Ayyukan Mai Girma Imam Khamene'i (H) Na Yau Da Kullum
(Watan Nuwamban 2003)


-30 ga Nuwamban 2003

Imam Khamene'i Ya Jinjinawa Dakarun Basij A Makon Basij Na Kasa

A yau lahadi 30 ga watan Nuwamban 2003 ne Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Aliyu Khamene'i (h), a wata ganawa da ya yi da wasu kwamandojin dakarun sa kai na Basij, ya taya 'yan Basij din da dukkan al'ummar Iran zagayowar makon Basij din da ake gudanarwa.

A yayin wannan ganawa dai Jagoran ya ce: Hakikanin ma'anar Basij shi ne mutumci da aiki tukuru a dukkan bangarori wajen ganin an cimma madaukakan manufofin tsarin musulunci a dukkan bangarori.

Har ila yau Imam Khamene'i ya ce: "Basij dai su ne madaukakiyar bishiyar nan da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya dasa kana kuma ta yadu a zukatan matasa da sauran al'umma".

Yayin da yake nasiha ga dakarun Basij din Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya kiraye su da su kula da ayyuka da zantuttukansu a duk inda suke yin hidima wa al'umma.

Dakarun Basij dai dakaru ne na sa kai da aka kirkiro su bisa umarnin Marigayi Imam Khumaini (r.a) don kare kasa da kuma tsarin Musulunci. An kirkiro wadannan dakaru ne kuwa a watan satumban 1980 bayan kallafaffen yakin da Iraki ta kallafa wa Iran da kuma bukatan da ake da shi da wasu dakaru na sa ma'abuta sadaukarwa don kare kasarsu da kuma kawo karshen makircin makiya da suke son ganin karshen jaririyar gwamnatin Musulunci wacce ta kasance musu babbar barazana wajen cimma manufofi da burorinsu.



-26 ga Nuwamban 2003

Imam Khamene'i: Hadin Kan Musulmi Shi Ne Mabudin Nasararsu A Dukkan Bangarori.

A yau laraba 26 ga watan Nuwamban 2003 ne Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya yi maraba da kuma ganawa da manyan jami'an Iran da suka kawo masa ziyara don taya shi da sauran al'ummar Musulmi murnar zagayowar bukin karamar salla.

Daga cikin jami'an da suka kai ziyara wa Jagoran har da shugaban kasar Iran Sayyid Muhammad Khatami, Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Sheik Mahdi Karrubi, Alkalin alkalai kuma shugaban Ma'aikatar Shari'a Ayatullah Mahmud Hashimi Shahrudi, shugaban majalisar fayyace maslahar tsarin Musulunci Ayatullah Ali Akbar Hashimi Rafsanjani, jakadun kasashen larabawa da na musulmi da suke Tehran da dai sauran al'umma.

Yayin da yake maraba da manyan bakin, Jagora Imam Khamene'i ya taya su murnar zagayowar wannan idi mai girma yana mai cewa wannan buki na da wani sako na musamman wanda shi ne kuwa bukatuwan hadin kai da taimakekkeniya tsakanin al'umman musulmi a duk inda suke a duniya.

Imam Khamene'i ya ce: Hadin kai dai shi ne mabudin nasarar al'ummar musulmi a wannan yanki da kuma sauran yankuna na duniya da kuma akan ma'abuta girman kai na duniya.

Jagoran ya ce irin halin kuncin da Palastinawa da mutanen Iraki suke ciki da kuma irin bakar siyasar Amurka na zalunci akan kasashen musulmi sun samo asali ne sakamakon irin rashin hadin kan da musulmi suke fama da shi. Don haka Jagoran ya ce matukar dai musulmin suna son kubuta daga wannan hali to dole ne su hada kansu waje guda.

Ayatullah Khamene'i ya ce makircin abokan gaban musulunci na fili da na boye wajen haifar da rashin jituwa tsakanin musulmi shi ya sanya ya zamanto wajibi ga al'ummar musulmi sama da kullum wajen su hada kansu waje guda don fuskantar wannan makirci na makiya.

Yayin da ya koma kan kasar Iraki kuwa Jagoran ya ce ya kamata al'ummar musulmi su fahimci cewa ma'abuta girman kan duniya suna kokarin haifar da rarrabuwa ne a kasar Iraki, to amma ya kamata su san cewa Iraki fa ta dukkan Irakawa ne. Yayin da kuma yake magana kan tsarin mulkin Irakin da za a rubuta, Imam Khamene'i cewa ya yi: Sabon tsarin mulkin Irakin dole ya kasance Irakawa ne za su rubuta da hannunsu ba wai Amurkawa ba, idan kuwa ba haka ba to Irakin ba za ta kasance mafaka ba ga 'yan mamaya.

Kafin jawabin Jagoran kuwa sai da Shugaban kasa Sayyid Muhammad Khatami ya isar da sakon taya murnarsa ga Jagoran da kuma dukkan al'ummar musulmi yana mai bayanin irin ci gaban da aka samu a Iran da kuma sauran kasashe.



-26 ga Nuwamban 2003

Imam Khamene'i: Gwamnatin Amurka Ta Sanya Al'ummarta Cikin Tsaka Mai Wuya A Iraki

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana taken kare demokradiyyar da Amurka take yi a matsayin "tsagoron karya da rashin kunya" yana mai cewa al'ummomin Iraki da sauran kasashen musulmi sun dauki Amurkan a matsayin babbar abokiyar gabansu.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba (26/11/2003) yayin da yake gabatar da hudubar sallar karama a masallacin idi na birnin Tehran inda ya ce: "Su kansu jami'an Amurka suna gaba da demokradiyya sun san cewa "Ko ina dai a duniyar musulmi aka gudanar da irin wannan zabe (zaben jin ra'ayin mutane kan Amurka), to sakamakon zaben dai shi ne abin da Amurkawan suke tsoro, shi ne kuwa samar da mutumin da zai yi kiyayya da Amurka ta kowani bangare. A ko ina ne cikin duniyar musulmi aka gudanar da irin wannan zabe, wannan dai shi ne sakamakon da za a samu, babu wani bambanci".

Yayin da yake tabbatar da karya Amurka na kare demokradiyya da kuma yadda Amurkan ta dinga shirya juyin mulki a kasashe daban-daban akan gwamnatocin da jama'a suka zaba don cimma manufofinsu, Jagoran ya bayyana cewa: "Gwamnatin Amurka dai duk da da'awar demokradiyya da take yi amma sai ga shi tana aikata nau'oi na ta'addanci daban-daban akan al'ummomin duniya da kuma demokradiyya, wannan gwamnati dai ta Amurka da ranar 28 ga watan Khordad ta kulla makirci ga Iran, ta shirya juyin mulki a kasar Chile akan gwamnatin da al'umma suka zaba, gwamnatin Amurka da ta sha shirya juyin mulki daban-daban akan halaltattun gwamnatoci a Latin Amurka, Afirka da dai sauran kasashe, gwamnatin Amurka da shekara da shekaru take goyon bayan manyan 'yan kama karya irinsu Muhammad Ridha Pahlawi na Iran, gwamnatin Amurkan da ko a yanzu takan amince da kowace gwamnati komai zaluncin da take yi kuwa matukar dai za ta biya musu bukatunsu, to wani mutum ne kuwa zai yarda da wannan gwamnatin".

Yayin da yake magana kan tsayin dakan da Irakawa suke yi wajen fuskantar Amurkawa 'yan mamaya a kasarsu da kai musu hare-hare da suke yi a kusan kullum, Imam Khamene'i ya ce hakan ya samo asali ne daga irin ayyukan ta'addanci da cin zalin da Amurkawan suke yi wa Irakawan a cikin kasarsu.

Yayin da kuma ya koma kan al'ummar kasar Amurka da irin halin tsaka mai wuyan da gwamnatinsu ta sanya su a Iraki, Jagoran juyin juya halin ya ce: "Ya kamata dai al'ummar Amurka su san cewa gwamnatinsu ta sanya su ne cikin tsaka mai wuya a kasar Iraki, gwargwadon yadda suka ci gaba da zama a Irakin kuwa gwargwadon irin matsalar da za su ci gaba da fuskanta. Ya kamata a san cewa fa tsaka mai wuyan da Amurka take ciki a Iraki ya kai matsayin da Amurkan tana ruwan bama-bamai daga sansanoninta da suke cikin ruwa, wanda hakan yana nuni da gazawarta wajen gudanar da ayyukanta a Irakin. Matukar dai suka ci gaba da zama to yanayinsu zai ci gaba da lalacewa da shiga halin kunci".

A wani bangare na jawabin nasa Jagoran ya jinjina wa al'ummar Iran da sauran al'ummomin duniya dangane da fitowar da suka yi ranar Kudus ta Duniya don nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu yana mai cewa: "A wannan shekarar ma dai al'ummarmu a ranar Kudus, take guda suka dinga rerawa wajen nuna goyon baya da kariyarsu ga al'ummar Palastinu raunana marasa kariya kamar yadda takensu guda ne wajen yin Allah wadai da kuma nuna kyamarsu ga Amurka, haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma sahyoniyawa, wadanda duk da irin farfagandojinsu na karya kan batun kare hakkokin 'yan'Adam da demokradiyya suke aikata mafi munin ayyukan ta'addanci akan wata al'umma da ake zalunta (Palastinawa). Don haka ina mika sakon godiyata, a matsayina na karamin mai muku hidima, ga dukkan al'ummarmu madaukaka, lalle kun daukaka matsayin Iran, matsayin Jamhuriyar Musulunci a idanuwan al'ummomin duniya. A kowani lokaci kana a kowani guri, al'umma da dukkan karfi da iradarsu sun nuna wa al'umma matsayarsu".

Tun farko dai sai da Jagoran ya taya dukkan al'ummar Iran da na sauran kasashen musulmi murnar zagayowar karamar salla da fatan Allah Ya karbi ayyukansu cikin watan Ramalana mai alfarma da ya wuce.

Mai Son Ganin Cikakken Wannan Huduba Na Jagora Yana Iya Matsa Nan (CIKAKKIYAR HUDUBAR)


-23 ga Nuwamban 2003

Imam Khamene'i: Dole Ne 'Ya'yan Shahidai Su Yi Alfahari da Iyayensu

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya nuna jin dadi da farin cikinsa saboda kasantuwa cikin 'ya'yan shahidan, inda ya ce: Mahaifanku ('ya'yan shahidan) sun sadaukar da rayukansu ne a lokacin da kasarmu take bukatuwa da jaruman mazaje.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Lahadi 23 /11/2003 a lokacin da yake ganawa da darurrukan 'ya'yayen shahidan da suka kai masa ziyara a gidansa.

Jagoran ya kara da cewa: Dole ne ku yi alfahari da wadannan iyaye naku don kuwa sun rasa rayukansu ne a tafarkin neman sa'ada wanda dukkan mutane suke burin samu, kamar yadda kuma suka sami damar bin wannan tafarki kuma suka sami isa wajen Madaukakan bayin Allah cikin karamin lokaci.

Yayin da yake ishara da irin karfi da shirin da 'ya'yan shahidan suke da shi wajen ba da gudumma a bangarori daban-daban na rayuwa da kuma kira gare su da su yi kokarin amfani da samartakansu.

Jagoran ya jaddada cewa: Bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci an samu samuwar wasu nau'i na matasa wadanda samuwarsu ta haifar da albarkoki ga al'umma da kasarmu, kuma a nan gaba ma kasarmu za ta ci gaba da amfanuwa da albarakan wadannan matasa.

A yayin wannan ganawa dai Hujjatul Islam wal Muslimin Rahimiyan wakilin waliyul fakih kana kuma shugaban Cibiyar Shahidan ta Iran ya gabatar wa Jagoran da rahoto kan ayyukan da 'ya'yan shahidan suke yi a bangarori daban daban.

An fara wannan ganawa ne dai da karatun Alkur'ani mai girma daga bakin daya daga cikin 'ya'yan shahidan, kana kuma bayan jawabin Jagoran, ya jagorance su sallar magariba da lisha kafin nan kuma suka bude baki tare da Jagoran.



-22 ga Nuwamban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Jami'an Cibiyar Kundin Ilmi

A yau asabar 22 ga watan Nuwamban 2003 ne tawagar jami'an cibiyar tattara kundin ilmi suka gana da Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) a gidansa da ke nan Tehran.

A jawabin da ya gabatar a farkon ganawar, shugaban cibiyar Malam Haddad Adil yayin da yake ishara da shekaru 20 da kafa cibiyar da kuma mai da ita zuwa wata cibiya ta ilmi da gwamnati ta yarda ya ce: A halin yanzu wannan cibiya tana da membobi sama da 100 da suka rubuta sama da rabin abubuwan da aka rubuta a juzu'i na 7 na wannan kundin ilmi.

A yayin da yake gabatar da nasa jawabin, Imam Khamene'i, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya gode wa shugaba da membobin wannan kungiya saboda irin kokarin da suka yi wajen tara wadannan ilmummuka, yana mai cewa: Dole ne jami'an su tsara wannan kundin ilmi ta yadda zai kasance cikin tsari na koli.

A yayin wannan ganawa dai wasu daga cikin jami'an cibiyar sun gabatar da shawarwarinsu da kuma yadda suke ganin ya dace a tafiyar da al'amurra.



-14 ga Nuwamban 2003

Imam Khamene'i: Tsohon Makircin Amurka Ba Zai Yi Aiki Ba A Halin Yanzu

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa a halin da ake ciki Amurka tana cikin hali tsaka mai wuya sakamakon rashin nasaran da ta samu a kasashen Afghanistan da Iraki, yana mai jan hankulan al'umma da su yi hankali don Amurkan yanzu tana kokarin kulla makirci na siyasa da al'adu don cutar da kasashen yankin.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Juma'a (14/11/2003) yayin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a a nan birnin Tehran yana mai cewa Amurka dai ta riga da ta fahimci cewa kamfain dinta na soji ba zai haifar da da mai ido ba a yankin Gabas ta Tsakiya, don haka ne yanzu suke son fitar da wani sabon salo a yankin.

Yayin da ya koma kan sabon makircin Amurka na cewa wai tana son tabbatar da demokradiyya a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma jan kunne kasashen yankin da su yi hankali da wannan makirci, Imam Khamene'i ya ce: "Duk wani mutumin da ya san siyasar shuwagabannin Amurka cikin shekarun da suka wuce tun daga yakin duniya na biyu zuwa sama zai ji kunya ya ji shugaban wannan kasa yana cewa wai su ne masu kare demokradiyya".

Jagoran ya ci gaba da cewa: "Ta ya ya za a yi mutum ya zamanto maras lamiri da har zai iya furta wannan magana maras tushe kana kuma karya? Wannan kokari dai na Amurkan kan batun demokradiyya wani kokari ne kawai na yin kafar ungulu wa kokarin da wasu al'ummomi yankin na tabbatar da adalci. Jagoran yana mai kawo misalin irin goyon bayan da Amurkan ta bai wa gwamnatin kama karya ta Iraki ta Saddam Husaini akan Iran a matsayin abin da ke karyata ikirarin Amurkan na tabbatar da demokradiyya.

A wani bangare na hudubar tasa Jagoran ya yi Allah wadai da kisan gillan da Amurkawa suke wa al'ummar kasashen Afghanistan da Iraki ba tare nuna damuwa ba, yana mai nuni da cewa duk da hakan kuwa Amurkan ta gagara cimma manufofinta a wadannan kasashe.

Yayin da ya koma kan al'ummar Iran kuma da irin makircin da makiya suke yi wajen rarraba kan al'umma, Imam Khamene'i ya ce: "Manyan kasashe ma'abuta girman kai tare da HKI suna ta kokari ba dare ba rana wajen haifar da sabani tsakanin bangarorin siyasa na Iran a matsayin hanyan da za su bi wajen cutar da Jamhuriyar Musulunci". Har ila yau jagoran ya ce Amurkan dai tana ta kokarin haifar da wani irin yanayi na fuskantar akidun musulunci, juyin juya hali da kuma tsarin mulki na Iran don dai su cimma burorinsu, sai dai kuma Jagoran ya ce matukar dai Amurkan ta ci gaba da wannan siyasa ta ta to kuwa za ta ci gaba da shan kunya.

Jagoran ya ce kamar yadda Imam Khumaini ya fadi ne a yau din nan Amurka ta kasance kasar da al'umman musulmi suka fi kyama kana kuma shugaban Amurka da prime ministan HKI sun zamanto mutanen da aka fi kyama a duniya.



-06 ga Nuwamban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Malamai da 'Yan Jami'a

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa tsananin bukatuwan da matasa suke da shi da abubuwa irinsu adalci, 'yanci da ilmin kimiyya zai tabbatar da nasara da ci gaba manufofin juyin juya hali.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Alhamis (06/11/2003) yayin da yake ganawa da masana da 'yan jami'a da suka kai masa ziyara yana mai cewa: Iran tana bukatuwa da matasa wajen biyan bukatunta a bangarori daban-daban yana mai karawa da cewa wadannan bukatu za su haifar da da mai ido ga jamhuriyar Musulunci.

Yayin da kuma ya koma kam makiya da irin makirce makircen da suke kullawa, Jagoran ya ja kunnen matasan da cewa makiya a koda yaushe suna kokari ne su kaskantar da ci gaban da matasa suke samu, yana mai cewa lalle wannan makirci na makiya ba zai ci nasara ba matukar dai matasan suka yi ayyukansu cikin kula da nuna damuwa.

Jagoran ya ce Iran ta ci gaba wajen ilmi mai zurfi yana mai ishara da irin kokarin matasan akan wannan batu.

A karshe Jagoran ya ce yana da kyau jami'ai su yi amfani da tajruban da matasan suke da shi wajen gudanar da mulki.



-05 ga Nuwamban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Gabatar Da Shirin Shekaru Ashirin Na Ci Gaban Kasa

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) a yau laraba 5/11/2003 ya gabatar da wani shiri na tattalin arziki, zamantakewa da ci gaban al'adu na nan da shekaru ashirin masu zuwa.

A yayin da yake gabatar da wannan kundin shiri, Jagoran ya ce: "Bisa dogaro da Allah Madaukakin Sarki, kasar Iran za ta cikin shekaru ashirin masu zuwa za ta kasance daga cikin kasashen masu ci gaba na duniya".

Yayin da yake ishara da tsarin mulkin Jamhuriyar Musulunci, Imam Khamene'i ya ce Iran za ta kasance a sahun gaba-gaba wajen ci gaban tattalin arziki, kimiyya, kere-kere a wannan yanki, muna godiya da albakacin musulunci da kuma juyin juya halin Musulunci".

Har ila yau Jagoran ya ce: "A shekaru ashirin masu zuwa Iran za ta yi aiki karkashin tsari da dokoki na Musulunci, demokradiyya, al'adu da manufofin kasa wajen tabbatar da hakkokin 'yan Adam, 'yanci, demokradiyya ta addini da kuma adalci tsakanin al'umma".

Imam Khamene'i ya ce Iran tana da hakkin ci gaba a bangaren kimiyya da kere-kere, muka godiya da karfin al'umma da muke da shi.

Jagoran ya ce lalle ne kowani Bairaniye ko Bairaniya ta yi alfahari da kasantuwansa/ta da kuma ba da himma wajen ci gabantar da kasa gaba.



-04 ga Nuwamban 2003

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da 'Yan Jaridan da Amurkawa Suka Kame A Iraki

A yammacin yau Talata (4/11/2003) ne Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya gana da kuma maraba da Sohail Karimi da Sa'id Abu Talib, 'yan jaridun nan biyu masu daukan hoto wa tasha ta biyu da gidan talabijin din Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sojojin Amurka suka kama da kuma tsare su na watanni a kasar Iraki da suka mamaye.

A yayin wannan ganawa dai Jagoran ya nuna farin cikinsa da sako 'yan jaridan da aka yi jiya litinin bayan sun shafe kimanin kwanaki 127 a tsare a kasar Iraki.

Karimi da Abu Talib dai an kame su ne a ranar 1 ga watan Yulin nan a garin Kut da ke kudu maso gabashin kasar Irakin tare da wani mai musu fassara da kuma direbansu a lokacin da suke kokarin shirya wani shiri kan rayuwar al'ummar Iraki.

Da farko da Amurkawan sun ce suna zarginsu ne da leken asiri to amma kuma rahotanni sun bayyana cewa sai da suka nemi izini daga Amurkawan kafin suka fara gudanar da aikin nasu.

Amurkawan dai sun tsare su a wurare daban-daban na Iraki, kafin suka mika su ga sojojin Birtaniyya da suke Umm Kasr. Tuni dai kafafen watsa labarai daban-daban suka yi Allah wadai da tsare 'yan jaridan da Amurkawan suka yi suna masu cewa hakan take hakkokin 'yan jarida ne.





-02 ga Nuwamban 2003

Imam Khamene'i: Za Mu Dakatar Da Duk Wata Tattaunawa Kan Batun Nukiliyya Matukar Muka Ca Hakan Zai Cutar da Ka'idojin Addini

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) yayin da yake ishara da matsayina dangane da batun tattaunawa da jami'an Turai kan batun makamashin nukiliyya ta Iran din ya bayyana cewa: Sanannen abu ne cewa matukar dai mutanen da suke tattaunawa da jami'an gwamnatinmu, suka ci gaba da neman karin bukatu da kuma dagewa kansu, to lalle babu makawa za a dakatar da duk wata tattaunawa da ake yi da su kuma ba za a biya musu bukatan ba.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Lahadi (2/11/2003) a yayin da yake ganawa da manyan jami'an gwamnatin Musulunci ta Iran don tattaunawa kan mas'aloi daban daban da suke fuskantar Jamhuriyar musamman ma dai batun korafin da wasu kasashe suke kan batun shirin irin na makamashin nukiliyya na ruwan sanyi, inda ya kara da cewa: "Dukkan matakin da muka dauka, to fa a duk lokacin da muka ga hakan zai cutar da ka'idoji na addini da kuma jamhuriyar Musulunci, to babu makawa za mu dakatar da wannan lamari a daidai wannan lokaci".

Jagoran yayin da yake mayar da martani kan korafin da wasu suke yi na cewa an yi watsi da irin nasarar da Iran ta samu a wannan bangare na nukiliyya ya bayyana cewa: "(Ina so in sanar da ku cewa) babu wata yarjejeniya da aka cimma a wannan bangare don yi watsi da wannan abin da aka cimman, lalle mun kasance cikin kula da sanya ido kuma hakan ba zai taba faruwa ba ko da a nan gaba ne".

Yayin da kuma yake bayani kan wannan matsaya da Iran ta dauka na sanya hannu kan karin sharudda da kuma abin da hakan ya ke nufi, Imam Khamene'i ya ce: "Jamhuriyar Musulunci da kuma madaukakan jami'anta sun yanke shawarar daukan mataki na yin bayani wa duniya da kuma barinsu su gane wa idanuwansu gaskiyar abin da ke gudana. Suna so ne su bayyana wa duniya cewa fa lamarin lalle ba haka yake ba, ku zo ku gane wa idanuwanku abubuwan da suke gudana don ku tabbatar. Wannan fa shi ne abin da ya faru. Ya zuwa yanzu fa wannan shi ne abin da jamhuriyar Musulunci ta dauka kuma ta yadda da shi. Ku zo da kanku ku gani, ku zo ku gani da idanuwanku kan yadda ake tace sinadarin (uranium) din. Sun zo kuma sun gane wa idanuwansu abubuwan da ke gudana da kansu. An ce musu su zo su ga duk inda suke tsammanin ana gudanar da irin wannan aiki don gane wa idanuwansu, don su tabbatar da farfagandar yahudawan sahyoniya ba komai ba ce face karya da zuki ta malle".

Imam Khamene' ya bayyana cewar: matukar dai wani mutum ya so ya wuce gona da iri kan jamhuriyar Musulunci kan wannan batu, to babu makawa jamhuriyar Musulunci za ta wurge su da abin da suke so a bakunansu. Shakka babu jamhuriyar Musulunci ba ta kuma ba za ta taba mika wuya kan wannan batu ba. Wannan dai lamari ne da kowa ya kamata ya mai da hankali kansa ya kuma fahimce shi. Dole ne mu kiyaye ci gaban da muka samu a wannan bangare na ilmi.

Yayin da kuma yake mayar da martani da mutanen da suke cewa jamhuriyar Musulunci ta mika kai ga makiya, Imam Khamene'i cewa ya yi: "Wani tunanin kuma shi ne a yi tunanin cewa - jaruman al'ummarmu za su yi tunanin - cewa, lalle gwamnati ta mika kai. Lalle lamarin ba haka ya ke ba, babu wani mika kai da aka yi, don kuwa wannan wata harka ce kawai ta siyasa, aiki ne na diplomasiyya, tattaunawa da kuma yarjejeniya. Babu wani mika wuya cikin hakan, ya zuwa yanzu.

Kafin jawabin Jagoran dai sai da shugaban kasa Sayyid Muhammad Khatami ya yi karin bayani kan matsayar da Iran din ta dauka yana mai nuni da cewa hakan shi ne abin da ya dace a yi, kuma hakan ba wai mika wuya ba ne ga makiya face dai kafar ungulu ne ga makirce-makircensu.


Mai Son Ganin Cikakken Wannan Jawabi Na Jagora Yana Iya Matsa Nan (CIKAKKEN JAWABIN)


             

Koma Sama