Ayyukan Mai Girma Imam Khamene'i (H) Na Yau Da
Kullum (Watan Satumban 2003)
-24 ga
Satumban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci A Bukin Ranar Aiko Manzon Tsira Muhammad (s)
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (h) ya bayyana cewa: "Madaukaka al'ummar
Iran, ta hanyar dogaro da darussan da ke cikin aiko Manzon Allah (s) za su ci gaba da tafarkinsu na daukaka da sa'ada da dukkan karfinsu.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Laraba (24 ga Satumba 2003) yayin da yake isar da sakon taya murnarsa ga al'ummar Iran da sauran al'ummar
musulmi na duniya a ganawar da ya yi da shugabannin bangarorin gwamnati guda uku, shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin Musulunci ta Iran, sauran jami'an gwamnati
da na soji, al'ummomi daban-daban na Iran, jakadoji da kuma wakilan kasashen daban-daban na Musulunci, inda yayin da yake bayyana cewa al'ummomin duniya, a halin
yanzu sama da kullum suna bukatuwa da sakonnin da ke cikin aiko Ma'aiki (s) ya kara da cewa: "Aiko Manzon Allah lamari ne da ke kiran dan'Adam zuwa ga tauhidi da hadin
kai a matsayin wata hakika ta rayuwa bugu da kari kan gutsure hannuwan azzaluman da suke zaluntar dan'Adam, don samun sa'ada ta duniya da ta lahira, duk da cewa cimma wannan
manufa tana bukatuwa da kokari da tsayin daka".
Haka nan kuma Jagoran ya bayyana tsarkake zuciya, tarbiyyar ruhi, girmama matsayin ilmi, tsayuwa domin Allah da kuma hadin kai da 'yan'uwantaka a matsayin kadan
daga cikin sakonnin aiko da Manzon Allah (s).
Yayin da kuma ya koma kan Jami'an gwamnati da kuma bayyana nauyin da ke kansu a matsayin nauyi mai girman gaske, Imam Khamene'i ya ce: "Kamar Manzon Allah (s) ya fadi, gyaran
kowace al'umma yana da alaka da gyaruwar zababbun wannan al'umma ne, don haka ya hau kan malamai da masana su sauke nauyin da ya hau kansu wajen tabbatar da tsayuwar al'umman musulmi a gaban
abokan gaba".
Haka nan kuma Jagoran ya bayyana gazawar da H.K. Isra'ila ta yi wajen fuskantar tsayin dakan al'ummar Palastinu a matsayin babbar alama ta tasirin tsayuwar wata al'umma a gaban
abokan gaba, inda ya ce: "A ko ina aka samu al'umman musulmi sun mike tsaye wajen fuskantar abokan gaba, to babu shakka za a ga irin wannan tasiri a fili".
Har ila yau kuma Jagoran ya ja kunnen al'ummar musulmi dangane da irin makirce-makircen makiya musamman kasar Amurka dangane da kokarin da take yi rarraba kan al'ummar musulmi
da nufin mamaye su, inda ya ce: "A yau manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai a kokarin da suke yi na fada da al'ummar musulmi, sun zaro dukkan fararunsu na zalunci akan Iran, ba don komai ba sai dai
saboda irin tsayin dakan al'umman Iran da kuma farkawarsu sun kasance babban kafar ungulu ga cimma manufofinsu".
Kafin jawabin Jagoran sai dai Shugaban kasa Sayyid Muhammad Khatami ya gabatar da jawabi inda yayin da yake isar da sakon taya murnarsa na wannan rana ta aiko Manzon Allah
ga Jagoran da kuma al'ummar musulmi ya bayyana hadin kai da 'yantuwa daga zalunci, jahilci son kai da kuma nuna banbanci a matsayin abubuwan da aiko Manzo din ya zo da su.
|
-20 ga
Satumban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci A Bukin Yaye Daliban Jami'ar Soji A Garin Nushahr
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci kuma kwamandan dukkan dakarun tsaro na Iran Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana cewa: "Gaba da Musulunci
da kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba abin da zai haifar wa abokan gaba in ban da kunya da rashin nasara".
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan asabar (10/9/2003) a wajen bukin yaye daliban jami’ar dakarun sojin sama, kasa da na ruwa a garin Nushahr da ke arewacin Iran,
inda yayin da yake magana kan asalin dalilin da ya sa makiya suke gaba da tsarin Musulunci na Iran, ya bayyana cewa: “Dakarun tsaron Iran, babu shakka ba za su kasa a gwuiwa ba wajen sauke
nauyin da ya hau kansu na kare Musulunci da Jamhuriyar Musulunci".
Haka nan kuma yayin da yake magana kan kokarin abokan gaba wajen sanya jin kaskanci cikin zukatan al’ummar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya ce: "Mallakan ilmi
mai zurfi a bangaren kere-kere da matasa masanan Iran suka yi yana nuni da cewa al’ummar Iran suna da dama mai girman gaske na ilmi da kuma kere-kere na ci gaba wanda hakan na daga cikin
abubuwan da suke damun makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Har ila yau Jagoran a ganawar da yayi da kwamandojin bangarori uku na dakarun Iran din, wato dakarun sama, kasa da na ruwa, ya nuna jin dadi da amincewarsa da irin ci gaban
da dakarun suka samu musamman dakarun ruwa a bangarorin kere-keren makaman kariya da dai sauran kayayyakin da suka shafi ayyukansu, inda ya ce: “Bisa la’akari da wannan ci gaba da aka samu,
ya zama dole dakarun su ci gaba da ba da kokari a wannan bangare har a kai ga manufa".
Haka nan kuma Jagoran ya bayyana dogaro da Allah da kuma jaruntaka a matsayin abubuwan alfaharin al’umma a gaban makiya inda ya ce: “Dakarun tsaron kasa da suka hada da sojoji,
dakarun kare Juyin Juya Halin Musulunci, dakarun sa kai, ta hanyar imani da jaruntaka za su ci gaba da ba da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da ‘yanci kasar Iran.
Shi ma a nasa jawabin babban hafsan hafsoshin sojojin Iran din General Sulaimi ya ce dakarun Iran din karkashin jagoranci mai cike da hikima na Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
a shirye-shirye hannu daya wajen kare Musulunci da kuma tsarin Musulunci.
A yayin wannan buki dai Jagoran baya ga halartar wani fareti na soji ya kuma halarci makabartar shahidan da ke wannan jami’a inda ya karanta musu fatiha.
|
-10 ga
Satumban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da 'Yan Majalisar Kwararru Masu
Kula da Kuma Zaban Jagora
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa koyi da kuma biyayya ga Amirul Muminina Ali (a.s)
ya kasance abin alfaharin al'umma da kuma jami'an gwamnatin Musulunci ta Iran
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba (10/9/2003) a lokacin da yake maraba da 'yan majalisar kwararru masu zabe da kuma kula da ayyukan
Jagora a nan Iran yayin da suka kai masa a yau ranar haihuwar Imam Ali (13 ga watan Rajab).
Yayin da yake kiran al'umma da jami'an gwamnati da su ba da himma wajen kyautata ayyukansu da kuma koyi da Imam Ali (a.s) da sauran Imamai (a.s), Imam
Khamene'i (h) cewa yayi: "Akwai banbanci mai girman gaske tsakanin ayyuka da dabi'unmu da kuma darussa da koyarwar da Amirul Muminina (a.s) ya koya mana, don haka ya zama dole,
ta hanyar neman taimakon Allah da kuma kokari, mu zama masu kusanci da Imamai da kuma riko da tafarkinsu".
Yayin da kuma yake magana kan hanyoyin da za a bi wajen magance matsalolin da ake ciki, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya bayyana kokari a bangarorin kiyaye 'yanci
da daukakan al'umma, yada al'adun Musulunci da koyarwarsa na asali, gyara kasa da kyautata yanayin zamantakewar al'umma, yada adalci da kawar da nuna bambanci a matsayin hanyar da kawai
za a bi wajen fita daga cikin matsalolin da ake fama da su.
Ayatullah Khamene'i, yayin da kuma ya koma kan fada da makirce-makircen manyan kasashen duniya ma'abuta girman kai akan J.M. ta Iran cikin shekaru 25 din da suka gabata, ya bayyana
cewa: "Kafa gwamnatin Musulunci a Iran ya kasance babbar barazana ga haramtattun manufofin ma'abuta girman kai na duniya kamar yadda kuma ya kasance ummul aba'isin din farkawar duniyar musulmi, wadannan
abubuwa dai su ne suka sa tun farkon kafa wannan tsari zuwa yau din nan take fuskantar matsaloli da makirce-makircen abokan gaba".
Har ila yau Jagoran ya bayyana kokari a bangarori daban-daban da kuma fuskantar matsaloli da dukkan karfi a matsayin hanya guda kawai ta ci gaba da tafarkin nasarar al'ummar Iran, inda ya kara
da cewa: "Kokari a tafarkin kiyaye 'yanci da daukakar kasa da kuma fuskantar bakar siyasar 'yan mulkin mallaka da kuma mamayan Amurka, suna daga cikin ayyukan da suka hau kan al'umma da suke bukatuwa da
taka tsantsan".
Haka nan kuma Jagora Imam Khamene'i, yayin da yake ishara da kokarin makiya wajen haifar da rikicin mazhabobi tsakanin al'ummar musulmi, cewa ya yi: "Kokarin haifar da sabani da rikici tsakanin 'yan shi'a
da 'yan sunna, wanda a halin yanzu ake ci gaba da yi a kasar Iraki, na daga cikin makirce-makircen 'yan mulkin mallaka kuma hakan na daga cikin tsohuwar siyasar turawan Ingila na rarraba kan al'umma, to sai dai kuma addinin
musulunci ya jaddada wajibcin hadin kai da fahimtar juna tsakanin al'ummar musulmi...".
Har ila yau Jagoran ya jaddada wajibcin ba da kokari da himma wajen kyautata yanayin rayuwar al'umma da kuma saukaka musu samun abubuwan da suke bukatuwa da su don rayuwa.
Kafin jawabin Jagoran dai sai da shugaban majalisar kwararrun Ayatullah Mishkini ya gabatar da jawabi da kuma isar da sakon taya murnarsu ga Jagoran da kuma al'ummar musulmi dangane da zagayowar ranar haihuwar
Imam Ali (a.s).
A yayin jawabin nasa Ayatullahi Mishkini ya bayyana biyayya ga adilan shuwagabanni a matsayin babbar ni'imar Ubangiji, inda yayin da yake wajibcin fahimtar ni'imar da ke cikin tsarin Musulunci ya bayyana cewa: "Dole ne
dukkan al'umma musamman malamai su fahimci wannan lamari da kuma sauke nauyin da ya hau kansu".
Har ila yau kuma yau din dai a yayin wannan ganawa, Ayatullah Ibrahim Amini, na'ibin shugaban majalisar kwararrun din ya gabatar da rahoto kan zaman majalisar ta kwanaki biyun da suka gabata na majalisar.
|
-03 ga
Satumban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Sarkin Jordan Abdullahi na Biyu
Da Tawagarsa
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa ana iya magance matsalolin kasashen
musulmi ta hanyar dogaro da Ubangiji, kishi, hadin kai da kuma dogaro da al'umma.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba (3/9/2003) yayin da yake ganawa da Sarki Abdullahi na biyu na kasar Jordan a lokacin
da ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke birnin Tehran, inda yayin da yake ishara da makwabtakan da Iran da Jordan suke da shi da kasar
Iraki ya kara da cewa tattaunawa tsakanin jami'an kasashen biyu kan kasar Iraki abu ne mai muhimmanci wanda kuma ya zama wajibi.
Imam Khamene'i ya kara da cewa: "Babu shakka yanayin da kasar Iraki take ciki lamari ne mai daga hankali saboda ci gaba da mamayan da sojojin
Amurka suke wa kasar wanda hakan ya sanya kasar ta rasa wata takamammiyar makoma".
Har ila yau Jagoran, yayin da yake ishara da wajibcin hadin kai da 'yancin dukkan kasar Iraki, ya bayyana cewa: "Dole 'yan mamaya su
gaggauta barin kasar Iraki, su ba wa al'ummar Iraki damar gudanar da mulkin kasarsu da hannunsu".
Yayin da kuma ya koma kan kasar Palastinu da kuma jaddada wajibcin da ke kan al'ummar musulmi da kasashensu wajen goyon bayan al'ummar Palastinun,
Imam Khamene'i ya ce: "Goyon bayan al'ummar Palastinu ba wai kawai goyon bayan wata kasa ko kuma al'umma guda ba ne, face dai wani kokari ne na magance
matsalar dukkan kasashen musulmi da na larabawa".
Yayin da kuma yake jaddada wajibcin taka tsantsan wajen fuskantar abokan gaba, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya ce: "Kasar Amurka cikin shekaru
hamsin din da suke wuce ta kasance tana goyon bayan haramtacciyar kasar Isra'ila ne, don haka idan dai ana magana kan lamarin Palastinu ne, Amurka za a lissafa
ta ne a matsayin mai fuskantar al'umman musulmi, don haka babu yadda za ta kasance mai shiga tsakani".
Har ila yau yayin da yake ishara da karen tsayen da haramtacciyar kasar Isra'ilan take wa dukkan yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu na sulhu, Imam
Khamene'i ya ce: "A irin wannan yanayi na rashin girmama yarjejeniyoyin da aka cimma da abokan gaban suke yi, hanya kawai ta magance wannan matsala ita ce
hadin kai tsakanin larabawa da sauran al'umman musulmi da kuma ba da himmarsu wajen goyon bayan al'ummar Palastinu marasa kariya".
Shi ma a nasa bangaren, Sarkin Jordan din Abdullahi na biyu, yayin da yake bayyana jin dadinsa da wannan ziyara da ya kawo Tehran din ya ce: "Akwai
bangarori da dama da za a bi wajen fadada alakar da ke tsakanin kasashen biyu, don haka ina fatan za a yi amfani da su wajen karfafa alakar Tehran da
Oman".
Har ila Sarki Abdullahin ya bayyana matsalar kasashen Palastinu da Iraki a matsayin manyan matsalolin da suke fuskantar duniyar musulmi, inda ya kara
da cewa: "Shawara da hadin gwuiwa tsakanin Iran da Jordan wajen kiraye manufofin dukkan bangarorin biyu zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin".
Har ila yau Prime ministan Jordan din Abu Ragib ya gabatar wa Jagora da wani rahoto kan yadda lamurra suke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.
Haka nan kuma ministan tsaron cikin gida na kasar Jordan din shi ma ya gabatar wa Jagora Imam Khamene'i da rahoto kan mahangar kasarsa kan kasar Iraki, inda ya bayyana
wajibcin hadin kai tsakankanin al'umma Iraki saboda yanayin halin damuwa da kasar take ciki.
|
|
-02 ga
Satumban 2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Ya Jinjina Wa Masana Ilmin Kimiyya Na Iran
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa irin nasarorin da
masana Iraniyawa suke yi wajen kirkiro abubuwa da ya sanya sauran al'ummomi samun karfin gwuiwa wajen dogaro da kai na
daga cikin abubuwan da suka sa makiya suke adawa da al'umman Iran din.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Talata (2/9/2003) a yayin da yake maraba da wasu masana ilmin kimiyya na Iran
wadanda suka sami nasarar kirkiro da kuma yawaita wasu matsi-matsin halitta, a lokacin da suka kai masa ziyara a gidansa
dake Tehran yana mai cewa Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya kasance babban ummul aba'isin din 'yantar da duniyar musulmi
daga danniya da mulkin mallakan ma'abuta son danniya na duniya.
Har ila yau Jagoran ya bayyana cewa wannan kokari da masanan suka yi wajen kirkiro wadannan kwayun halittu nesa ba kusa
ba ya ruguza dukkan wani shingen da makiya suka sanya wa al'umman Iran din cikin shekarun baya-bayan nan don hana su amfanuwa
da karfin da suke da shi.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin nasarori da kirkire-kirkiren da matasa muminai Iraniyawa suka samu bayan
nasarar Juyin Juya Halin Musulunci, Imam Khamene'i ya ce: "Dole ne a tuge jijiyan jin shu'urin gajiyawa a tsakankanin al'ummar
Iran, don kuwa tun tsawon tarihi al'umman Iran sun tabbatar wa duniya a fili karfin da suke da shi a bangaren ilmi da
nasarorinsa". |
|
|
|
|
|
|
|
Koma Sama |
| |