafarki na Amirul Muminina (a.s) kuma lalle za mu yi aiki da shi. Har ila yau kuma kokari wajen kyautata rayuwar marasa galihu na daga cikin matakan farko na tsarin Amirul Muminina (a.s), kuma a wannan shekara, an gudanar da irin wadannan kokari. A hakikanin gaskiya jami'ai sun aikata ayyuka da yawa a wannan bangare, sai dai kawai ba sa fadi ne, wanda hakan ma abu ne mai kyau. Mu mun yi amanna da cewa ba dole ba ne sai an ta fada, duk da cewa dai dole ne mutane su san irin kokarin da ake yi. Dole ne a gaya wa mutane abubuwan da suke faruwa, duk da cewa dai abin bakin ciki isar da sakonmu a wannan bangare ya yi kadan. Kokarin da jami'ai a bangarori daban-daban suka yi wajen samar da aikin yi wa al'umma, daya ne daga cikin irin wadannan ayyuka da ake yi don koyi da halayen Ali (a.s). Sai dai kuma wadannan abubuwa ba su isa ba; ni dai a lokuta daban-daban na sha jaddada wa jami'ai a bangarori daban-daban na gudanarwa da gwamnati cewa dole ne fa ayyuka su ci gaba don a cimma manufa kana kuma a ga tasirinsu a rayuwar al'umma, to sai dai fa fara aiki shi kansa wata albarka ce, duk da cewa irin wannan aiki na daga cikin shirye-shiryen gwamnati, amma kyautata ayyukan na daga cikin albarkan wannan shekara ta ayyukan Ali, ina fatan, cikin ikon Allah, za a cimma manufa. Amma fa yana da kyau a fahimci cewa bi da kuma riko da wannan tafarki na tare da makiya da 'yan zagon kasa. Babban makiyin wannan tafarki shi ne makiyin da yake cikinmu; wannan makiyi kuwa shi ne: dabi'ar nan ta cin na bulus, gafala, kasala da kuma kokarin gudu daga fagen daga a lokutan wahala. Babu shakka wannan tafarki yana bukatuwa da kokari da juriya. Karkatattun sha'auce-sha'auce na dan'Adam - sha'awar dukiya, sha'awar rayuwa a waje na musamman, sha'auce-sha'auce daban-daban - suna daga cikin abubuwan da suke kafar ungulu wa wannan tafarki, musamman ma daga mu jami'ai da sauran 'yan'uwa maza da mata da suke bangarori daban-daban na kasa. Dole ne mu dogara ga Allah Madaukakin Sarki, mu kasance cikin hayacinmu da kuma tunasar da juna. Wannan dai shi ne makiyi na cikin gida, wanda ya fi na waje hatsari. Haka nan kuma wannan tafarki yana da makiyi na waje. Makiya na waje dai su ne irin mutanen nan da suke kallo daga gefe, suna ganin Jamhuriyar Musulunci ta Iran fa a halin yanzu tana ci gaba da zama abin koyi a kasashen musulmi, su kuwa ba sa son hakan. Saboda sun san cewa matukar dai Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu daman magance matsalolin da al'umma suke ciki, to fa musulmin duniya za su juya gare ta, don haka suke daukan matakan yin kafar ungulu wa hakan. A halin da ake ciki, shekara da shekaru kenan makiya suke ta kokarin yin kafar ungulu wa ci gaban da ake samu a bangarorin tattalin arziki na kasa da dai sauransu. To sai dai kuma irin wadannan abubuwa ko da wasa ba su isa su hana al'umma ko hukumar da ta kuduri aniya kana mai azama ba wajen ci gaba da ayyukanta. A halin da ake ciki dai da yake sun riga da sun jarraba hanyoyi daban-daban wajen hana Jamhuriyar Musulunci ci gaba amma ba su ci nasara ba, sai kuma suka koma ga barazana ta kai harin soji. To sai dai irin wannan barazana ta soji cikin shekara da shekarun na samun nasarar Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya zuwa yanzu ta gagara tabbatar musu abin da suke so. Ina so in sanar da ku cewa barazana ta soji ko da wasa ba za ta tabbatar musu da abin da suke so din ba. Da yardar Allah a nan gaba kadan zan yi cikakken bayani kan jawabin shugaban Amurka da sauran masana da suke tare da wannan hukuma ta ma'abuta girman kai, kuma da yardar Allah, matukar dai ina raye, za ku ji ra'ayimu kan wannan batu, a halin yanzu dai ba na son shiga wannan fage, to sai dai idan kuna son bayani a takaice kan wannan lamari, to ga abin da zance: A halin yanzu jami'ai da 'yan bokon Amurka a aikace da kuma da bakinsu, sabanin dukkanin ikirarin zaman lafiyan da suke yi, suna nan suna kaddamar da yaki a matsayin wani abu mai tsarki. Shekara da shekaru dai suka yi suna ta yada maganan cewa su suna girmama akidu da ra'ayin 'yan'Adam; a koda yaushe suna ikirarin cewa suna goyon bayan sulhu da zaman lafiya ne; suna cewa dalilin shiganmu wannan kasa da wancan kasa shi ne don tabbatar da sulhu da zaman lafiya; matakin da muka dauka a waje kaza, mun dauka ne don tabbatar da sulhu. A halin da ake ciki yanayi (da suka shiga ciki) ya tilasta musu tsarkake yaki da bayyanar da shi a matsayin tsarkakakken abu. Wannan dai kuskurensu ne mai girma da ba za a mance shi ba, inda suke lashe aman da suka yi a baya, ba su fahimci irin bala'in da son zuciya ya haifar musu ba; haka suka ta aikata kuskure daya bayan daya kuma yanzu ma suna aikatawa. A duniya dai fuskokin ma'abuta tsokana da son yaki sun fito fili kuma sun kasance abubuwan kyama a wajen al'ummomin duniya; hakika ba su da wata mafita. A wani bangaren kuma (wadannan mutane) suna da'awar cewar su masu goyon bayan demokradiyya da hukumomin da al'umma suka zaba ne, to sai dai kuma a daidai wannan lokaci sai ga shi suna goyon bayan hukumomin kama-karya wadanda suka dare mulki ta hanyar juyin mulki, ko kuma hukumomin da wajen tabbatar da su babu wani mutum ko da guda ne da yake da hannu cikinsu. Kafin dai su fahimci abin da suke son aikatawa, sun yi kuskure daya bayan daya, kuma ma suna ci gaba da aikata sabbin kura-kuran, a hakikanin gaskiya wannan matakin farko ne na faduwa (kasa warwas). Cikin wauta ba tare da la'akari da abin da suke fadi ba, suna ce wa wata al'umma (kasa) mai girma da jaruntaka, kasar da cikin shekaru ta tabbatar wa duniya iyawanta a bangarori daban-daban, cewa dole ne ku mika wuya ku kasance raunana don mu daina kiyayya da ku da kuma muku barazana. To lalle dai ya kamata a fahimci cewa wadannan mutane dai ba za su ji dadi ba matukar suka ga al'ummar Iran su hada kai waje guda. Abin da zai faranta musu rai dai shi ne sukan su al'ummar Iran su sami sabani tsakaninsu, su watsar da hadin kan dake tsakaninsu, wannan kungiya ta zargi wancan, wancan ta zargi wannan. Abu na biyu kuma (da zai faranta musu rai) shi ne kasarmu ta mika wa Amurka kai, kamar yadda wasu kasashen wannan yanki suka yi, al'ummomin wadannan kasashe suka kasance cikin mummunan yanayi saboda mika kan da shuwagabanninsu suka yi wa Amurka. Abu na uku kuma shi ne kasar Iran, a bangaren siyasa da soji ta kasance raunanniya, ta rasa karfin kare kanta da iyakokinta. Matukar aka samu haka, to nan ne shugaban Amurka zai yarda da al'ummar Iran. Amsarmu dai ga hakan ita ce, al'ummar Iran, da albarkan Musulunci, ba za ta taba yin watsi da daukaka, 'yanci da hadin kan da ta samo da kuma tafarkin da ta zaba wa kanta ba, kamar yadda kuma za ta ci gaba da bin wannan tafarki ta hanyar dogaro da hadin kai, karfin al'umma, riko da Musulunci da dogaro da Allah, za mu tsaya kyam wajen fuskantar duk wata barazana, kuma mun yi imanin cewa rashin nasara da shan kashi shi ne sakamakon duk wani wanda yake son fuskantar wannan tafarki. Ya Allah, don darajar Muhammadu da Iyalan Muhammadu Ka rufe mu da inuwar Imam Husaini, Ahlulbaiti da Ghadir. Ya Allah, Ka ba da nasara ga kasar Iran a dukkan bangarori, sannan kuma Ka gutsure hannuwan makiya da suke cikinmu. Ya Allah, Ka kaskantar da masu adawa da wannan jamhuriya ta Musulunci, Ka hada zukatan al'umma, jami'ai da 'yan siyasarmu. Ya Allah, Ka sanya mu cikin addu'oin Waliyullah al-A'azam, Imam Mahdi (ATFS), Ka sanya mu daga cikin mabiyansa na hakika. Ya Allah, ka sanya wannan rana ta Ghadir ta kasance abin ceto da faranta ran al'umma. Ya Allah, ka sanya wannan rana ta Ghadir ta kasance abin ceto da faranta ran al'umma.
Wassalamu Alaikum Wa Rahmatullah Wa Barakatuhu.
|
||||