Ayyukan Mai Girma Imam Khamene'i (H) Na Yau Da
Kullum (Watan Oktoban 2003)
-23 ga
Oktoban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Prime Ministan Pakistan A Tehran
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana cewa alakar da ke tsakanin Iran da Pakistan tana ci gaba tun bayan samun nasarar juyin juya halin Musulunci a 1979, kuma akwai bukatar a ci gaba da hakan.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Laraba (23/10/2003) a yayin da yake ganawa da Prime Ministan kasar Pakistan Mir Zafarullah Khan Jamali da ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke nan Tehran inda ya ce: "Alaka da manufofin Iran da Pakistan ba wai kawai sun takaita da alaka ta siyasa ce kawai ba, face dai suna da tushe na al'adu,
addini da tarihi.
Yayin da kuma ya koma kan halin da duniyar musulmi take ciki da kuma irin barazanar da ake wa al'ummar musulmi musamman al'ummomin kasashen Afghanistan, Iraki da Palastinu, Jagoran ya yi kira da a dada samun alaka da hadin kai tsakanin kasashen musulmi.
Har ila yau Jagoran ya ce, abokan gaba karkashin jagorancin Amurka suna tsoron ganin kasashen musulmi sun hada kansu waje guda, don haka ne ma suke kokarin wajen ganin sun haifar da rarrabuwa tsakaninsu, don haka Jagoran ya yi kira ga kasashen musulmin da su kasance cikin shiri wajen fuskantar wannan barazana ta makiya.
Shi ma a nasa bangaren prime ministan kasar Pakistan din Mir Zafarullah Jamali ya bayyana wa jagoran irin tattaunawar da ta gudana tsakaninsu da jami'an Iran, yana mai cewa lalle alakar kasashen biyu ta wuce batu na kasuwanci da tattalin arzikin, don haka ya ce lalle alakar za ta ci gaba da karfafuwa nan gaba.
|
-20 ga
Oktoban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Shugaban Kasar Aljeriya Abdul'aziz Bouteflika
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana cewa dole ne jami'an kasashen musulmi su tabbatar da kyakkyawar alaka tsakaninsu a matsayin babbar manufarsu da kuma ba da himma wajen daukan matsaya guda kan mas'alolin da suka shafe su.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Litinin (20/10/2003) yayin da yake maraba da shugaban kasar Aljeriya Abdul'aziz Bouteflika da ya kai masa ziyarar ban girma a gidansa a nan Tehran, inda ya ce: babbar matsalar da take fuskantar duniyar musulmi a yau din nan ita ce ta rarrabuwa da rashin
hadin kai.
Yayin da kuma ya koma kan kasantuwan Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma halin da Palastinawa suke ciki, Ayatullah Khamene'i ya ce: "A halin da ake ciki al'ummar Palastinu suna bukatuwa da taimako da goyon bayan kasashen musulmi".
Imam Khamene'i ya kara da cewa: Ya zama dole kasashen musulmi su saukar da nauyin da yake kansu na taimakon Palastinawa ba tare da jin tsoron barazanar Amurka ba".
Jagoran ya ce: "Faduwar haramtaciyyar kasar Isra'ila zai haifar da faduwa da rashin nasara bakar siyasar Amurka a yankin kuma wannan lamari ne mai yiyuwa".
|
-12 ga
Oktoban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Al'ummar Garin Zanjan
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i ya bayyana cewa da a ce shuwagabannin kasashen musulmi sun dogara da karfin al'ummarsu kamar yadda al'ummar Iran suka yi da manyan kasashen duniya
ma'abuta girman kai ba su aikata musu abin da suke aikatawa a yanzu ba.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Lahadi (12/10/2003) a lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban dubban al'ummar garin Zanjan da suka taru don masa barka da zuwa, inda ya kara da cewa: "kafa tsarin mulki a kasar Iran karkashin jagorancin
addini da mulkin al'umma yana tabbatar da mulki irin na musulunci da kuma al'ummar. Al'ummar Iran dai suna son 'yanci wa kawukansu ne kuma ba sa so su kasance karkashin ikon Amurka da sauran ma'abuta girman kai".
Ayatullah Khamene'i, har ila yau ya kara da cewa: "Jawaban da jami'an Amurka suke yi na wajibcin canza taswirar yankin gabas ta tsakiya wani kokari ne na ma'abuta girman kai na mallake dukiyar kasashen yankin da kuma kwace musu irin 'yancin da suke da shi
bugu da kari kan kafa gwamnatocin da za su kasance 'yan amshin shatansu masu kare HKI.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagoran Juyin Juya Halin Musuluncin ya bayyana cewa: "A halin yanzu kasar Amurka tana fuskantar matsaloli da yawan gaske duk kuwa da abubuwan da suka aikata a kasashen Iraki da Afghanistan. Kamar yadda HKI take fuskantar halin tsaka
mai wuya da kuma gazawa a kasar Palastinu sakamakon tsayin daka da imanin al'ummar Palastinu".
Har ila yau kuma yayin da ya koma kan batun taron shuwagabannin kasashen musulmi na kungiyar kasashen musulmi ta duniya OIC da za a gudanar a kasar Malaysiya, Imam Khamene'i ya yi fatan shuwagabannin kasashen musulmin za su fahimci muhimmancin karfin al'ummar musulumi da kuma
fuskantar barazana da kasashen musulmin suke fuskanta daga Amurka da dukkan karfinsu ba tare da tsoro ba.
|
-09 ga
Oktoban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Mahalarta Taron Majalisar Koli ta Mabiya Ahlulbait
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya bayyana cewa abin da kawai zai magance matsalolin da duniyar musulmi take fuskanta a halin yanzu shi ne kiyaye da
kuma karfafa ruhi da siffa ta Musulunci.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Alhamis (09/10/2003) yayin da yake ganawa da mahalarta taron kara wa juna sani na majalisar koli ta mabiya Ahlulbaiti (a.s) ta duniya da aka gudanar a nan birnin
Tehran, inda yayin da yake ishara da cewa kafa gwamnatin Musulunci a Iran ya tabbatar da tutar 'yanci da fada wajen tabbatar da adalci a hannun mabiya Ahlulbaiti (a.s) ya kara da cewa: "Mabiya Ahlulbaiti ('yan shi'a)
a koda yaushe sun kasance masu kira zuwa ga hadin kan musulunci, kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran bisa la'akari da wannan batu ta dau hakkin kare al'ummar musulmi a matsayin wani nauyi da ya hau kanta".
Yayin da kuma yake magana dangane da irin goyon bayan da J.M ta Iran ga al'ummar Palastinu da kuma gwagwarmayar da suke yi da yahudawan sahyoniya 'yan kaka gida, Imam Khamene'i ya bayyana cewa: "Gwamnatin Musulunci
ta Iran cikin shekaru 25 na kafa ta ta ci gaba da nuna adawarta ga ma'abuta girman kai da yahudawan sahyoniya 'yan share guri zauna da masu goya musu baya kuma koda wasa ba za ta juya da baya ba".
Har ila yau kuma Ayatullah Khamene'i yayin da yake ishara da kokarin kasashen duniya ma'abuta girman kai karkashin jagorancin kasar Amurka na kawar da ruhin musulunci a zukatan al'ummar musulmi da kuma wajibcin
da ke kan al'ummar musulmi musamman mabiya Ahlulbaiti (a.s) ya bayyana cewa: "Shahid mai girma Marigayi Ayatullah Sayyid Muhammad Bakir al-Hakim, wanda ya kasance daga cikin manyan jami'an wannan majalisa ta mabiya Ahlulbaiti (a.s),
kuma ta hanyar kokarinsa ya samu damar hada kawukan al'ummar Iraki waje guda karkashi tuta ta musulunci".
Yayin da kuma ya koma kan kasar Iraki da kuma bayyana mamayan da 'yan mamaya suka yi wa kasar a matsayin babban matsalar al'ummar Irakin, Imam Khamene'i ya bayyana cewa: "Idan da a ce an bar al'ummar Iraki su zabi hukuma
da dokokin da suka dace da su bisa akidunsu, to babu makawa da sun tafiyar da kasarsu cikin yanayi mai kyau".
|
-07 ga
Oktoban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Sayyid Abdul'Aziz Hakim
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya jaddada wajibcin samun hadin kai tsakanin 'yan shi'a da sunna da kuma
tsakanin kabilun kasar Iraki don cimma mafiya daukakan manufofin al'ummar kasar.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Talata (07/10/2003) yayin da yake ganawa da shugaban majalisar koli ta Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran Sayyid
Abdul'Aziz Hakim a ziyarar da ya kai masa gidansa da ke nan birnin Tehran.
A yayin wannan ganawa Imam Khamene'i ya jinjina wa iirn imani, jarunta, tunani da tsantsainin Marigayi Shahid Ayatullah Muhammad Bakir al-Hakim, tsohon shugaban
majalisar koli ta Juyin Juya Halin Irakin da ya yi shahada a sanadiyyar harin da aka kai masa a haramin Amirul Muminina, inda ya ce: "Duk da cewa shahadar wannan shahidi ya janyo
babbar hasara da kuma rashi ga al'ummar Iraki da sauran al'ummar musulmi, to sai dai saboda matsayin da shahid Hakim din ya ke da shi shahdar tasa ta yi tasiri ga halin
da kasar Irakin ta ke ciki kuma za ta ci gaba da haifar da tasirori daban-daban".
Yayin da kuma ya ke nuna jin dadinsa da zaban Sayyid Abdul'aziz Hakim da aka yi a matsayin shugaban majalisar kolin juyin juya halin Irakin, Ayatullah Khamene'i ya ce: "Ta hanyar
wannan zabe da ke cike da tunani da sanin ya kamata, za a ci gaba da bin tafarkin da Shahid Hakim din ya ke kai".
Imam Khamene'i ya ce kin mamaya da kuma kira ga ficewarsu daga Iraki na daga cikin bukatun al'ummar Iraki, don haka ya kirayi majalisar kolin ta juyin juya halin musulunci ta
Irakin da ta dada karfafa alakarta da manyan malamai da sauran masu kishin addini, inda ya ce: "Dole ne majalisar ta yi taka tsantsan wajen tsara dokoki da tsarin mulkin kasar Iraki ta yadda
hakan zai biya bukatun al'ummar Iraki da ake zalunta".
Shi ma a nasa bangaren Sayyid Abdul'aziz Hakim ya mika godiyarsa da damuwar da Jagoran juyin juya halin musuluncin, Imam Khamne'i, da al'ummar Iran suka nuna dangane da shahadar
Ayatullah Muhammad Bakir Hakim, kana kuma ya gabatar wa jagoran da rahoto dangane da yadda yanayin yake a kasar Irakin.
|
-04 ga
Oktoban 2003
Jagoran Juyin
Juya Halin Musulunci Yayin Ganawa da Insifoton 'Yan Sanda da Sauran Manyan Jami'an Tsaro
Na Iran
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) ya jinjina wa irin kokari da ayyukan da 'yan sanda
da sauran jami'an tsaron kasar suke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau din nan Asabar (4/10/2003) yayin da yake ganawa da babban sufeto janar na 'yan sandan Iran da sauran
jami'an hukumar 'yan sanda a duk fadin Iran, inda yayin da yake jinjina wa ayyukan da suka yi wajen tabbatar da tsaron kasa ya ce: "Dole ne Jami'an tsaron kasa
('yan sanda) su yi amfani da irin karfin da suke da shi da kuma goyon bayan al'umma wajen ci gabantar da ayyukansu gaba da kuma kara yawansu".
Yayin da kuma ya koma kan irin kokarin da 'yan sandan suke yi wajen biya wa al'umma bukatunsu, Imam Khamene'i ya ce: "Duk wani irin ci gaba da zama
cikin al'umma don tabbatar da tsaron lafiyarsu da jami'an 'yan sanda suka yi hakan zai kara dankon zumuncin da ke tsakaninsu da al'umma don kuwa tabbatar da
zaman lafiya da tsaron al'umma na daga cikin bukata ta rayuwar mutanen".
Har ila yau Jagoran ya nuna jin dadinsa da yanayin ladabi da biyayya da jami'an 'yan sandan suke da shi, inda ya kirayesu da su gudanar da
ayyukan da za su jawo hankulan mutane zuwa gare su da kuma samun kwanciyar hankali da su.
Imam Khamene'i ya bayyana rashin da'a da kuma taka doka a matsayin abubuwan da za su iya sanya al'umma su janye imanin da suke da shi da 'yan sanda, don haka ya ce: "Dole
ne a fuskanci duk wani saba wa doka da dukkan karfi musamman ma idan har hakan ya shafi haka kai da masu laifi ne, a irin wannan hali dole ne a gurfanar da masu saba doka
a gaban kuliya manta sabo".
Har ila yau kuma Jagoran ya jaddada muhimmancin kula da abubuwan da za su kara wa 'yan sandan imani da Allah da kuma dogaro da Shi don hakan shi ne ummul aba'isin din
ci gaban aikisu.
Kafin jawabin jagoran sai da babban sufeto 'yan sandan Iran din Mr. Kalibof ya gabatar wa Jagoran da rahoton irin ayyukan da hukumar tasa ta gudanar cikin shekara wajen ganin an
tabbatar da tsaro da zaman lafiyan al'umma.
|
|
-01 ga
Oktoban 2003
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci
Yayin Ganawa da Mataimakin Shugaban Kasar Siriya
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamene'i (H) yayin da yake ishara da matsayi na
musamman da alakar da ke tsakani kasashen Siriya da Iran ya bayyana wajibcin ci gaba da irin wannan kyakkyawar alaka a bangarori
daban-daban.
Jagoran ya bayyana hakan ne a yau Laraba (1/10/2003) a yayin da yake maraba da mataimakin shugaban kasar Siriya Abdulhalim Khaddam da
'yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma a gidansa da ke nan Tehran, inda ya kara da cewa:
Jagoran ya ce: "Jigon wannan alaka (da take tsakanin kasashen biyu) tun lokacin marigayi Hafiz al-Asad aka gina shi kuma a halin yanzu ma
lokacin Basshar al-Asad, a matsayinsa na Hafiz al-Asad karami, alakar ta ci gaba a yanayi mai kyaun gaske".
Yayin da ya koma kan halin da yankin Gabas ta Tsakiya ya ke ciki a halin yanzu musamman kasar Iraki da Palastinu, Imam Khamene'i ya ce: "A irin
wannan hali hadin kai da karfafa juna tsakanin kasashen yankin yana da muhimmancin gaske". Imam Khamene' ya bayyana faruwar rikici da fadan kabilanci da addini tsakanin al'ummar Iraki a matsayin babban hatsarin da zai iya fuskantar kasar Irakin,
inda ya ce: "Dole kungiyoyin kasar Iraki da sauran kasashen da suke da bakin magana a yankin su yi kokari wajen ganin sun kiyaye hadin kan da ke tsakanin al'ummar
Iraki.
Har ila yau Jagoran ya bayyana barazanar da Amurka take wa kasashen musulmi a matsayin hanya da suke bi wajen razana jami'an wadannan kasashe don samun daman
cimma burorinsu, inda ya kirayi shuwagabannin kasashen musulmi da su gane cewa wannan barazana ta Amurka ba wai tana nufin wata kasa guda ba ce face dai barazana ce
ga dukkan kasashen musulmi, don haka yayi kira ga kasashen da su hada kansu waje guda don ganin sun hana Amurka cimma wannan munanan manufofinta
Shi ma a nasa bangaren, mataimakin shugaban kasar Siriya Abdulhalim Khaddam ya yi kira da a ci gaba da samun karfaffiyar alaka tsakanin kasashen biyu. Har ila yau
mataimakin shugaban Siriyan ya bayyana mamayan da Amurka suka yi wa Iraki da kuma zaluncin da HKI take wa Palastinawa a matsayin lamari mai hatsari da ta da hankali, inda ya ce
hadin kai tsakanin kasashen musulmi ne kawai zai kawo karshen wannan zalunci. |
|
|
|
|
|
|
|
Koma Sama |
| |